"Bismillan ku , ga abinchi nan " cewar iman tana kokarin daukan nata data zuzzuba musu
"Yawwa yar albarka " cewar malam yana dariya
Dukansu suka zauna suna cin abinchi cikin kwanchiyar hankali
Sai k'aran cokula ne kawai ke tashi a gidan
Chan Sai Ahmad yace "kai jamaa amaryata kullum idan ina cin abinchi ki , Sai dai naji cikina ya cika badai bakina ba " yana magana yana hararan malam"Oho dai , Ku kuka sani, abinchi babu kalan Wanda banchi ba , eheeeeemmm" cewar malam yana rama hararanda Ahmad yayi masa.
Nidai ban kulasu ba , saidai kawai nayi murmushi
Suna ta fira sosai,abunsu gwanin ban sha'awaSai wajen karfe 10:30 Ahmad yayi mana sallama
Har ya kai kofa Sai ya juyo ya cemin"gobe ki shirya zamu cika application din postgraduate sjumaa
da malam ya fada min"
Sai nayi kaman ban jiba tunda bai kira sunana baImannnnnn!!!!!
"Naam " cewar umma tana taboni a zaton su banji bane
"Okkk tohmmm , Allah ya kaimu da rai da lafiya"
Murmushi kawai yayi
ya juya ya tafi dan ya rigada yasan rainin wayo nake shirn masa dan saida muka hada ido dashi sanda yake magana~~~~~~~~~~~~~~
Yau ta kasance jummatu babban rana
Ba abunda yake tashi a garin kano kaman kiraye kirayen sallar juma'a
Da akeyiDaidai lokacin na futo , na shirya cikin lace fari dinkin half gown ne da zani , sai NASA hijab kalan bagyondi da takalmi kalan hijab din
"Kai kai kai amaryata gaskiya dole na bada barka da juma'a wanan kalan kwalliya haka, chanchadi inyeeee"
cewar malam yana washe hakora, yayi kwalliya cikin fararen shadda , yayi kyau sosai dama aladarsace duk jumma farin kaya yake sawa"Uhmmm basaban ba , anzo birni zaa waye a kwacemin miji, Allah ya fiki"cewar umma tana mata hararan wasa
"Ina ruwanki dani , bakin ciki kike min" nace mata tana murkuda mata baki
"Kinji rabu da ita" cewar malam yana tura hannu a cikin aljuhu , ya ciro dubu daya yan dari Dari sababbi , ya mikamin
Na amsa ina Dariya tare dayi mata gwalo
Umma tana kokarin magane muka ji sallama
Assalamu alaykum
Waalaykumus sallam
Wani dattijo na gani ya shigo yaci wani babban rigan ash colour , Sai Ahmad da wani da ban sani ba suka shigi cikin fararen kaya
"Alhaji bello sannu da zuwa" cewar umma tana murmushi
Ya tsunguna yana gaidasu cikin natsuwa
Suka amsa cikin kulawa
Nima haka na tsunguna na fara gaishe shi" barka da juma'a daddy"
"Barka dai daughter, ya gida" cewanshi duk da bai sanni ba amma yasan tabbas ni jikan gidan ne da ummansu Ahmad ta fada masa nazo
"Lafiya qlau daddy"
Na juya na gaida su Ahmad da bakon
Suka amsa cikin kulawaUmma naga ta futo daki da turare da sujud babban a hannun ta
Ta mika ma Ahmad sujud din,
Haka tabisu daya bayan daya tana fesa musu turaren
Bayan ta gama ne ,
ta mika min turaren ,
ta zauna ta ringa musu addua sosai , saida ta kusa mintuna 5 tana musu addua ,
sanna suka futa zuwa masallachi ......Sai bayan sun futane nake tambayan umma su wayene????
Sai take cewa "baban Ahmad ne , da abokin Ahmad mubarak"Muma muka shige dan muyi sallah.......

YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
Storie d'amoreIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......