Page 35

241 8 0
                                    


Wanka sukayi suka shirya ,iman tana ta Wani nokewa ,shi kuma ahmad Sai zuba uban rashin kunya yake 🙈🙈🙈(ni bazan iya dakko wanna ta rahotun ba ,umma zata iya zaneni 🏃‍♀️🏃‍♀️)

Nidai ganinsu nayi sun shira cikin wata Genza sky blue,  yasha wani arniyar aiki da royal blue Zare , ita  iman nata yasha aikin stone work a jikin shadda ,
Fuskarsu Sai Gyalli yake tabarakallah Masha Allah

Iman ba wani kwalliya tayi ba (she's not a fan of makeup,shima Ahmad ba wani so yake ba )
Hoda kawia ta shafa ,ta saka gazal tayi lining ido Sai lipstick din da ta saka .

Ahmad Sai kallonta yake yana murnushi kaman wani soko

Horn suka ji , hakan ya nuna musu bakinsu sun iso
Mayafi iman ta samu babba royal blue ta saka , suka futa kwananin sha'awa

Kitchen ta wuce
Shi Kuma Ahmad ya wuce budewa baki  kofa

Sallama sukayi suka shigo ,
Hamma ne da iyalanshi da Ka kannen su iman su 5

Iman tana ganinsu ta fasa kara taje ta rungumesu da guda Dan murna

Hamma Sai hararanta yake tayi ,yana cewa "Haba Maman baba har yanxu baki girma ba koh "

Dariya tayi ya kulle fuska taki cewa komai .

Zama sukayi anata fira da zolayar juna , sunchi abinchi ,sun huta
Lokacin sallah yayi sukaje sukayi sallah
Iman Sai farin ciki take , kaman yau take sallah a wajenta ,

Kannenta suna ta farin ciki , wasu kuma daukan rahoto ya kawo Su , wasu bakin cikin fal a zuciyarsu (note :dama aka rayuwa take ba kowa keson farin cikin Ka ba ,wasu ji suke kaman su kasheka )

Haka dai Suka yini
Hamma ne suka fara haraman tafiya ,zai wuce da iyalenshi ,kannen iman kuma zasu wuce gidan malam su kwana biyu

Iman tayi tayi a bar mata kannenta su kwana hamma yace sanda malam yayi warning nasu

Ganin ta damuna yasa hamma cewar kannenta su bari Sai yamma Ahmad ya kaisu chan .

Hamma da zai tafi Sai ya bata 10k
Amsa tayi tayi godiya

Ta hada ma matan hamma sha tara na arziki
Sukayi salllama suka tafi ............

Sai yamma Chan da magriba Ahmad ya wuce da kannenta iman ,suka ce mata sai sun zo kafun su tafi
Sallama sukayi suka tafi

~~~~~~~~~~~~~~

Bayan baki sun tafi , iman ce zaune ita dayan a gidan , ya Ahmad bazai dawo da wuri ba Dan daga  gidan malam  zai tsaya yaje wajen mubarak ,
Bata saba zama ita daya ba duk gidan be mata dadi gaba daya , ga kewar bakin da tayi ,ga kewar gida ,gashi babu watan nefa, mikewa tayi taje kitchen ,taga babu Wani aiki, ta wuce daki ta dakko laptop dinta ba bude ta rasa me zatayi Ita gaba daya, kawai Sai ta yanke shawaran tayi kallon, Indian film ta kunna me taken *HAPPY NEW YEAR*
Na sharuukhan

Tana cikin  kallo aka kira sallah mikewa tayi taje tayi sallah magrib ,sannan ta dawo ta Cigaba
Sai ga nefa sun kawo wuta ,haka dai ta Cigaba da kallo tun kallon na bata shaawa har ya dena , Sai akwai ta kashe system din ba tare da ta gama kallo ba

Sallah isha'i tayi tana mamakin me ya tsaida ya Ahmad har wanan lokacin, ga wani uban yunwar dake damunta
Kuma ya Ahmad yace kar tayi girki ,indomie zasu ci ,tafi son ya dawo Sai su tafa kar ya huce

Zuwa tayi ta dakko cupcakes guda biyu da maltina
Ta zauna taci , ta wuce tayi wanka ta shirya

Chan wajen 10:00
Saiga ya Ahmad ya dawo
Lokacin iman ta cika tayi fammmmmm....😂🤣😂🤣😂

Shine daya dawo fuskarshi babu annashuwa ko daya ,sallama yayi ya shigo ,Ita ta amsa masa ,tayi masa sannu da zuwa ya amsa ,yake tambayarta ya gidan tace lafiya qlau ,
Kujera daya ya samu ya zauna ,ita kuma ta bashi ruwa yasha ,sanna ya wuce daki yayi wanka ya futo ,Sai take tambayarsa a dafa indomie ?
Kai ya girgiza mata ,shi ya koshi ,yaci abinchi a gidan mubarak .uhmmm tashin sense ,nan iman ta kuma hawa .... Haba sai ga hawaye
Mikewa tayi ta wuce daki tana  kuka ,kuma ta rufe kofan kafun ya karaso babu

Magana yayi  tayi Amma Ina shuru ,ya ta mata Magiyan ta bude kofa ,Amma tayi ,shima gashi an bata masa rai ya dawo gida dana iman ,me makon ta tambayesa me ya tsayar dashi ko kuma ya akayi yaci abinchi a wani waje Amma kama kofa ta rufe , nan ranshi ya kuma baci dakinsa ya wuce ya kwanta be kuma neman iman ba

Turkashin nan 😱😱😱😱

Ga Ahmad ga iman
Waye yafi laifi a cikinsu ?????????

Shin ya zasu kasance ????????

Ku biyoni ...................

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now