Page 46

198 9 1
                                    

Sallama tayi cikin gidan mutane Sai amsawa sukayi suna kallonta ,da mamaki fal a zuciyar yadda iman ta koma kamar wata baturiya ga wani uban genza da ta saka a jikinta , gashi taui kyau ,skin dinta dai Kelli yake ,tana taku kaman wata sarauniya .

Gaishesu tayi cikin daddadan murya ,
Wasu ma basu samu natsuwar amsawa ba .........
A cikin  Yaran gidan  sai kallonta suke , kowa burinsa yay mata ta amsa ,yaran gani suke kaman ba Yayarsu  bace .

Ita dai iman bata kara bi takan matan gidan ba ,wucewa tayi dakin hajiyarta ,

A dakin hajiyar ta tadda auta ma , hand bag da gyale dinta ta ajje ,ta zauna suka gaisa da hajiya sosai
Fira suke yaushe gamo.......

Abinchi aka kawo masu ,shinkafa da wake daga gidan hamma ,Amma ita Iman tace Tuwon dawa zata ci ........

Adda Halima dake mata wani kallon sama da kasa suka kwashe da dariya ita da Zainabawa  da hafsatu.

    Hararsu tayi cikin wasa, "malamai lafiya?".
Cikin dariya adda Halima tace "Ashe kina cin Tuwon dawa😂🤣😂"
Kallon su zainabawa tayi da hafsa suka  dena dariya tunda sun san hali

Kallon adda Halima tayi tace "kawia shi nake son ci "

Hango bilkisu da ke wucewa tayi Ka kirata "Keesu  Tuwon  dawa nakeso miyar kuka ko kuɓewa ɗanya, asamo yajin daddawa da manshanu".

      "Naga ta kaina, Adda iman  wannan lissafin fa? To bara nakaima yaya Ahmad fura na dawo".

         "To maza, idanma babu manshanun a aika gidan ardo karami  nasan baza'a rasaba".

   Fita bilkisu  tayi tana amsawa, yayinda su Adda Halima  suka dasa sabuwar dariya.

A haka anty Amarya  ta shigo ma Iman  da tuwon dawa sai tururi yake, "Iman  ga tuwon, ga bilkisu can zata soya miki man shanun".

    "Lah anty  na sakaku aiki, maimakon kubar zainabawa  ko hafsat  suyi".

Dariya anty amarya kawai tayi ta wuce ....

Ba Iman kawia ba har su adda Halima sunyi mamakin Sauyawan anty Amarya ..
Shigo da man shanun da bilkisu tayi ne yasa babu Wanda yace komai ,
Zama Iman tayi za labci abinchin ta .kowa sai kallon Iman  yake, komai nata birgesu yakeyi, kallonta suke tamkar wata sabuwar halitta daban a cikinsu.

A cikin kananun maganganu na mata Iman  taji abinda ke faruwa ,abunda ya faru  da Baffa ardo ,wannan abokinsa wanda yaso Iman ta aura ne ,ya damfaresa
Yasa baffa ardo hada duka dukiyarsa wai zasuyi Sana'a dashi ya hade ya gudu dasu gaba daya .

Gashi ya gudu ya bar mata guda shida da 'ya'ya 36
Ga tashin hankali , idan anyi sata a unguwanan 'ya'yansa ne ,ko shaye shaye ga mugun caca ,subhallahi rayuwan 'ya'yansa sai a hankali

Allah sarki Iman har da kwalla ,sun bata tausaya,Alhamdullah ta ringa fada ,da tana tunin tana cikin wanna masifan  😭😭😭

Shi kanshi Baffa ardo ,tsabar tashin hankalin har dena gani yayi ,abinchi Sai an dafa a nan gidan zaa Kai ma gidansa , munafukan matansa masu zugashi duk sunyi sanyi  babu da Komai yanxu

A haka dai iman ta yini babu inda taje ,Dan Ahmad yace karta futa wannan zuwan saboda baba sukayi shi .

A haka dai suka yini sai 5 suka shirya zasu tafi , Amma auta bata nan ta raka zainabawa cikin unguwa ,suna tsaka da jiranta Sai gata ta dawo

Suka wuce gida..........

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now