Page 32

293 17 0
                                    

Tsorone ya kuma kama iman jin Ahmad yana neman kauce hanya , hannunsa ta rike da yake yawo a jikinta, tsayawa yayi cak , ya dena kising nata Dan tayi mugun tsorata, jin ya tsaya  yasa ,ta fara kokarin tashi daga jikinsa ta koma Dayan kujeran ta zauna

Ahmad bece mata Komai ba ,Asalima dariya ta bashi

Zama tayi ,sanna tayi kasa da Kai tana wasa da yatsun hannunta ,so take tayi wanka ,Allah Allah take yace ta tafi .

Zaman hijab dinta ta gyara , yadan tabe baki sanna ya gyara zama daga inda yake zaune

Ki shirya anjima wajen 11am , zamu gaida malam , nayi missing nasa sosai sosai 
Dadi ,farin ciki ,murna sun dabaibaye iman , ta rasa wanne zata fara bata sanda tayi wani tsalle Dan murna ba ,

Kafun tace Komai Ahmad ya rigata
Cewa"gama tsallenki yarinya ,zan Kai Karanki wajen umma ne "

Fuska ta cabe kaman yar yarinya , kaman zatayi kuka tace" me na maka , Ka rufa min asiri umma Sai a hankali tana iya cewa zata dukeni ,Amma lefin me nayi "

Dariya yayi sanna yace" lefin babba ma kikayi "

Zari ido tayi sannan tace "ni?"
Girgiza Kai yayi sanna yace "ehhh mana , lefin farko bakya Sakewa dani , na biyu idan Ina kisss....)
Ai kafun ya karasa tayi sauri ta rufe masa baki 😂😂
Sai kuma kunya ya kamata ta Ruga daki da gudu Sai kace budurwan village

Shi kuma ahmad dariya ta bashi

~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Ahmad ne sanye cikin kayansa na alfarma , yadi ne ash ,yayi mugun kyau kamar a sace Shi , yana zaune yana jiran iman
Daman yasan  mata indai zaa waje dasu sai sunma mutane delay ,
Tashi yayi ya tafi dakinta

Zaune ya sameta cikin lace dinta purple yasha dinki gashi ya zauna mata sosai , kaman a jikinta aka dinka kayan , Dan kunne da sarka take kokarin sakawa ,shine ya taimaka mata ta saka ,
Gaskiya iman tayi kyau sosai sosai
Ahmad kasa hakuri yayi sanda ya dagata ya juyata ,yace wow Mrs Ahmad gaskiya kinyi kyua sosai sosai
Zan bada tukuci fah
Amma da gyara
Kallonsa tayi ,Amma batayi magana ba

Sai yace"bana daya daga cikin mazaje masu son matansu su futa da Jan baki ,Dan haka idan zamu futa ki dena sawa"
Kai ta daga masa alaman Okhh

hijab dinta ta dauka ta saka sanna ta dauka tissue da zata goge Jan bakin
Kallonta ahmad yayi Sai admiring dinta yake tayi
"Haba wifey ya zaki goge ban gama gani kwalliyan ba , zo mana "
Ya fada yana kashe mata ido

Zuwa tayi gabansa ,shi kuwa ya runguma abunsa.
Sanan cikin tabara ya saka lips dinsa ya sanye Lipstick  din tasa (nidai nace ohoo ni halimatu ) .Hannunta yaja suka futo
Switch din palour da kitchen ya kashe ,sanan suka rufe gaban gidan
Ya bude mata gaban mota ta shiga ,ya rufe sanna ya zagayo wajen driver ya kunna mot-a sukayi sallama da me gadi suka kama hanya

A hanya babu Wanda yace ma Dan Uwansa Uffan , Sai sauraron waazin malam shiekh kabiru Gombe (my crush💃💃💃💃) suke yi

  A kofar gidan malam kyauta sukayi parking , iman ji take kaman ta tashi sama ta kosa ya gama parking su shiga ,
Parking Ahmad yayi sanna ya futa ya budema iman kofa ta futo (so romantic🥰)

Jerawa sukayi  , suka shiga gwanin ban sha'awa , gaskiya sun hadu

Da sallama suka shiga gidan
Malam suka gani a tskara gidan ,aiko washe baki yayi yana ta murna shi kanshi sun masa kyau ,
Sannu da zuwa ya musu
Suka gaishe cikin annashuwa ,
Umma ce taji maganar mutane tsakar gida itama ta futo Anata Murna da zolayan juna ,
Haka suka yini wajen malam
Dan mummy mahaifiyar Ahmad bana tana sunje Dubai ita da auta ,daddy be dawo aiki ba
Mubarak ma nan yazo suka hade

