"Assalamu alaikum baba kun karaso "cewar hamma cikin farinki
"Wa'alaykumus sallam ,tohmmm kace Musa bismillah su shigo "cewar baba yana kokarin mikewa ,
Mazane suka shigo su uku ,Sai kuma bayansu yara ne dauke da akwatina ,suna shigawa sashen baba ,
Baba ya taresu cikin murna yana nuna musu wajen zama ,suka zauna ,a haka yaran suka Cigaba da shigo da Kayan ,bayan sun tafi sanna suka fara gaisawa cikin natsuwa ,
Sai hamma ya shigo ,bayanshi kuwa ,step sister din iman ne dauke da tray na Kayan snacks,drinks da ruwa .suna zuwa da Kayan suka tsunguna suka gaidasu cikin natsuwa kansu a kasa ,suka amsa sanna suka juya suka tafi
"Barkanku da yamma"hamma ya gaishesu cikin natsuwa
"Barka dai mun same ku lafiya"suke amsa da farin ciki a bayyane da fuskansu
"Madallah sannun ku da zuwa"cewar hamma
"Sannu dai ,Masha Allah,kaya ne muka kawo na lefe ,kasancewar yamma tayi zamu wuce ,hanyar bata da kyau "
Godiya suka yi ,suka mike
Tashi hamma yayi ,ya musu takeaway din su drinks din da sauransu ,sannan ya musu rakiyan ,zuwa bakin mota ,ya samu Komai da Komai ,da wani farin envelope ✉ dauke da kudi naira dubi Hamsin (50,000)Bayan sun tafi ,hamma ya daga Kai ya kalle mahaifinsa yace ,nikam baba da zaa bi tawa ,a bar kayannan a dakin nan,Kowa yazo ya kallah,idan an gama nan da kwana biyu na dauka na kaiwa su malam kano ,daga nan kawai a ajje su kawai a Chan".
Daga Kai malam yayi cikin gamsuwa da bayanin da hamman yayi sannan yace "ehhh kana ne ,amma yanxu Ka samo yara kasu dauke a Kai sashen Ardo da Ayuba su gani sannan ,sanan naka iyayen sunzo nan su gani da sauran yaran gida"cewar baba
"Gaskiya ne baba ,hakan zaayi "cewar hamma cikin gamsuwa da bayanin baba ./////////////////////////////
Kayane na alfarmfarma akwaiti 10Akwai set din maroon Mai akwaiti 4
Wanda babban ke dauke da atamfofi guda 37
Na biyu kuma lace da shada da material guda 30
Na ukun kuma underwears cike da kanan kaya
Na karshen kuma vails da hijabsSai wani set din pink Mai Akwai 3
Babban ke dauke da bags,shoes
Na biyun bracelet, harda gold guda biyu
Na karshen kuma su sujud ne da al-QuranSai wani box 📦 Mai guda uku
Duka cosmetics ne a ciki
Su perfume kaman suyi magana
Da dubu ashirin kudin dinkiKayan ne ,Sai Wanda ya gani ,
Gidan yayi shiru kowa Sai kallon yake , wasu da murmushi a fuskansu wasu kuwa tsabar bakin ciki ne, wasu kam sun futo Fili sun nuna nasuHaka dai aka gama masu cewa ,daman ta tsaya Ruwan ido ne ,shiyasa bata yi aure da wuri ba ,gulma kala kala ,balle gidan yawa ,gashi kuma a kauye daman abun sai a hankali , kafun kace mene gari ya dauka ,iman zata yi aure,kuma mai kudi ,wai an kasa sanin aikin shi😂😂😂😂
/////////////////////
Ahmad ne zaune a gaban malam sunyi shiru Kowa da alama damuwa a tattare dasu
Hankalin Ahmad a tashe yake sosai tunda yake da malam bai taba ganin malam yayi shiru ba ,duk tuaninsa kan malam ,gaba daya hankalin a tashe yakeShi kuma malam ,Tunani yake ta yadda zai fara fada ma Ahmad wanna labarin,duk da yasan Ahmad yayi Dace sosai indai ya aure iman ,amma dasun sani tun daga farko sun fada masa da wanna labarin
