page 18-19

285 25 3
                                    

Abinchi muke ci hankali kwance ,bayan sun gama ne ,na kwashe kwanukan , na wuce Daki ,ina tunanin maganar da Malam ya fada min dazun , aure fah , wai nice zanyi aure .

Allah sarki babana nasan sai yafi kowa jin dadi,
"Wayyo ni"na fada cikin murna
"Wait wait wai wait amma wazan aura ne ma ?"

A haka dai Ina ta wannan tunanin, har lokacin Islamiyya yayi na shirya na tafi.

/////////////////////////////////

"Assalamu Alaikhum" na fadi, tare da shiga ofishin headmaster, Kai na a kasa

"Wa alaikhumus salam" Malaman dake ciki suka amsa.

Bayan mun gaisa ne, na nufi wajan bookshelf din da ake ajje littafen da Malamai ke amfani da su wajen koyar da dalibai, a bangaren seerah, na dauki murshidul dullab,Wanda zan koyar da en aji uku.

Jikina ne, ya bani ana kallo na, na juya in gani, Sai Muka hada ido da headmaster,da sauri na Mayar da Kai na kasa. Nayi sallama da malaman na fita daga ofishin.

Har na gama darussan da zan koyar yau, hankali na, na kan ganin dalilin da Malam Aminu ke kallo dazun.

Kai na girgiza, _*uhm iman, ki Bar tunanin nan a ranki, watakila ma kawai co'incidence  ne, kina overthinking ba gairu ba dalili *

//////////////////////////////////

Alhamdullahi alhamdullahi ..............
Baban iman kana nufin Mamanka ta samu miji ?, Masha Allah ,ni Malam din ba bai fada min ba
Wai kuma *Ahmad*
Kai gaskiya abu yayi dadi sosai , gashi yaron akwai hankali ,Kai "Alhamdullahi" cewa hajiya mahaifiyan iman cikin matsananchin farin ciki Mara musaltuwa💃💃💃

"Hajjaju kenan ai nafi kowa murna da wannan , abinchin da kika kawo min ma saboda murna na manta banchi  ba😂😂😂 ,Kai Masha Allah
Gaskiya bazan sa auren da wuri ba zan hada auren me da saura "Cewar baban iman  Kusan ma ya fita farin ciki .

"Assalamu alaikum  " cewar hamma da ke kokarin shigowa cikin farin ciki lullube a fuskan cikin  annuri

"Wa'alaykumus sallam" suka amsa a tare

"Barka da yamma baba"cewar hamma yana kokarin tsungunawa

"Barka dai ,da fatan Ka yini lafiya ,ya Iyali?cewar Malam cikin so da Kauna tsakanin da' da uba

"Lafiya qlau kowa yake "cewar hamma tare da juyawa inda yaga hajiya tana zaune

"Sannu da Hutawa hajjaju da fatan kin yini lafiya"
"Lafiya qlau Dan albarka Ina kishiyata?"
"Lafiya qlau suke duka "

"Malam naji labari Mai dadi naji bazan iya bari ba sai Nazo da kaina"

" Kai yayansu maimakon Ka bari saida Safe "
"Ai Malam idan banzo ba banjin zan iya bacci sosai ..............

/////////////////////////////

"Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun ........
Me daddy yake nufi dani ne hasbunallahu wa Niimal wakeen ,ya Allah Ka kawo mun *sabuwar rayuwa*
Kaman ni *AHMAD* ace ba daddy zai mun aure nan babu dadewa,kuma da wacece ban sani ba ,sai kace a film yawwo ni 😭😭😭"cewar Ahmad ya fada cikin tashin hankali Dan maganar tayi mugun  Taba'shi

*Yanxu nan da 4week aure tunda zaa hada dasu maryam ,da me da me zanyi ,gashi mubarak baya cikin kwanciyar hankali, wayyo ni😭😭😭, mema ake yi idan zaayi aure ,ni gaskiya bazan wani banzan bidia ba gaskiya kam ,me zanyi?*


"Ahmadu lafiya kuwa tunda nazo Ina ta magana baka jina? Ka tafi wata duniyar daban ,ina ce lafiya koh....."cewar Malam da ya shigo tun dazun yana ta magana Ahmad baya ji

Wani nannauyan ajiyan zuciya ya sauke tare da wata wahallaliyan hamma ma'ana baici abinchi ba tun safe da daddy ya fada masa mgnr."sannu Malam , lafiya  , lafiya qlau"

"Ina lafiya ? nazo Ina ta magana baka ji ,kuma da alama kana Jin Yunwa"Cewar Malam cikin nuna kulawa
"Malam daddy ne yake son ya sani cikin matsala kuma yasan bazan taba masa musu ba ,amma bai duba min ba sosai, Malam aure Zai mun , Ina laifin ya fada yace na zabi mata ,amma

/////////////////////////////
Ya kuka ji novel din

Idan a cigaba
Ina son naji comment da Sharhi sosai Akan novel din......

Daga taku har iya kullum
Ameera madobi

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now