"*Malam Dan Allah wani bawan Allah ne yayi aure kafun a kawo amaryan ya saketa , shine yake son maido da ita ,Tambayana a nan shine zai CE ya maidota ne?, ko kuma zaice zaa daura sabon aure saboda bata da iddarshi?*" cewar iman, kanta a kasa cikin kunya, duk da tasan a neman ilimi babu kunya
Wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, sai da yayi 5min yana tunani, dayan malamin da su Ahmad kowa yana son yaji ta bakin malamin, dan wanan tambayan abun dubawa ne
"Tohmmm Alhamdulillah , khadijatul iman kinsan ilimi kogi ne yana da fadi, a nawa fahimtar insha allah
Amsar tambayarki shine maidata zeyi batareda sake aure ba tinda ba saki ukku yamata ba Idan saki ukkune , sannan indai an daura suka kebanta tsakaninsu su biyu, kinga tana da iddansa, amma insha Allahu zan kara bincikawa zuwa gobe, idan kinzo insha Allah" cewar malam, yana jinjina tambayan a cikin ransaAhmad ne ya mike tare da miko ma malam hannu suyi sallama, shima Mubarak ya mika masa, mukayi sallama , muka futo.
Tafiya mukeyi wanan karan babu wani mai magana kowa da tunanin da yakeyi
Ni ina tunanin*ohni yar baba ta ina zan fara koyarwa a islamiyyan , duk da nasan ina koyarwa a book, Allah dai ya rufa min asiri*Ahmad*gaskiya tana da ilimi haka ne son mace, shiyasa kullum nake takura su Maryam dan suyi karatu,amma alhmdllh,kai amma tambayan da tayi tazon idan da nine cewa zanyi sabon aure , Allah ya kara mana sani*
Mubarak*wow gaskiya beauty na ta birgeni, gaskiya bari na maza nazo nayi proposing dinta kafun wani ya rigani*
~~~~~~~~~
Malam ne ke zaune a dakinsa duk tunanin iman ya damesa , har mafarkinta yayi, yana tufka yana warwara
Chan sai wani tunani ya fado masa, koyama Ahmad magana dan tafi kama da yar uwansa, dan ya kula da irin kallon da Mubarak ke mata*uhmmm duka bari na gyalesu , zamu cigaba da tafiya ina nuna mata so har Allah ya bani saa, naxo na fada mata*
"Tabashi yaji anyi ana malam da sanyin safen nan kake ta tunani tun da na shigo nake ta magana amma shuri babu amsa" cewar matansa asiya da ta tsaresa da ido tana jiran amsan shi
"Mata ta gari ai banji shugo wanki ba, amma kiyi hakuri kinji" cewar malam cikin lallashi yayi magana
Kai kawai ta girgiza masa , ta mike ta tafi dakko masa ruwan wanka
~~~~~~~~~
Mabarak!!!!!!!!!
"Naam ammi" cewar mubarka dake sakko wa daga bene..
"Barka da asuba"cewar Mubarak yana Sosa kai saboda yasan yayi laifi , jiya tace bayan asur zaje dakko wata cousin dinsa a airport amma ya ki zuwa
" barka dai, an tashi lafiya, ai nasha har yanxu haka gidan ne ai"cewar ammin
"Ammi kiyne
hakuri""Sai ka zo kayi breakfast idan kaso"
"Tohmm ammina , Allah dai ya biya ammina"
"Ya Mubarak ina kwana " yan biyu suka hada baki wajen gaishe sa
"Yan biyun ammi kun tashi lafiya" cewar Mubarak yana kokarin zama a kujeran dake tsakanin su dan dama haka suke zama kullum idan abinchi zasu chi
Wata zazzakan murya yaji a kunnensa yana cewa "ya mubarak ina kwana"
Shidai harga Allah bai ganta ba tunda yazo wajen, amma yaji bakon turare "lafiya qlau aneesa kinzo lafiya ya Hutu"
"Alhmdllh"
"Masha Allah , ina su akeehy da su Ummi da abbi"
"Duk suna tafiya "
Kawai sai ya jawo abinchinsa ya fara ci
Ringing din wayan sane yasa ya ciro ta Ahmad ne
Mubarak:hello guy
Ahmad :kai ka shirya kuwa
Mubarak: yes abinchi nake ci , insha Allah yanxu zan futo
Ahmad: chop chop kawai
Kafun Mubarak yayi replying har Ahmad ya katse kiran ma
~~~~~~
Suyan kosai nakeyi hankali kwance , saiga Maryam ta shigo da sallama .
Iman an tashi lafiya,
"Lafiya qlau ina umma"
"Tana lafiya qlau" cewar Maryam tana kallon tsakar gidan bata gibtawan umma ko malam
"Su malam basu tashi bane" cewar Maryam
"No yanxu suka bar wajen nan"
"OK, dama zuwa nayi nace zaki raka kasuwa duba anko.""Okk babu damuwa amarsu, bari su umma suzo na fada musu, kaman karfe nawa?"
"Wajen 10 , OK babu damuwa" cewar Maryam
"Miko min wancan kulan na zuba muku kosain " cewar iman tana pointing ma kulan
"Okhhh tohmn"
~~~~~~~~
"Kai bazaka ci abinchi bane " cewar daddy da yake kallon news
"Noooo kasuwa zani akwai wasu kayan da zaa siya ne masu yawa, yanxu Mubarak nake jira, Wai zaiyi breakfast ne" cewar Ahmad
"Okhhh, kaiwa wuce kayi breakfast din" cewar daddy yana nuna masa dining
Assalamu alaykum .
Wa alaykumus sallam
"Good morning daddy"
"Morning daughter kin tashi lafiya"
"Lafiya qlau "
"Ke me wannan ?" Cewar Ahmad yana pointing kulan da ta shigo dashi
"Kosai ne iman tayi shine ta zubo mana" cewar Maryam tana kokarin zuwa koko a cup
Mikewa Ahmad yayi ya nufe dinning yana ma Allah godiya dama baya son cin chips and egg din da Maryam tayi
Zama yayi yana cin koko da kosai hankali kwance
Har ya gama sannan ya miki ,ya dauki jakanshi , ya futo,
Tsayawa yayi a gidan malam dan ya gaidashi ,sannan ya jira Mubarak dan a motar Mubarak zasu kasuwan yauSallama yayi
Na amsa masa tare da gaishe shi.........................
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......