page 52

255 16 3
                                    


Bayan sati uku da haihuwar Su hanif da hanifa
Ahmad ya dawo daga Dubai daya je saro kaya ,Tabbas yara sun San babansu yayi tafiya,Dan wani uban tsaraban da yayi musu kaman besa darajan kudi ba ,ita kanta iman Tasha tsabara ,su umma da mommy suma ba barsu a baya ba
har yanzu kuma fushi yakeyi da iman , zaidai shigo yad'auki yan biyu yafita, Umma ma baya kulata, yana dai gaisheta amma babu hira.

Idan kaji yana dariya tohmm da malam ne ,Dan shima be bada goyan bayan rike masa matanshi ba ...

*YAN BIYU sunyi bul bul abunsu ,ita kanta iman tayi kyau sosai sosai ,abunka da farare duk Wanda yaga 'ya'yan Sai sun tanka ........

Shirin tafiya gora ta fara ,ya rasa ta yadda zatayi ta tambaye ahmad ,gashi ko text tayi masa ,be cika reply ba ,idan ta kirasa ko ya kirata ,iya karsu gaisuwa . Ta rasa yadda zatayi da Ahmad ya sakko daga wanan fushi ,

Wani shawara ta yanke na cewa ta kirasa kawia

Wayan ta dauka ta kira Ahmad "Assalamu alaikum"
Daga bangaren ahmad kuma ya amsa da"wa'alaykumus salam ,masu jego kin wuni lafiya ,Ina twins"
"Lafiya qlau muke alhamdullah ,and you too?"
"Alhamdullah "
Sauri tayi ta fara masa magana ,sanin dana nan zai kashe wayan ne "qalbee plsss idan ka shigo unguwar su malam Ina son muyi magana da Kai " ta fada tana addua Allah yasa ya yarda

Shuru yayi na Dan lokaci sannan yace" nifa ba zuwan bane bazanyi ,Kinsan halin umma "
"Aaaa Abbansu Haneefa ,nima yanxu gidan mommy zani ,gora suka tafi da malam yanxu Sai yamma zasu dawo "

Shuru yayi , shima ya gaji da wanan fushi yana son matansu a kusa dashi ,yayi missing dinta sosai kam

Cewa yayi" tohmm mu hadu a part dina a gidan daddy "

Hanif ta dakko ya Goya ,ta dauki hanifa a hannu ta rufe kofan ,me gadi kawai ta gani a tsakar gida ta wuce part din Ahmad Sif sif sif ba tare da kowa ya ganta ba ...........

Knocking tayi ya tashi ya bude yana murmushi ,haneefa ya amsa yana cewa "Oyoyo yar baba ,sannu da zuwa "yana ta mata wasa
Ita iman burgeta sukayi ,tana ta murmushi abinta

Iman Ce ta daure tace"qalbee barka da rana "
Kallonta yayi sama da kasa tayi mugun yi masa kyau ,ji yayi kaman ya rumgumeta .
Iman jin Ahmad yayi shuri ,Sai tayi murmushi ,tunda tasan weekness dinsa sai kawai ta rungumeshi ,tace "Haba qalbee ,fushi ya isa haka , ace mijina yayi tafiya ya dawo ,ban masa sannu da zuwa ba ,sanna baya barin naji muryansa,baya bari naga dariyarsa , plss Ka tausaya na wanna yar yarinyar mana ,ko baka son na samu kwanciyar hankali da walwala, kullum da tunain kana fada dani nake kwana Haba my lollipop 😂🤣😂"

Shuru Ahmad yayi ,iman ta rigada ta gama dashi ,Sai yace"Haba dai yan mata ke da akace ki dena kulani ,ku kin rainani kema "

Shagwa6e murya iman tayi. tace, "to kadaina fushin dani please,and Ai kuma kulaka yanxu na fara ,su twins suna rokan ma na ammiensu Dan Allah "
Dariya ahmad yayi "an yafe miki "
Rungumeta yayi back , kissing d'in wuyanta yafarayi, bata hanashiba, saima wani salo data fara masa.

Aikam dandanan mutumin naku ya afka.

Mommy ce tazo ,zata aike Ahmad ,tunda taga motamshi ,dukdai be shigo cikin gidan ba

A kofar palour dinsa taga takalman iman ,mamaki ya cikata

Zuwa tayi ta kwankwasa kofar palour din taji a rufe ,buga kofar tayi baa bude ba .....

Su Ahmad kuwa Saida suka more iya morewa sannan Ahmad yabar iman , kunya dukta isheta.

Muryarsa sanyaye yace, " nifa gaskiya kuyi ayi arba'in d'inan, a hannu nake wlhy".

Iman tayi 'Yar dariya tana kauda kanta gefe.

" uhmmm , dariyama nabaki ko?".

" a'a fa".

In kuma naje na Kara aure ne shikenan tohmmm .

"Haba dai me kuma kara aure ,saura sati daya fa muyi Arabian fah"ta fada cikin kwaba fuska .......

~~~~~~~~
A bakin gate mommy ta samu daddy shida mai gadi ,tambayan me gadi tayi shin yaga shigowan iman,
Amsawa yayi da cewar "ehhh tun dazun ya shigo na "
Kai Kawai mommy ta girgiza ta juya ta tafi part dinta ,
A palour ta samu ta zauna ,shuri tayi tana tunani wauta irin na iman
Daddy ne ya shigo yana tambayan mommy lafiya"lafiya qlau ,wauta irin na iman ashe Ahmad sati uku baya kulata saboda yana fushi da ita ,Amma yanxu ta kwashe kafa taje dakinsa ,ya rufe "

Dariya daddy ,sanna yace "ki barsu baa shiga tsakanin miji da mata "

Uhmm kawia tace
"Kuma ban yarda ki musu magana ba balle ki fada ma umma ba "lokacinsu ne ,muma munyi namu "ya fada yana kashe mata ido 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️

~~~~~~~~~~~~~

Haka rayuwar tacigaba da tafiya, Su iman sun kammala arba'in, har gora taje tayi sati daya ,tasha gyara kam sannan aka maidata d'akinta, suka cigaba dakashe juna da soyayya itada qalbee dinta , suna tattalin hanif da hanifa , Wanda duk Wanda ya gansu Sai sun basa shaawa .

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now