Page 23-24

324 21 7
                                    

SAURA KWANA BIYU BIKI
"Haba iman sai kace karaman yarinya kina sane da Wanda zai kaimu ,banma San wani tashin hankali bane yasa ya Ahmad yace zai kaimu ba ,salon ya ishemu da balain sa"cewar Maryam tana hararanta ,saboda sanin halin yaya Ahmad.
Kallon iman tayi sai ta kyalkyale da dariya "sorry tawan ai bazaayi haka ba mu tafi na fasa wanka "
Cewar iman tana kokarin zura hijab dinta

A falo suka taradda da malam kyauta (mai 'ya'ya mata kyauta Allah ) zagaye da yayansa mummy barrister,mummy doctor,Sai mummy nurse ,da yayansu gaba daya .hajiyatane kawai bata zo ba ,dalili kuwa babana yace ya bar ma malam  aurena  ,daurin aure ne kawai zaayi a Chan,

Mummy nurse tace "my baby sai Ina ?"
"Mummy saloon zamu "
Duka Allah ya kiyaye suka mana
Sanna muka tafi,
A kofar gida muka tarad dasu ahmad ,da mubarka a mota
Muka musu salama
Suka amsa
Sanna maka shiga baya
"Sannu ku ,Ina wunin ku "muka hada baki wajen gaishe su
Amma abun mamaki ya Mubarak ne kawai ya amsa
Bamu damu ba sanin Halinsa
Kallon gaban Motan nayi
Aiko ina daga kaina muka hada ido da yah Ahmad ta madubi ,Sai ya wani  basar kaman bashi ne yake kallona ba ,nan da nan gaba ya fadi
Nayi maza na Kauda Idon

Ya mubarka ne ya Katse shirun da cewa "amare  ranar juma'a"cewar Mubarak yana dariya

"Kai ya Mubarak cewar Maryam tana rufe fuska"
"Ni kuma murmushi nayi nace ya Mubarak Ina amarya "juyowa yayi yana harara na ,
"Tohmm shugaban Marasa mutumchi ,da kika ki zuwa zaki wani ce ina amarya"cewar Mubarak
"Ya Mubarak ba laifi na bane laifin Maryam ne "
"Maryam ne tayi saurin cewar wallahi karyane ya Mubarak ,Kai iman Kifada gaskiya fah"cewar Maryam tana balbaleni da harara
"Kai Maryam , idon ki zai fadi ,ki rufa min asiri fah "cewar iman tana dariyan mugun ta

Motar ne ya tsaya ,duk muka kallah juna da Maryam ,sanna maryam tace "yaya yi hakuri "cewar Maryam tana nuna masa hanyar da zai bi zuwa wajen saloon din ,tsaki yayi sanan ya Kama bin kwatamce da take masa
Muna zuwa daidai saloon din ,ya juya ya kalle ni sanna yace "idan kunsan da akwai na miji a saloon din ku dawo "cewar Ahmad yana yamutsa fuska
Kai kace yaga kashi .
Mu kuwa ko a jikinmu
Muka sauka
Ya Mubarak ya bamu envelop yace ga kudin saloon Maryam ta amsa mukayi godiya .
/////////////////////

Maryam Aka fara mawa ,sanna ni
Bayan an gama ma Maryam ,ta koma gefe tana ta waya da Wanda zata aura ,amma ni banma San wanda zan aura ba ,nan da nan naji hawaye na shirin Zubomin ,nan da nan nayi saurin maidasu Dan kar su zubo .amma gaba daya zuciya a tunkushe yake
Ina ta adduan Allah yasa wanna auren ya kawo min *SABUWAR RAYUWA*.
Har aka  gama min ,Sanan Maryam ta yanke wayan
Tana cewa "Masha Allah amaryanmu gaskiya kinyi kyau sosai"cewar maryan mudubin wajen na kallah , kaina sai sheki ,ga Kai din bakin wull,Sai kwalli yake

Harara nayi sanna nace "ke dai kika sani ,ke lokaci yaja sosai ,yanxu naga text din mummy nurse cewar Mai Lalle tazo "cewar iman tana kokarin nunawa Maryam text din
"Chab gaskiya iman muna ruwa ,Dan samun abun hawa a nan zaiyi wahala mu isa da wuri "cewar Maryam so disappointed
"Tohmm muje dai mu gani"cewar Maryam a Sanyaye
Sallama suka yi mata Mai saloon sanan suka kama hanya