Chan wajen. Yamma Ahmad da mubarak suka futa
Umma ta saka iman a daki tana ta mata masiha da dabaru na yadda zata rike mijinta (ina ganin yadda Xarathy,Fatima walah ,small sister,blood suke ta miko kunne suna son su ji suma😂🤣🤣🤣)
Suna cikin haka saiga malam shima suka hade suka mata fada da shawara irin na manya
Haka iman Tayi ta zama ,Sai taji kaman Ahmad yace ta dawo nan da zama
Suna haka har dady ya dawo aiki ya shigo wajen malam , a nan suka hadu da iman ,
Yana ta farin cikin ganinta

Sai bayan magrib su ahmad suka dawo , dauke da ledoji ,suka ba ma malam nashi da daddy
Mubarak shima ya dauka nasa , sukayi musu sallam suka tafi ,
Iman duk ta hada rai kaman zatayi kuka , bata son tafiya
Shi kanshi ahmad ji yake kaman karsu lafi .
Haka dai sukayi sallam .suka tafi

A mota iman harda yan kwallanta ,Ahmad yana kallonta yayi Banza da ita .
A haka har suka iya gida


~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Iman  tabud'e k'ofar shikuma yakwaso ledojin daya ajiye suka shiga, afalo suka yada zango, yana ajiye ledojin yajuya zuwa masallaci,iman  kuma tatafi d'akinta itama tayi sallar.

     Bai shigoba har iman  tadawo falon, tazauna akan doguwar kujera tana danne-danne awaya dan babu wuta and'auke.

        Kusan mintuna 10 da zamanta aka kunna Gen...., haske ya gauraye ko ina, saiga Ahmad shima yashigo, sannu da zuwa tamasa.

    Ya amsa babu yabo babu fallasa, d'akinsa yashiga, kusan mintuna 15 yafito d'aukeda laptop ahannu, yacire kayansa, yacanja zuwa 3quarter da vest .

       Ya ajiye kayan hannunsa sannan ya zauna,
Iman tamik'e tad'akko masa ruwa.

         Zubawa tayi tabasa yasha, yamik'a mata kofin yana fad'in thanks.

     Jinjina kai kawai tayi batace komaiba.
Kallon lodojin da suka shigo dashi tayi ta dauka tayi kichen dashi , tana bud'e ledojin, kayan fruits ne sai gasassun kaji guda biyu da robar ice-cream guda biyu, saikuma fura guda uku.
Daukan komai daya tayi ,sauran ta ajje a fridge.
ta dakko tray a hadasu waje daya da ruwa tayi hanyar palour dashi
A saman center table a ajje
Kallonsa tayi tace masa bismillah

Kallon ta yayi ta wutsiyar idanu
Yace"dakkowa zakiyi ki bani Naci , kin wani ajje a center table"
Shuru tayi tana tunanin me zatayi dakkowa tayi ta daura akan cinyarta ,
Tsaban mugunta ta dakko babba wanda yafi karfin bakinshi zata bashi .
Shi kuma yana kallonta yayi murmushi yake "yadda kika bani haka zan miki a gado  😱😱"
"Kutmeleshin chan ta fada , tace kawai abar chin kazan " ta fada cikin tsoron  da kwalla duk ya cika Idonta

"Haba dai girl ,me zai Hanani chin kaza , kema Sai kin ci , kuma Sai kin biya shi ."ya fada with full confidence yana mata Wani kallon kasa ,me girgiza zuciyar masoyi .
anawa azuciyarta yau komai zai faru bazataci kazar nanba, haka kawai yadawo yace tabiyashi kuma, har yanzun bata manta da wahalar data shaba adaren ranar,
Kallonta ya kuma yi yace"am waiting ....."

  "Nifa na k'oshi, tayi maganar a shagwa6e".

        Yata6e bakinsa, "hummm, kuma bazai hanani abinda nayi niyyaba ba, gwamma kicima kisan cikikayi kika biya .

    Jin tayi shiru yajuyo ya kalleta, dariya tabashi yanda tayi wani kwale-kwale da idanu, aransa yace, " nasan maganin ki yarinya ".         Afili kuma yace, ''infa tahuce yazama sau biyu kenan, kuma babu k'oraf.......".

      ......aibama tabari yakai k'arshen maganarba, tad'ibo Takawo bakinsa.....

         "Hhm, d'uran k'arfi zakimin?".

      "wlhy kaifa ya Ahmad d'inan........

   Tayi shiru takasa k'arasawa.

          "Nifa ahmad  me?, dukdai yanda kikai dani, haka zanyi dake agado, garama kibini a sannu ehe.......😜"

Wanna kenan ...........

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now