Page 26

285 23 1
                                    

K allo kallo suka yi ma juna ,kowa a abunda yake kisawa zuciyarsa ,zuciyarsu sai harbawa yake sosai ,Bai San me zai fara ba ,shiru yayi ,Sai kuma yayi murmushi
"Mrs Ahmad wanna kallo haka karkisa ,daddy ya kasa gane Dansa mana , ai sai ki sa na kasa zama "ya fada cikin Zolaya Dan yaga duk a tsorace take

Ita kuma duk tsoro da mamaki ya kamata ,wai yau Ahmad ne a tsaye a matsayin mijinta ,Dan kallansa tayi da gefen ido suka hada ido ,Sai murmushi yake mata ,ai nan da  nan tayi maza ta rufe fuskanta da vail ,tana murmushi kasa kasa , a zuciyarta tana cewa 'alhamdullahi Allah ya amsa mata adduan ta ,Allah yasa wanan *SABUWAR RAYUWA* ya kawo mata farin ciki sosai

"Haba mrs Ahmad,ya da rufe min fuskana ,ban gama gani ba"cewar Ahmad,shi kanshi yana mamakin sabon Halinsa ,gashi yana jin dadin yadda take murmushii
Tunawa tayi da ya kamata ta gaisheshi ,Sai tace "ya Ahmad barka da dare"Ta fada kanta a kasa kaman tana gaban surikai😂😂😂😂 murya sai rawa yake

Shi kuwa ahmad tayi mugun basa dariya ,duk da yasan tana da sanyi ,amma tayi mugun basa dariya ,shiyasa ake cewa aure Yakin mata 😂😂

Kallonta ya Karayi ba Adadi ,sanna ya amsa tare da cewa ta samesa a falo,ya juya ya tafi , tashi tayi a hankali ,ta fara lafiya zuwa palon cikin natsuwa,
A falon ta Tarar dashi ,ta samu waje ta zauna a kujeran da ke opposites dinshi ,tayi  shiru tana wasa da yatsar hannunta .sai yanxu ya kare ma kwalliyanta kallo tsaf ,aiko tayi masa kyau sosai sosai ,lallen hannunta ya kalla da ke sheki ,gaskiya ta tafi da imaninshi .

Ita kuma iman jin shirun yayi yawa ne ,yasa ta dago kanta ,aiko suka hada ido tayi maza ta kauda kanta ,Sai ta fara tunanin dama haka ya Ahmad yake da shegen kallon tsiya ,

Tashi taga yayi ,yabi wani hanya ,da take tsamanin kitchen ne .
Jin takun takalminshi ne yasa ta dawo daga tunanin da ta shiga .

Plate da cup ya dakko ya darasu a bisa tray.

Yana zuwa yaje gabanta ya ajje ,sanna yakoma inda ya ajje ledan da ya shigo dashi , ya bude ,kazace guda biyu sai Hollandia yoghurt 🥛,Sai kuma kayan fruit (nace kai akwai cin dadi ,Ina su mrs Abdul Dan nasan nan aka fi auki😂😂😂)

Kaza daya ya bude ,ya saka a plate sai kanshi take ,sanan ya dakko cup din ya zuwa yoghurt Din a ciki ,

Ya dago kanshi yace mata yanmata sakko mana , Marairecewa tayi tace ta Koshi , aiko nan da nan ya koma Ahmad dinshi da ta sani , yace sakko mana ,da taga alam ba wasa a fuskanshi Sai ta sakko ,ta zauna chan nesa dashi ,Sai ya kuma cewa dawo nan ,ya nuna Mata kusa dashi ,
Matsowa tayi kaman zata yi kuka ,

Muko mata yoghurt din yayi yace amsa ki sha ,
Taki ko motsi kuwa balle ta amsa ,
Mutmushi yayi a zuciyarsa yace masan maganin ta ,yanxu zai koma mata Ahmad dinshi Dan yasan idan ya lallabata ,bazata taba cin abinchi ba ,kuma yasan bata ci abinchi ba tun safe,

Daure fuska yayi ya tashi ya dakko yoghurt din yace bude baki ,da zata mishi musu Amma ganin fuskan chi a daure yasa ta bude baki a kunyace ,
Shikuma ya fara bata tana sha ,yana bata Kazan a haka ya ciyar da ita har ta koshi ,ya koma zauna ,
Ita kuma ganin ya koma wajen da ya tashi sai ta miki zata gudu kunya duk ta kamata
Sai yace idan kika tashi kema sai kin rama wa Kura ayinarta ,aikuwa kafun ya rufe baki har ta koma ta zauna ,duka kunya ta dabaibayeta ,
Shima bismillah yayi ya fara cin kazan yana Shan yoghurt dinshi hankali kwance ,yayi kaman ya mata da ita a falon .
Tashi kije kiyi alwala ki jirani
Aikuwa da sauri ta mike ta tafi cikin sauri  harda tuntube
Dariya yayi ,tayi mugun basa dariya ,Sai yayi dariya ce zuma sai da wuta . Tun dazun yake kunshe dariyarsa .yasan da be mata haka ba bazata taba cin abinchin ba .

Shima mikewa yayi ya kwashe kanukan da sauran kayan ,ya Zuba ragowan su kazan a frige sanna
Ya Kai kwanunkan kitchen .

Dakinsa ya wuce ,Kai Masha Allah dakin yayi mugun yi kyau ,Komai fari , bathroom ya wuce yayi wanka ,yayi  alwala ,
Bayan ya futo, ya shirya cikin kayan bacci farare ,ya feshe jikinsa da turare
Sanna ya futo ya kaman hanyar dakin iman....................

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now