Page 33

297 20 2
                                    

Idon iman  yacika da kwallah, danjin wannan k'arfa-k'arfa, itadai addu'arta ALLAH yasa wasa yakeyi, ba irin abun shekaran jiya yake nufin mataba".
Haka ta runga basa yana ci ,
har saida ya tabbatar ya k'oshi sannan yace, "Alhmdllh dainamin d'ura hakanan, karna kasa sunnah anjima".

    Ita bamata fahimci Inda zancensa ya dosaba, tamik'e zata maida kayan kichin yace, "dawo aii ba'a gamaba".

      Dawowatayi tazauna, duk tsoronsa ya gama kamata, mamakinma wad'annan abubuwan dayakeyi take ita.

      Kunsan Mintina 2 sannan ya gyara zama ya yajuyo sosai yana fuskantarta, tiren yakar6a yamaida kan cinyarsa fuskarsa k'unshe da murmushi cike da soyayyah  yad'ebo naman yakai bakinta.

       ''Masha Allah , Alhamdullah Na k'oshi ai tunda kaci Alhamdullah ....ta canja maganar tata saboda uwar harara daya balla mata".

        "Kinga gwamma ma kici, Dan babu d'aga k'afa babu alfarma, Niba na chanza ba zaki  Biyani ba  aii, da zuciya d'aya nabaki".

    d'ago idanunta tayi takallesa Dan tabbatar da gaskiyar maganarsa, ya jinjina mata kai yana lumshe idanu, dukda ba yadda ta iya  dashiba bakin ta bude ya fara bata, haka yayta bata naman saida yaga taci da yawa sannan ya k'yaleta.

     Ruwan data kawo ya wanke hannunsa aciki, yad'auki cup yazuba fura, ita kuma yamik'a mata ice-cream Dan bata Shan fura ,
Aiko tunda taga ice-cream ta manta da wani biyan kaza (Sai kace mrs_Avbdool18  idan taga Ice cream uhmm😂🤣😁😂🤣)

Zama tayi ta nada abun ta hankali kwance .

Sai da suka gama ta kwashe kwanukan ta Kai kitchen ya wanke sanna ta dawo palour ta zauna ,kallonta yayi yace ta dakko alqurani suyi karatu ,baya son tashi , mikewa tayi taje ta dakkon ,suka fara Karatu daga suratul nisa'i zuwa anfal .
Sai wajen 10:30 suka gama
Sai ya mike yace bari yaje yayi wanka
Ita mikewa tayi tayi dakinta , tana shiga ta dakko key tasa dakin a ajje key din a side drawer .
Ta shiga wanka cikin farin ciki , tana cewa Sai taga ta inda zata biya kaza .
Idan ta tuna Sai tayi dariya .
Haka ta futo ta shirya cikin kayan bacci masu kyau , tana cewa"yau zanyi duk kalan shigan da nake so zan sha iska tunda ba iya shigowa  Zaiyi ba💃💃💃💃 "duk ta gama ayyanasa a zuciyarta .(ni kuwa nace yaro man chicken 😂😂😂)
Ta gama shirinta ta kwanta ta kashe fitila da side lamp yayi addua ta kwanta cikin kwanciyar hankali.

Shi Kuwa Ahmad sanda ya Kama Komai na aladar rayuwansa ,shima ya saka kayan bacci
Har ya futo palour ya Kashe switches din gidan , Sai ya tuna halin iman zata iya rufe kofa ,Dan haka ya koma dakinsa ya dakko spare key din dakin ya kwada cikin saa kuwa dakin ya bude
Iman ya hango rabashe akan gado
Dariya ta bashi
Kwanciyar yayi shima ya kashe wayoyinsa ta daurasu kam side drawer

    Cikin barci iman  taji ana shafata, abirkice tafarka, tazabura zata tashi ya maidata, cikin kunnenta yace, "k nutsu mana nine".

      Jikinta Na rawa tace, "amma ya akayi kashigo bayan Na kulle k'ofar?".

      Murmushi yayi, yakuma rungumeta da k'yau, cikin kunnenta yace, " haba 'yammata, zakici kazane a banza baki biyaba?".

              "Aii wlhy banciba, kaine kasakani dole naci aii, kuma ALLAH shine shaidata, cikin kuka tayi maganar".

       Yanda take magana tana kuka saita bashi dariya, cikin salonsa na jarumta   yana mata abinda ke k'ara firgitata.

          Tarik'e hannunsa tana fad'in, " naji kabari da safe zan biyaka  kazarka danaci".

         "Tab kinma rainani kenan, banason wata kaza, sunnah zanyi yarinya".

      Yink'urin tashi tayi yamaidata da sauri yakuma matseta.

       

🚶🏻‍♀Sum-sum nafito dannagafa ahmad  da gaske yakeyi, yauma bazan iya dakko rahotu ba , idan ba so nake umma ta mun duka ba ,,,,,👩‍🦯👩‍🦯👩‍🦯

Shi ba mugunta zai mata ba chicken.dinsa zata biyashi.😂🤣😂🤣😂

~~~~~~~~~~~~~~~
Washe gari
   Da k'yar iman  tatashi tai sallah, tun dare ahmad  ya taimaka mata ta gasa jikinta da kansa, Dan wlhy yauma tasha bak'ar wahala, azuciyarta tana mamakin masucewa aure da dad'i, ina wani dad'i anan ana azabtar damutum😢😜.

     Tana idar da sallah takulle d'akinta takoma ta kwanta, batawani dad'eba barci ya d'auketa, Dan barcin bai ishetaba.

     Sai around 9am tafarka, cikin hanzari ta dirgo daga gadon saboda ganin time.
Tana mamakin kalan baccin da tayi

Mikewa tayi taje tayi wanka
Ta shirya cikin bakar abaya ,ta shafa powder ta aka Jan baki ta feshe jikinta da turare masu mugun kashi
Tunani ta fara me zata yi yanxu
Me zata dafa ma ya Ahmad ?

Futowa tayi , tana zuwa taga palour Sai kwalli yake alaman yasha gyara ,
Buruntuuu taji a kitchen
Tana zuwa ya iska Ahmad yana musu breakfast ................😘
Ido ta gwalalo tace ..........................................

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now