Shigowanmu falon naga dukan su sunci ado cikin dinkin babbar riga mai yar ciki da wando, malam da Ahmad na Sanye cikin Farrar shadda kamar kowace jummah, shikuma Mubarak Sanye yake cikin shadda mai ruwan madara wacce aka yima aikin hannu da golden din zare, sai baza kamshi yake kana ganinsa ba sai ancemaka shine angon ba domin kuwa yayi kyau matuka.
Maryam ce ta kalle mubarka cikeda fara'a tana masa kirari ,irin na Ango
"Ango ango kasha kamshi"
Duka dariya suka saka cikeda murna,Nima dan murmusawa nayi ganin sun burgeni sosai.
Ummace ta futo dauke da turare a hannunta ,kasancewar wannan Aladace a gidan duk ranar jummuah,fisamusu tashiga yi daya bayan daya ba kakkautawa, tana ma mubarka kirari itama,nikam babu abunda nake sai murmushi.
Kowanne su fita yayi su shiga motacidon zuwa filin daurin aure, Mubarak da Ahmad zaune suke a mota sai kuma wasu abokansu gida biyu, shikuma malam da sauran iyayensuna cikin wata motar,
Tafiya suka Dan ba mai tashi ba, kowane yafito fuskarnan tasa cikeda Annuri, batareda Bata lokaci ba aka daura auren Mubarak da Amarya akan sadaki naira Dubu hamsin.
Mikewa kowa yayi yanufi Mubarak don gaisawa dashi da kuma yi masa Allah yasa alkhairi, shikuwa kamar An masa Bushara da aljannah bakinan nasa yakasa rufuwa, gakuma maroka dake ta masa kirari yana musu barin naira, karshe gajiya yayi bai ma gaisa da wasu ba Ahmad ya jasasuka wuce.
Direct gurin reception suka isa, wato Inda aka tanadi abinci da abinsha kala kala Don baki, Anci ansha komai Alhmdullh kuma biki yayi biki,
Daga karshe kuma aka kaimasa amaryarsa daki bayan suma sun sha kalar masu bakin dakuma pixs don tarihi.
Bayan kowa ya watse a gidan Amarya, misalin karfe goma Ahmad ya rako Mubarak dakinsa dauke leda a hanunsa, afalo suka yi sallama, Ahmad na kara masa nasiha sosai, murmushi Mubarak yayi tareda cewa wai tuzuru kema Ango nasiha yafada tareda fashe dariya, girgiza Kai Ahmad yayi tareda cewa plss a rangwantamata,
Key yasaka ya kullule gida bayan Ahmad ya fita ya kashe duk fitulun tsakar gidan sannan yashige dakin da yake tunanin nan ne dakin amaryarsa,
Da sallama ya shiga dauke a bakinsa...... nikuma da ganan nayi reverse da Dan littafina a hannu tareda cemusu asuba tagari Amarya da Ango.
*Ahmad kuwa yana lafiya yana tunanin ,har tunda mubarka yayi ma nasa iyayensa biyayyah na auren aneesa Mai zai Hana shima yayi ma nasa iyayen biyayyah ,duk da dai bai San waye zai aura ba ,amma iyakan abunda ya sa a ranshi yasan iyayensa bazasu taba cutar dashi,gashi dai yaga aya Akan mubarka babu Wanda zai ce ba auren soyayyah mubarka yayi ba ,lura da yadda yar ta yin shaaninsa hankali kwance,Allah yasa mu dace * ahmad da fada duk acikin zuciyarsa,tare da danna horn ,Dan ya iso gida
//////////////////////////
Bayan sati daya
"Assalamu alaikum " Mubarak ya shiga falon malam fuskarsa dauke da murmushi,
"Wa alaikhumus salam"cewar malam ya Kara gyara zama,
"Ina Wuni malam."mubarak yafada tareda da dan durkusawa cikeda ladai,
"Lpy qlau. Ango, bismillah mana zauna, ya nuna masa gurin zama sa hannu, Ya amaryar taka"
"Alhmdllh, tana nan qlau" cewar Mubarak tareda shafa kansa yana Sunne Kai kasa alamar kunya,
"MashaAllah MashaAllah. Ka gaishe ta"
"Zata ji da kyau, inshaAllah" malam.
bayan sungama yan gaishe gaishe malam yayi gyaran murya tareda cewa
"Dama na Kira Kane kazo Kai Kadai, sbd Ina so in maka magana akan abokin Ka Ahmad!Malam ya numfasa ya Cigaba "Akan maganar wacca zai aura ne! To daman iman ce Matar da muka zaba Masa Amman bamu gaya masa ba, sannan haka mukeson tsarin ya tafi harsai bayan auren nasa, indan yaje dakinsa ya ga matar tasa, so yanzu ya kake ganin abin zai kasance?
Shiru mubarak yayi, ziciyarsa na bugawa da karfi, duk iskar gun jiyake gaba daya wani uban gumi ke karyo masa,yama rasa Mai zaice,Ina ma zai iya tsintsuwa yabar wajen ba tare da malam ya gansa ba, don Idan bai kama kansa ba tofa malam zai harbo jirginsa.
Tattali sauran jarumtarsa yayi, ya bude yaki yace "malam iman dai ,khadijatu ta nan gidan wacce nasani"ya fada cikin dakiya duk da Haka muryanshi a shake take,
"Ehhh ita fa nake nufi "malam ya fada cikin Zakwaki
"Masha Allah gaskiya Ina taya abooookiiiinaaaaa murrrrrrna"ya fada a warware kamar mai koyon magana, yana kokari saisaita kanshi,
Kalanshi malam yayi ,tare da nazarin shi "tohmm yanxu mene shawaranka game da boye masa da nace ayi?"
Dan sauke kansa yayi tareda cewa "malam ni a ganina da An fada wacece zai aure da hakan ya fi, kuma Ahmad ya rigada yayi naam da batun, kuma Ahmad yaro ne mai biyayya dakuma hakuri, insha Allahu babu abinda zai faru sai alkhairi, Idan kun Bani dama ni zan iya Sanar masa wacece matar tasa"ya fada cikin jarumta
Jinjina Kai malam yayi cikeda gamsuwa yace, gaskiya kayi tunani mai kyau Mubarak Amman bari zanyi shawara akan hakan sai mugani koh,
To shikenan malam nagode kwarai Allah yasaka da alkhairi,
Ameen Mubarak Allah shiyi albarka, insha Allahu zan nema,
Yafita falon malam da kyar don jiyake kafarsa na barazanar yardashi, shiru yayi yana tunanin idan bai taya abokin nasa murna bekyauta ma rayuwansa ba,duk son da yake ma iman zai iya hakura ya barma ahmad,Amma idan yaji iman zai aure ya zeyi tunda shi yasan yana sonta ,haka nan zan hakura tunda nayi aure kuma bani da matsala da Matata.
Kuma Ina da tabbacin idan Ahmad tassss zai hakura
Tohmm yanxu zan iya fada masa kuwa ..........
Kodai abi shawaran malam .
Wayyo Allah ya zanyi ..................
![](https://img.wattpad.com/cover/200537846-288-k548411.jpg)
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......