*WASHE GARI*
Tun 7am Ahmad ,ya shirya ya wuce asibiti , direct wajen doctor yaje ,suka gaisa ,ya tambayesa yame jiki ,ko kuma da wata matsala .
"Aaa malam Ahmad , babu wata matsala kam ,kuma jikin nata yayi sauki ,data tashi bacci zan sallame ku Insha Allah"Cewar likita
"Okhh babu Komai ,Allah ya kaimu "'Dakunan da yake kusa dana iman ya shiya ya gaigaida marasa lafiya
Sanna ya wuce dakin iman , umma ya gani zaune bisa sallaya tana Jan charbi ,
Tsungunawa yayi a gefenta
"Umma barka da safe"
Kallonsa tayi ,Sai tayi murmushi
"Barka dai ahmadu harka zo kenan "
"Ehhh nazo umma ,ya mai jiki, dafatan babu matsala koh ".
"Ehhh babu matsalan kam ,tunda ta kwanta bata farka ba har yanxu "cewar umma tana kokarin Mikewa
"Masha Allah,Allah ya bata lafiya ."
"Amin Amin ""Bari kaga na danje gida na dawo kafun ta farka Insha Allah , nabar Dan mijina a gida shi daya "cewar umma cikin zolaya tana kokarin gyara hijab .
Dariya ahmad yayi sannan yace"Haba dai wannna soyayyah zanga sanda zaa dena shi "cewar Ahmad cikin neman a fada
"Ai Wannan soyayyah Sai sanda muka mutu Insha Allah "ta fada tana kama hanyar futa"
Ahmad cikin ranshi yace amin ,muma allah yasa mutuwace kawai zata raba Insha Allah.
Waje ya samu ya zauna kusa da iman ,babu Wani abunda yake yi Sai kallon iman ,ya samu aiki kam .
Wayan mubarka ne ya tasheshi iman daga bacci daya kira Ahmad ,yana tambayan ko akwai abunda suke bukata zasu zo Insha Allah.Ahmad yana ajje wayan iman ta bude ido .
Kallonsa tayi cikin sanyin murya irin ta marasa lafiya tace qalbeeDagowa yayi cikin sauri yace "wifey kin tashi ,sannu kinji"ya fada yana dagata daga kwanciyar .
Bayan ya zaunar da ita da kyau tunda ta Samu sauki , Sai tace masa zatayi sallah ,
'Dagata yayi da kyua ,suka wuce toilet ,tayi brush tayi alwala yazo tayi sallah .Bayan ta gama ta dawo gadon ta zauna ,hannunta ahmad ya hada ya rike cikin hannayensa yana cikin wata annashuwa mara musaltuwa .
"Qalbeee me ya kawo ni hospital har aka kwantar dani ?"ta fada cikin damuwa Dan harga Allah bata San me ya kawota nan ba ..........
Dariya yayi yace "alkhairi mana "ya fada yana rumgumeta cikin farin cikiIdo ta gwalalo tace"qalbee alkhairi ne zaisa na kwanta a asibiti"
Kai ya girgiza mata sannan yace"wifey kin biyani saka makon kazata da kika biya 😁"
Kallonsa tayi cikin rashin ganewa Sai tace "qalbee ban gane ba ,wata kaza na biya ,nifa shiyasa na dena cin kaza idan Ka siyo!!!"Dariya yayi me karfi sannan yace "mrs Ahmad ,ciki gareki na sati 3"
Kallonsa tayi cikin firgici da mamaki tace "qalbeee ni keda ciki?"ta fada tana shafa cikinta Sai kuma kunya ta rufe ta,ta boye fuskanta a kirginsa
Dariya ta basa ,haka yata son yaga fuskarta Amma Ina taki dagowa ......,~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Mr and Mrs Ahmad da mr and Mrs mubarka ne tsaye a bakin office din doctor ya sallamesu
Zasu wuceAhmad da iman suka wuce ,suma su mubarka suka wuce .
Ahmad direct gidan daddy ya wuce , shi yafison ya wuce gidanshi ,Amma mommy ta hana .......
Suna isa suka tarad da mommy,cikin murna ta taresu tana tambayan iman ne zata ci
Cikin bata fuska iman tace, "Dambu zanci me zogalai da yawa"
Dariya mommy tayi tace "bari naje gidan malam na samo zogai Sai a miki kinji"
Kai iman ta daga alaman ta ganeSai mommy ta wuce gidan malam ......
Ahmad yace ma iman ta tashi taje wanka ,tace ita bazatayi wanka yanxu ba ,
Rokonta yayi tayi da kyar ta yadda
Shikuma yay murmushi yakaita toilet d'in Dakin auta .Dak'yar ya yarda yafito tayi wankan da kanta bayan yahad'a mata ruwa maid'an zafi, amma da ya dage saiya mata wankan dakansa.
Ganin shagwa6ar datake zuba masa zata sakashi ya narke, yasakashi hak'ura yafita.
Tanayi tana hutawa, haka tagama wankan, saboda jikinta duk babu k'wari, ga ko INA ciwo yake mata, musammanma mararta kuwa .
Koda tafito abakin gadon auta ta iskeshi zaune, yabud'emata hannayensa alamar tazo gareshi.
Akunyace tak'arasa tashige kuwa, ya rungumeta tareda gyara mata zama acinyarsa, ahankali ya sumbaci goshinta, murya k'asa-k'asa cikin kunne yace, " nizan shiryaki ko? Tunda kin hana namiki wanka".
"kai qalbee wai bakajin kunya? Mommy fa zata iya shigowa ta ganmu".
Hannu biyu yasaka ya tallafe kumatunta, sai raba idanu yakeyi a fuskarta, itakam takasa kallon cikin idonsa, saikawai ta lumshe idanu, ganin haka yayi murmushi tareda d'ora bakinsa akan NATA yashiga abubuwa.
Tun tana k'ok'arin kwace kanta harta hak'ura ta mik'a wuya. Saida ya sumbaceta San ransa sannan yacire bakinsa suna sauke numfashi.
Kunya ta lullu6e iman , tayunk'ura ahankali zata tashi Yakuma rik'eta da Kyau , "kinga yi zamanki , bara Na shafa miki man, nasan jikinki babu kwari sosai".
Dole iman tahak'ura ya shafa mata man, amma idonta arufe akayi komai.
Sai bayan sun gama ,shi kuwa wai ta rakashi part dinshi shima yayi wanka..........🤫🤫
![](https://img.wattpad.com/cover/200537846-288-k548411.jpg)
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomansaIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......