page 12

340 21 0
                                    

Iman!!!!!!
Naam umma

"Futo Mu shirya musu abinchi yanxu zasu dawo" cewar umma ta shirya cikin kamfalan ta

Na futo ina mata tsiya"Wai wannan kwalliyan haka ba"

Karba naki , tana min daku'wa

Baki na turo, ina kunkinai "ace mutum bazai huta ba tun safe kin hana mutum ya huta, daga girki sai wanchan "

"Ungo wani ta kuma min daku'wa "

Sai kawai nayi murmushi

Haka na ringa futo mata da kayan abinchin da drinks din da nayi ,
Muka jera da plates da cups

Muka zauna zaman hira , tana bani labarin zaman kirki da mutunchi da sukeyi da gidan Alhaji bello ,tana cewa duk ranar jumaa anan suke cin abinchi , su kuma umman su Ahmad duk ranar lahadi a nan suke yini gaba dayan su

Sai Mubarak abokin Ahmad kullum idan basa kasuwa suna nan gidan

Abunsu kwanin ban sha'awa

A haka suka zo suka taddamu

Assalamu alaykum

Waalaykumus sallam

Sannu da zuwa muka musu
Suka amsa

Sannan umma ta gabatar  musu da abinchi

Abinchi tuwon shinkafane da miyan alaiyahu , Sai pepper chicken
Sai kunun aya da pineapples da milk drink (dan umma tace Ahmad da Mubarak basa shan kunun aya)
Na zuba musu daya bayan daya , sannan umma ta umurcheni da na zuba mata da ni kaina

Na zuba mata
Nace mata ni na koshi saidai kawai nasha drink din

Haka suka zauna suna ci

~~~~~~~~~~~~~~~~~~

"Assalamu alaykum babana"

"Waalaykumus sallam"

"Barka da juma'a babana "

"Barka dai, ya mutan gida da su malam dafatan kowa yana lafiya"

"Lafiyan kowa qlau , yasu mama da Baffa da sauran mutan gidan"

"Su nanan lafiya qlau"

"Masha Allah"

"Iman Allah ya miki albarka , yasa ki gama da duniya lafiya , ya baki miji na gari, Allah yayi ma karatun albarka, iman ki kara hakuri , Insha Allah komai zaizo da dauki"

"Amin ya Allah "

"Tohmmm baba na gode sosai Allah ya kara lafiya da Nisan kwana, Allah ya albarkanchi rayuwan da kayi da Wanda zaa karayi a duniya"

"Amin yar albarka"

"Nagode baba na barka lafiya"

Kittt na kashe wayan tare da sauke nannauyan ajiyan zuciya ,ina mugun son babana , shiyasa a kullum nake son kiransa  saboda yawan adduan da yake mun kullum
Kullum ina adduan Allah ya kawomin *sabuwar rayuwa* yadda baba yake son ganina cikin farin ciki da annasuwa

Duk da haka ina godema Allah , dan nasan na chanza a gidan malam da nake shiga cikin mutane ana raha dani
Alhamdullah

~~~~~~~~~~~~~~~

Bayan asur , ina kwance ina karanta novel din sanadin boko a wayata ,na Halima k/Mashi
Hankalina ya tashi lokacin da hafsat tace ma Abubakar ita karuwace gashi a gaban Hashim , kuma ina mugun son suyi aure, kawai sai na fada tunani

Sai muryan umma naji tana kirana na

Amsawa nayi cikin sanyin murya dan gaba daya novel din ya kashe min jiki

Na tashi nasa hijab dina na futo

A tsakar gida na gansu zaune suna fira ita da yan gidanta Ahmad da mubakar , suna ma mubakar tsiya wai yaji dadin England yaki dawo wa da wuri

"Yar tsohuwa gani" nace ma umma ina Dariyar mugunta dan ta tsani ace mata tsohuwa

Kafun tayi magana Mubarak ya chabe yana cewa...................

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now