Amma mene??Ahmad na zaune a nutse, kafafunsa a kalmashe kansa akasa yana sauraron malam,
Malam yayi kyaran murya irin nasu na manya tareda cewa "kayi hakuri da iyaye Ahmad,kasan iyayenk ka sunada Iko da Kai ,sannan kasan bazasu taba yin abunda ba zai cutar da kaiba,kuma nasan Kai yarone Mai biyayya ga iyayensa , Don haka nasan zakayi alfahari da wannan auren,yanxu abunda nake so dakai Ka rungumi kaddaranka ,Ka kuma cigaba da addua, Allah yayi maka Albarka" cewar Malam cikin Muryan lallashi , da nazari irin Nasu na manta.
Ahmad gyada kansa yayi cikeda gamsuwa yace "Malam Insha Allah babu wata matsala, kuma zanyi biyayya da duk abinda iyaye sukeso ,Allah ya sanya haka shine yafi alkhairi" yakarashe zancen cikin murya mai sanyi.
To Ameen, Ameen yaron kirki, Allah yasa sanya Albarkaa ciki, malam yafada cikeda farin ciki.
"Ameen" Ahmad yace shima cikin murmushin yake, Yawwa Dan gidana ,maza a fara shirye shirye,wai Ina Mubarak Ka turomin shi ,Ina son ganinsa kaji malam ya bashi umarni.
"Insha Allah zan fada masa "cewar Ahmad
*iman iman iman* taji malam nakiranta cikin babban sauri.
"Naammmmmmmmm"na fada tare da karasowa, a tsakar gida na gansu zaune su biyu, don umma bata nan ta tafi makwota karban haihuwa .
"Yawwa yar albarka , Dan kawo ma yayanki abinchi kinji" cewar Malam cikin muryan lallashi Dan ya kuwa nima Ina cikin damuwa
"Na masa da tohmm, amma ina zuwa naga babu abinchi, Sai dai na dafa masa indomie" na fada cikin dauriya saboda tsohon soyayyah da nake ma ya Ahmad zai iya sani kuka idan na kallesa
//////////////////////////
Mutane ne zaune Bisa tabarma ,kowanne cikin shiga na alfarma duk Wanda kaga fuskan kasan akwai tsantar farin ciki da annashuwa.
Tabarman farko Alhaji ilyasu mahaifin iman ne zaune ,Sai Baffa Ardo da Baffa Ayuba dakuma Liman
Dayan tabarman kuma , Alhaji Bello mahaifin Ahmad da kannensa uku , Sai abokin Alhaji Bello
Bayan an gabatar musu da kayan ciye,ciye Dade sauransu
Cikeda manyance, Alhaji bello ya fara magana "kamar De yanda kuka sani bawani abu ne yatarumu nan ba face Alkhairi, A Inda mukazo nemar ma Dan mu Auren yarku.
Sauran iyayen dake gurun suka gyad'a Kai cikin gamsuwa,
Batare da bata lokaci ba, suka gama magana aka Tsaida biki nan da 4week.
Godia sosai iyayen Ahmad sukayi da karbar girma da akayimasu kafin daga bisani suka tafi.
/////////////////////////////
Kallonsa kawai yake kaman wani wawa ,tunda ya shigo baice Komai ba "my guy lafiya naganka haka ,nida ya kamata a gani a hakan amma kaine kake wani pretending din Banza "cewar Mubarak yana hararan Ahmad
Banza Ahmad yayi dashi ,Sai tsaki yake ,yayi tsaki yafi a kirga tun Mubarak na Banza har ya kare da cewa"my guy tashi Ka Barmin daki,Ka barni da abunda ke damuna ,yanxu saboda rashin tausayi maimakon kazo muyi magana akan abunda ya kamata muyi tunda saura 2weeks bikin amma kazo kana mun iskanchi"ya fada yana huci ,ransa ya baci sosai
Shiru Ahmad yayi ,yana tunanin bai kyauta ba ,saboda shi shaidane da Mubarak dinne da Tunun ya kirasa ya fada masa duk da shima yana cikin matsala ,amma yakamata ya sauraresa "kayi hakuri my guy bazaka gane yananyin da nake ciki bane ,zauna muyi magana Dan Allah karkace aaa"cewar Ahmad cikin muryan Sassanya murya.
Kallansa mubarka yayi ,Sanin Ahmad da yayi tashi zaiyi ya tafi bazai ce Komai ba ,amma tunda har yace haka bari ya sauraresa "Ina jinka "cewar Mubarak ya fada tare da ya zauna
Shiru Ahmad yayi ,ya rasa ta inda zai fara Mashi bayani ,ya saki ajiyar zuciya yakai sau uku sanna ya fara masa bayani dalla dalla ...................
///////////////////////////////
Bayan *SATI BIYU*
Komai yana tafiya daidai ,domin kuwa na kwantar da hankali na rungume kaddarata ,duk fargaban da nake na rasa wanda zan aura ,duk na barma Allah Komai ,
Hayaniya naji sosai sosai a falo ,
Kasancewa yau Friday
Naci kwalliyata cikin wani ash lace da red vail takalmi da bag duka red ,nayi kyau sosai ,a Raina nake cewa dama haka vail yamin kyau ,tunda ba gwanar sawa bane,badan Maryam ba bazan iya sa gyale na futa ba,Sallaman Maryam ne ya dawo dani daga tunanin Dan shiga .itama tasa kaya irin nawa ,sakamakon bikin Mubarak yau ,*Ahmad* ya siyan mana ankon
Kallona ta fara sama da kasa ,tana murmushi ,ta rasa me zata ce "wow wow in-law na kinyi kyau sosai sosai ,wayyo Allah ya kamata na bada tukuci"Maryam ta fada tana fadada murmushinta cikin Jin dadi
Wani kallo na mata ,Mai hade da Harara "waye kuma in-law din naki ,sunan daga Ina? "na tambayeta duk da nasan ta fada cikin tonan fada ne
Hahahahaha dariya ta fara harda rike ciki "ke tsaban kinmun kyau ne yasa na fada shirme"cewar Maryam cikin pretending tana Allah Allah kar iman ta kuma cewa Komai
"Ke gafara min na wuce"nace mata saboda shirmenta bame karewa bani.

YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......