A dining ta jera komai na abincin lafiyayyen breakfast ne daga gidan mummy,
Zama tayi ta zuba uban tagumi tarasa yanda zatayi takira Ahmad, jitayi a jamata kumatu da sauri tayi farga daga tunanin datake taresa da Dan sa ki murmushi, Dan rankwafowa yayi saitin fuskar yana shakar ni'itamcen kamshindatake hankali cikin sanyin murya mai kama da rada yace morning wifey, Dan kallonsa tayi saitaga yamata wani mugun kyau sai walkiya yake cikin wata arniyar getzner mai ruwan toka, Dan ajiyar zuciya tayi don tasan Ahmad badaga baya ba gun kyau a hankali tace morning yaya, fuskar sa dauke da fara a yace kintashi lpia, Dan daga masa kai tayi,
Kujera tajawo masa daga gefenta ya zauna mikewa tayi ta fara bude wermers din wani kamshi mai mugun dadi ke tashi daji ba sai ance maka abincin ciki zai yi dadi ba, ta dauki serving spoon zata fara serving ya rike hannunta tare da zaunar da ita, serving ya shiga yi a plate yasaka spoon biyu tare da turawa gabanta, kallonsa tayi sai ya shafa ciki tare da nuna Cikin shi da hannu dariya ya bata sosai sai kace wani yaro Aranta tace dama haka ya Ahmad yake kamar kuwa yaji abinda tace shima yace nama wuce nan kauda Kai tayi tana tunanin yanda zata fara bashi abinci,
Jin shiru yayi yawa yasa ya jawo plate din tare da nuna mata kan laps din shi akan ta zauna da kyar ta zauna yacigaba da bata a hankali saida tankoshi sannan shima yaci yakoshi tare suka kwashe plates din suka shiga dashi kitchen suka wanke,
Kallo ya kunna musu a falo tana gefe yana gefe itade iman kallon tv kawai take bata ma San abinda akeyi ba duk ta tsargu a zaune tunani take yaushe zata sake da Ahmad ne kamar kowa, knocking dinda akayi a kofa yasa tayi saurin dawawo daga duniya tunanin da tafada mikewa Ahmad yayi a hankali yaje ya bude kofa handshakes sukayi ganin abokansa ne sai iya shege suke masa suna mai kirari na ango ango,
Da sauri ta Mike ta shige daki ta sako hijab ,ta Dan kuma kintsawa ,taje fridge ta dauko drinks da naman kaji ,ta shigo falon a hankali ta ajiye tare da gaishe su cike da labadi duk amsawa sukayi atare sannan tamike tashige daki,
Daya daga cikin su yace shege abokina ashe shiyasa mukajika shiru wannan aiki haka ah lalle Allah yasaka mu a danshinka yafada yareda kwashewa da dariya dayan dake daga gefen Ahmad yace Kai masha allah gaskiya Ahmad ka dace wallahi gata da kunya Allah de ya Baku zaman lpia, wanda yafara magana da farko ya matsatso kusa da Ahmad cikin muryar rada yace abokina Batada kanwa ne, duka Ahmad yakaimasa a kafada yace shege namamajo Batada, Dan marairaivewa yayi tare da cewa am serious fa wallahi, duk dariya suka haka suka cigaba da fira cikin nishadi da zolayar Juna sun dan jima kafin suka wuce saida sukayi sallama da iman suka bata 10k tayi godia sosai sannan ta wuce.
Bayan Ahmad ya rakasu yadawo ya tura dakin iman a hankali ya shiga zaune ya ganta gaban mirror tasake wanka tana shafa ganin sa tayi ta mirror ta Dan kwalo ido tare da cewa wayyo yaya plss kafita mana kamar zatayi kuka, infita kuma iman akan me kefa mata ce yafada yana kara takowa, dukewa tayi tare da rike towel din jikin ta,
Takowa yayi har Inda take fuskar sa dauke da shu'umin murmushi dafata yayi a baya tare da cewa haba wifey Dina tayaki dressing zanyi fa, wani mugun shock taji wanda yasa ta mikewa da sauri don ta Boye bayan waredrope Jan towel dinta yayi wanda yasa yacire gaba daya Dan zaro ido yayi don tinda yake bai taba ganin mace haka a gabansa ba, itukawa ihuu ta kurma tare da dukewa kasa tana hawaye, takowa yayi jikin sa sai rawa yake ya sungume chak ta dorata a kan gado, kukanta ne ya tsanan ta tana yaya plss kabari wallahi ban lpia haba yaya Ahmad plss mana ganin yaga cire Kaya yasa taja blanket ta lunlube jikin ta, (ni Ameera dagudu na rufe musu dakin nayi waje da yar takardata nace Asha amarci lpia).
Bayan kamar 3hrs haka Naga Ahmad yafito shirye cikin wasu kananan Kaya sun masa kyau sosai Amman ina ganin idonsa nagane harda barci yayi ma, makullin matarsa yadauka jin Ana kiraye kirayen sallar magrib yayi waje,
Dakyar iman ta Mike ta saka gown Marar nauhi tayi sallarta Anan ta zauna har akayi isha saida tayi isha tayi shafai da wuturi sannan tamike tasaka ma dakinta key jin Ahmad baidawoba ta koma ta kwanta, tana kwanciya taji karar motarshi, saurin duba time tayi taga karfe 9pm mikewa tayi a hankali ta leka ta window ta ganshi yana fitowa daga mota saurin sakin labulen tayi ta koma ta kwanta.
Bayan shogowarsa da kamar minti 30 yaji yana mata knocking banza tayi dashi ya dinga yi tama kashe Kwan fitilan tayi kwanciyar ta nan da nan bacci yayi gaba da ita, can tafarka Ahmad na ranta a hankali ta bude nan taganshi kowace a kofar dakinta bacci yayi gaba dashi, zuciyarta ce tayi sanyi ganin bata kyauta masa ba, a hankali ta rufe kofar ta koma ta kwanta.
A hankali Ahmad ya bude Idonshi shima saurin mikewa yayi yawuce daki ya aje ledodjin dake hannun shi ya kawanta ranshi ba dadi, Bawani bacci yayi ba daya kulle ido scene din dazun ke dawo masa ganinshi rungume da iman din shi ahaka yadinga juyayi, ita haka a gun iman din.............
*Comment n Share*
_The higher the comments, the sooner the next page_
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......