Zama iman a gidan su Ahmad ba karamin farin ciki yake sanya mommy ba ,tana jin dadi zama da iman ,haka auta ma
Kafun mommy ta tashi har ta shirya auta ta Musu breakfast,
Itama autan tana jin dadi sosiaTsakanin Ahmad da iman kuwa ,Sai abunda ya karu kullum Sai sunyi video call ,yata bata lbr soyayyah ruwa ruwa 😂😂😂
Satin su ahmad daya da tafi kenan
Kusan kwanakinta uku kenan batajin dad'i, k'irjinta namata ciwo, dauriya kawai takeyi bata son mommy Ta gane .
Kitchen din taje zata daura abinchi , takasa yin abinchin saboda jiri datake gani kad'an-kad'an.
Gashi mommy ta futa ,auta yanzu zata dawo makaranta ,Bata San me zatayi ba , d'aki ta dawo ta kwanta , shiru tayi tana tunanin qalbee dinta , tunda yatafi take jin wani changi a jikinta ,Amma ta alakanta haka da missing dinsa takeyi ,
Waya ta daga ta kirashi , ringing din farko ya Dauka ,kaman yana expecting kiran a lokacinDauka yayi suka sha soyayah ,Amma tayi kokarin karya gane halin da take ciki , suna cikin wayan auta ta dawo .sukayi sallama
Iman tace "auta wallahi kaina ciwo yake mun ban samu na yi miki abinchi ba"
Cikin tausayawa da kauna auta tace "Allah sarki adda ,sorry kinji ,babu Komai bari na dafa mana indomie zaki ci ?"Daga mata kai iman tayi ,sannan auta ta wuce kitchen.
Indomie ta dafa musu me rai da lafiya ,
Ta kawo musu
Iman ta zauna saka ci
Nan take iman taji zuciyarta na tashi Sai tace "auta dan dakko min ginger din nan a frige din kitchen "
Dakko mata auta tayi, sha tayi sai taji daidai , tana mamakin yadda bata damu da ginger juice ba Amma yanxu tana son ta sha shi ,yaji citta da kayan kamshi~~~~~~~~
Yau ta kasance Friday kwana su ahmad 9 da tafiya
Iman da auta suka shirya suka je gidan malam yini
Umma Sai korafi take musu, wai kwana biyu basu shigo ba ,tana kallon iman ta fara tuhumar ta , taga tayi wani fari ne sosia , gashi mamanta sun chichi ko kaman me shayarwa, Amma Sai ta kame bakinta tayi shiru kawaiMikewa umma tayi wai zata daura abinchi , fankasau zatayi da Miya ,
Auta ta mike zata taya ta ,ita kuma Iman tace Sai ta huta , kallon mamaki umma tayi mata ,sanin kanta ne iman bata da 'kiwa ko dayaMurmushi umma tayi cikin Jin dadi tace "kima yi zaman ki ni bance ina son a tayani Yima mijina abinchi ,tsohon shekara 57 babu Wanda ke taya ni , Nike yin kayana ahhhheehhh😏"
Dariya iman tayi bata ce Komai ba sanin halin umma
Ita da auta sukayi fankasau da Miya ,ita iman tana Chan tana waya da mijinta ,
Sai da suka gama miya ,saura kadan su gama suyar fankasau iman tazo , babu Wanda yace mata ta Tafasa sauke ,
Guri ta Samu ta zauna babu abunda take Sai surutu kaman radio ,(iman din da surutu be dameta bane ta koma haka 😂😂😂)Ana gama wa ko kwashe baayi a kitchen din ba wai zata ci ,ita yunwa take ji
Umma dai yau tana kallon ikon Allah,
Cewa umma tayi "kin taba ganin na hana wani abinchi a gidannan ?, kije ki zuba mana "Mikewa tayi taje kitchen ta zuba fankasau gida biyar ,tana bude miyan taji ba zata iya ci ba
Sai kawai ta dakko sugar ta sakaDaga auta har umma babu Wanda bata sa dariya ba ,Allah sarki iman baiwar Allah Sai kawai ta fashe da kuka😂😂😂😂, daidai an malam da daddy suka shigo sun dawo masallachi,
Su samu su umma da auta na dariya , iman na kuka
Ga uban abinchi a gabanta wanda ko wani namijin bazai cinyeba"Iman lafiya kuwa"cewar dady
Kunya ce ta rufe iman tayi shuru tana goge hawayeShi kuwa malam harara ya dalla mata
Itama tayi Banza dashiSai yace ma daddy "Wace wannan zata cinye mun abinchin gida "cewar malam cikin zolaya
Kwabe fuska tayi bata ce Komai ba ,Dariya dady yayi ,su malam suna zolayan iman dady hana shigar mata .
Haka suka ci abinchi suka tashi
Ita ko iman sanda ta cinye abinchi ita daya😱(lallai Ahmad kana da aiki)
A nan dai iman da auta suka yini Sai bayan isha'i suka koma gidaSuna zuwa gida mommy tace sun mata yaji
~~~~~~~~~~
Washe gari bata tashi daga bacci ba Sai 11, haka yake wanan mugun bacci , bama tasan tana yi ba Sai idan ta tashi .Mikewa tayi da wani mugun yunwa , tana tashi taje tayi brush , ta futo dakin mommy taje ta gaidata tasan daddy ya futa ,ita mommy futa zatayi ,tare suka jera mommy tayi hanyar waje ita kuma idan tayi dining
Tea ta fara hadawa ,Sai chips ,egg and plantain , jikinta har rawa yake ,tana kokarin sawa a baki taji ance "wifey indai Ina nan , Ai bazan bari kiba kanki wahala ba wajen ciyar da kanki...............................

YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomantikaIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......