Haka kawai yayi shahada ya fada masa
"Ahmad kana jina"ya tambaye Ahmad ya kula ya nisa a tunani
"Ehhh Ina ji"cewar Ahmad da alam Tsoro a tattare dashi
Kallonshi malam yayi tare da karanta shi sosai kafun ya fara cewa "ba kowa bace kace........."dariya malam ya fara ganin yadda Ahmad yayi ,duk na rikice ya kosa malam ya fada ,Ahmad kam gaba daya zufa ya jikashi ,idon shi yayi jaaaaa,
"Kana ji koh Ahmadu ba kowa bace bace iman "cewar malam ya tsaresa da ido yana son ya Karanci me ke zuciyar malam
Yayi irin zazzafan huci tare da wani sassanyan ajiyar zuciya da ya biyo ,
Malam ,Ahmad ya dago ya kallah da idon shi da yayi red,Sai ya samu kanshi da kasa kallon malam din , rasa wani tunani zaiyi , farin ciki zaiyi ko kuma bakin ciki ,
Saidai a iya saninsa ba son iman yake ba ,Amma shi yasan yana crushing mana ,duk abunda take birgeshi take (nace ahmad Zaka ma fadi gaskiya kuwa 😂😂😂😂)
Kallonshi malam yayi da mugun mamaki ,a tattare dashi ,Dan Ahmad yayi mugun basa mamaki ,ji yadda yake murmushi ya manta da malam din a wajen ,koh tunani me yake ohoKafadansa malam ya taba , nan da nan Ahmad ya zabura ,Dan ya manta a gaban malam yake ,
Malam yace "Ahmad Kai nake saurara fah "
Shiru Ahmad yayi kaman ruwa ya Shanye shi ,sanda malam ya kuma magana sanna Ahmad yace "malam har duniya ya nade bazan taba kin jinika Ka ba ,Kai malam koda tsohowa yar shekara 80 kace na aura zan aura balle iman jikan Ka , Insha Allah malam bazaka taba samun matsala daga wajena ba ,na gode Allah ya saka da alkhairi"cewar Ahmad murya na rawa ,gaba daya jikinsa yayi sanyiShima malam jikinsa ne yayi sanyi ,sanna ya daga Kai ya kalla Ahmad, sannan yace "ba Komai Ahmad, nine da godiya ,alfarma daya zan nema a wajenka karka nuna ma iman cewa Kai zata aura "
Kar kada Kai ya hauyi kaman wani karamin yaro cikin gamsuwa da baya nin malam ........../////////////////////////
"Oyoyo uncle "cewar wasu yara suna kokarin zuwa su rungume Ahmad
Nanda na fara ansa ya karu kasan cewar ya son yaran sister din shi sun zo ,yana mugun son yaran sosai
Rungumeshi sukayi suma suna muryan
"Chuchu yaushe kuka zo "ya tambaye Namijin
"Uhmmm in d morning muka zo "ya fada cikin muryan yara
"Mummy tana ta neman tun dazun"cewar macen
"Ohooooo my baby tohmm muje"
Yaja hannunsa suka tafi ,yaran suna ta tsalleAngo ango ango
Cewar babban yayansu tana ta mishi bud'aMurmushi yayi ya rasa me zai ce"ya Hindatuu kinzo kenan tun kibi ki takura mutane "cewar Ahmad cikin Zolaya,
"Ehhh din ,nazo kenan,yanxu zan shirya naje naga amarya ma gwanda kaji ma kuwa"itama ta fada cikin zolaya .
"Ya Ahmad Ina wuni cewar nusaiba ,autan su ahmad"
"Lafiya qlau auta,Ina Maryam " tana daki
"Bari naje wajen daddy na dawo"

YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......