Page 51

672 22 9
                                    

  Cikin mintunan dabasufi 30 ba umma da mommy  Suka gyara  maijego da jarirai  tsaf, d'akinma aka gyarashi, kaikace ba'a haihuba.

    Gyara gidan akayi  mommy ta dakko kayan Jarirai da tazo dasu masu k'yau.

        Turaren wuta masu kamshi  ta kunna, Dan danan gidamn yad'auki k'amshi, aka sakama jarirai fararen kayannan Na sanyi, sun musu kyau ,duka kamansu daya a yanxu baa banbambace mace dana namijin, sai barci suke hankali kwance ......

Shugowa dakin ahmad yayi ,idonsa ya sauka akan wasu 'kyawawan 'ya'ya ,masu shegen kyau kaman larabawa .
bakinsa d'aukeda addu'a ya 'daukesu , wani farinciki yaratsashi, wai wannan nasane, kai 'ya'ya k'yautar ALLAH, ya mannesu duka k'irjinsa tareda lumshe idanunsa.

hawaye suka fara Fita daga idonunsa ,bakinsa yana d'an motsawa ahankali, dagani kasan ALLAH yakema godiya , yakai tsawon lokaci ahaka sannan yabud'e idanunsa akan yaran , yashiga sumbatarsu daya bayan daya ,ya kalle mace ya kalle namijin kaman me son karantar Wani abu a tattare dasu


      Alhmdllh, maijego da jarirai lafiyarsu lau ,an kira doctor ya duba lafiyarsu ....

Sai wajen magriba daddy da malam suka zo duba yaran......
Dakko yaran akayi ,malam yace a bashi abokinsa ,malam yace a bashi matanshi ,daman mommy ta tsufa ,haka suka dakka yaran cikin murna,yaran Sai bacci suke abinchi ......
Malam ne ya ha'da yaran duka yana musu addua .

Daddy ne yace a kira masa iman . Autace ta kirawo ta .
Cikin ladabi ta durk'usa gaban daddy  tana gaidashi, ya amsa da kulawa, yana tambayarta jikinta.

     Kasa amsawa tayi saboda kunya, takumayin k'asa da kanta tana d'an murmushi, daddy  yanata zubamata addu'oi da albarka, ahankali take amsawa da ameen
Malam daya dawo yanxu yana tayata amsawa cikin murna ,shima malam addua yayi na ,da albarka ....

~~~~~~~~~~~~~~~~

Washe gari aiba'a magana, gida yacika da 'yan uwa da abokan arzik'i, su Maryam
Da aneesa , kowacce danata cikin, Yayyen  iman  suma sunzo , su anty barister da doctor  ma tabiyo
Sunzo danta sun kasa  hak'uri sun zo .

Auta duk yan dangi ta tura musu hotunan jarirai ,
Duk Wanda basu zo ba har sun

Har hamma ta nuna masa,shi kuma na nuna na baba , duk murna ta kashesu ,

Ita hajiya anty barrister Ta tura masa

Yaran tabarkallah Masha Allah...............

Ana gobe suna yan gidan su iman suka zo matan su baffa ardo ,Baffa ayuba,matan babansu iman duka sunzo duk da wasu gulma ya kawo su , yafendo ma tazo da 'yayanta duk , iman taji dadi sosia sosai ganin yan uwanta sunzo sosai fiye da zatonta ......

          *RANAR SUNAN YAN BIYU*
Washe gari aka saka suna a massalacin anguwar bayan anyi sallar asuba.

      Yara duka ci sunan Muhammadu da aishatu (hanif da hanifa)
Akaita sakama yaran  albarka.

Muhammad Ahmad Bello
             &
Aisha Ahmad Bello
Allah ya raya cikin addinin musulumchi

Dagananfa shagali yadawo Na mata acikin gida.

     Aharabar gidan aka shirya walima iya mata zallah.

    Suma su Ahmad sunyi tasu daga 11am zuwa 1:0pm, saboda abokan aikinsa da abokansa, aikam nasha mamaki, dannaba k'aramin cika akayi awajenba, shi harma mamaki abin yayta bashi..  

  
      Ansha hotuna kam sosai, lamarin harba'a cewa komai.



4:0pm Na yamma  Mata sukayi  Nasu  shagalin acikin gida, babu k'arya ansha  cashe, lamarin harba'a cewa komai.

   Kai fans kun bani mamaki wlhy, Ashe haka kuka iya rawa ,Ashe iya rawa baa hijab ake ganewa ba,su mrs Abdul,xarathy ,blood,small sis ,Fatima walah ,Maman jani ,Gololo,Ummu Safna ,Ummu Abdul halq ,murjanatu,Maman abdallah ,yan al-Mar'atus  saliha , first class writers , novely librato ,flower novella, rudin zuciya Fan group babufa Wanda banganiba, munci random munsha zo6o, kowa saida yaciko jakka dakayan alatu, su Oooohhh ina kallonta harda guziri tayi a leda bakko😜, bandai fad'i sunaba ehe😏.




         Alhmdllh suna yayi suna, Aysha da Muhammad sunsha gayunsu, kuma sunyi koshi ,iman harda kuka tayi ,Dan ta  sha mamakin yadda mutane suka yi mata bajinta sosai sosai ..........

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
_____________

  Washe gari kuma bak'i sukaita tafiya d'ai-d'ai.

    Cikin kwana biyu kowa yakama gabansa, kaikace gidan baitara kowa ba .

         Umma  tace sai iman  takoma gidanta  kokuma gidam mommy ,Dan ita bazata bar mijinta shi kadai .

   Ahmad yaki yarda ,ya daka tsalle yadire akan bai aminceba, Umma  kuma tace bai isaba.

       Ankai ruwa rana kam kafin ya yarda dan dole iman  takoma gidan  Malam , saida daddy  ya saki bakima sannan.

    Aikam Ahmad yayi mugun fushi dakowa agidan, harma ita iman  kanta, wai Itama  da tace bazata je ba ,babu Wanda zai tilas ta mata .

A gurGuje plsss🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃🏿🏃‍♀️

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 24, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now