"Ke iman kalla "cewar Maryam cikin tsananin mamaki , Dan abun yayi mugun bata mamaki
"Lah Maryam ,gaskiya Alhamdullahi,Allah ya yi ma su ya Ahmad albarka ,Ashe zaman jiran mu suka tsaya yi,ai gaskiya naji dadi sosai "cewar iman cikin farin ciki
*lalle ya Ahmad,har ya fara Kishin iman ,Ashe zamu sha kallo kuwa ,Sai ya ta wani basarwa yana wani bakin hali ,Allah sarki my iman Allah ya Baki hakuri da ya Ahmad,Maryam ce ke gulma a cikin zuciyar ta*
Karasawa mukayi
Muka  yi Musu  Sannu
Amma ya Mubarak ne kawai ya amsa ...........

////////////////////////

Zaune muke an gama mana Jan Lalle saura baki ,
gidan cike yake da Dan uwan mama ,duka cousins Dina na wajen Mamana duka sunzo , Duka sun zagaye mu ,Sai neman fada mu da sharri suke mana,yawanchi ma duka masu aure ne ,gaskiya abun yamin dadi sosai
Haka muka zauna gaba daya ana Fira Ana dariya ,nan da nan na manta da duk wani damuwar ta

LALLE  dai an gama  yayi kyau sosai ,Jan lalle Sai sheki yake ,yayi dark maroon sosai ga Zanen na zamani abun baaa cewa komai ,ga bakin zanen shima yayi kyau sosai sosai gaskiya babu karya nayi  kyau sosai, baa magana
Ni kaina na sani
Saidai nace Masha Allah

Text ne na gani a waya ,da number din malam din islamiyya ,cewar Akwai waliyam da suka shirya mana ranar juma'a bayan daurin aure

Shiru nayi Ina nazarin wazan fada mawa
Haka nan na tashi naje na fada malam , Shima yaji dadi sosai sosai..............:


//////////////////////////

RANA BATA KARYA ,SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA
Yau ta kasance  juma'a , yau aka daura auren
Ahmad Bello zamfara
Da khadijatul iman ilyasu
Akan sadaki naira dubu hamsin ,saboda albarkan auren ake so
Aurene Wanda ya tattari mutane da yawa saboda aurene ya 'yaya har guda biyar(gaskiya dole a jinjinawa baba ,auren 'yaya mata ba kadan ba )

Chan na hango malam da mutanen da su baban Ahmad ,
Kai gaskiya mutane da yawa sun hallachi daurin auren

Baza idanu nayi ko zanga Ahmad, don dauko muku rahoton shigarsa,

Aikuwa Chan na hangosa
Ahmad da yaci kwalliya cikin wata arniyar farar shadda, idan ka hangosa da nesa kace man gyada aka zuba masa saboda maiko da shaddar keyi, dinkin babban riga aka masa na zamani ,Wanda suka sha ado da golden aikin hannu ,hulansa ma golden ,haka ma agogonsa da takalmin shi sau ciki , fuskan nan sai annuri fuskar sa dauke da farin ciki marar misaltuwa don jiyake yau his d guy kamar anbasa tiketin aljannah,Sai baza babbar riga yake ga wani ni'imtancen kamshi dake ziryartar hancin duk wanda ya rabe shi ,dan kusan kala goma ya fesa , Banda kuma wanda hajiya umma da mubarak suka fesa masa.

Gafe Gudu gayyar su Mubarak ce da sauran abokansa suna take masa baya suma sunyi ba karya bade kamar Mubarak wanda yafi kowa kyau acikin su Sanye cikin shadda mai kalar sararin samaniya (light blue) wacce tasha sitaci.

Sai murmushi yake zabgawa, har saida su mubarka da sauran abokanshi suka tasa shi a gaba ,suna cewa ya rufe bakin karda kuda ya shiga .....................

Ahaka yagama gaisawa da kowa sukashiga mota suka nufi reception.

////////////////////////////
INTERMISSION
Ku biyo ni cikin littafin sabuwar rayuwa
Dan jin ya rayuwan wainann ma'auran zai kasance ..................
Taku har kullum
Ameera sani madobi

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now