Page 49

220 14 0
                                    

Amsawa tayi da"ban zuwa bayan Ka gama kunya tani a wajenta "

"Haba wifey ,Dan Allah ki shirya muje wallahi ta miki girki fah,idan mukaje aka dunduma miki kika ci ,kinga abun yazo da sauki koh"

Kafa'da ta make alamar bazataje ba ,zama Ahmad yayi, yata mata dadin baki har ta yadda suka tafi

Suna isa gidan sukayi sallama a palour autace ta futo da gudu ta rumgume iman ,
Sannu da zuwa auta ta musu

"Auta ina mommy "cewar Ahmad
"Tana dakin  din dady ,daddy ya dawo cin abinchin rana yanxu zasu futo"cewar auta

"Okh okh , Ina abinchin da mommy tayi ma iman jiya "

Tunani ta fara yi Sai tace "yana cikin fridge,Ina tunanin ana ta saka shi"

"Oya je kiyi warming dinsa"

Mikewa auta tayi ta wuce kitchen

Suna zaune kusan 10min babu Wanda yace ma kowa komai ,kowa danna wayansa yakeyi

Autace ta futo daga kitchen tana ajje ma iman abinchin a bisa dinning

Dinning din suka je ,suka zauna ,iman ta kosa ta fara cin Tuwon ,Ahmad ya zuba mata Tuwon ,bata wani jira su mommy sun futo ba ta kama cin Tuwon nata ,
Ahmad da auta suna ta mata dariya ,Itako ,ko a jikinta,

Tana tsaka da cin abinchin ,mommy suka sakko ,
Kallonsu ta tsaya yi ,sunyi mugun bata mamaki,ta hade rai ,daddy kuwa ganinsu yasa shi dariya .

Kallon Ahmad mommy tayi ,Sai kuma ta kasa ce masa Komai ,Dan Ita abun ya rigada ya wuce tun tayi balbalinta

Gaishe dasu iman tayi ,suka amsa ,Ahmad ya gaidasu
Daddy ne ya amsa ,mommy kuwa ko kallonsa bata kara yiba ............

Bayan sun gama cin abinchi ne ,daddy da kanshi ya bama mommy hakuri on behalf of Ahmad din

Haka mommy tana ji tana gani ta hakura........

~~~~~~~~~~~~~~

After a month

       Kwance take tana kallonsa haryagama tsane ruwan jikinsa, ya d'akko mai yadawo bakin gadon kusada ita ya zauna, idonsa akanta yad'ora hannunsa Na dama bisa gishinta.

     "wifey  tunda zazza6in ya sauka kidaure kitashi hakanan kiyi wanka ko?."

     Yatsine fuska iman  tayi tana d'ora hannunta kan nasa, murya a sanyaye take magana, ''ALLAH qalbee  banajin tashinne, bank'i nawuni kwanceba batareda nayi komaiba, gaba d'aya sainaji jikina a kasalance."

        Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, ''karki damu komai zai dai-daita idan cikin yay kwari kamar yanda mommy tace, amma kuma ahaka da kikemin  zaki koma makaranta ?".

        "ALLAH qalbee  sonake nagama masters dinnan  cikin salama, kaga tunda na gama course work ,saura progect work ,kaga abun da saura ".

       " hakane, insha ALLAH kuma zaki k'arasa kinji. tashi muje namiki wankan mu shirya, bana son na fita  na barki haka ,kuma mubarak jirana yake ".

        "Kai qalbee ,  ina Zaka je  haka wai?".

      " , kasuwa zamu je, a nema na Kai ,na tara kafun babies su fara zuwa ."cewar Ahmad cikin zolaya
Dariya ya bama iman ,
Sai ya kuma cewa"ko da yake ga baby daya nan ,saura na zuwa Insha Allah "

     Batace komaiba ya taimaka mata ta sakko, kayanta tacire ,ta d'aura towel.

   Yace muje to.

      "A'a kayi zamanka Na hutashsheka, gamma naringa k'arfafa jikina, yanzu kwatsam tafiya ta taso maka wazai dinga tattalina haka? gamma Na daureda koyaya inayin wasu abubuwan ko?."

       Kansa ya jinjina mata yana murmushi

    Mai shima yashafa, sannan yafice d'akinsa domin shiryawa
      Itama iman  bata 6ata lokaciba tafito, adaddafe dai tad'an shafa mai, tasaka doguwar riga  ta atamfa , kayan sunmata k'yau, ta d'aukko madaidaicin gyale tayi rolling, tsaf tafito kamar wata balarabiya.
Tana cikin fess turare ne ya shigo da sallama

     Bata d'ago ta kallesaba amma ta amsa masa sallamarsa. tsaye yayi abakin k'ofa ya jingina da bango yana kallonta, tamasa k'yau sosai, hardai yakasa hak'uri ya tanka.

"Wifey wanan kyau fah,Ai Sai na kasa futa ma ,na tsaya kallonki kawai "ya fada cikin wata murya ,me nuna saukin soyayyah

Fuska ta rufe"Kai qalbee ,baka ganka bane shiyasa kake cewa nayi kyau, da Ina da daman sawa Ka rufe fuskanka da niqab idan kana fita ,dana sanya ka saka"

Kallon yayi cikin wani shauki sannan yace "Kai wifey na ,Al mar'atus saliha "

Iman ta bude baki zatayi magana ,wayan ahmad ya fara ringing ,kallon wayan tayi ,yasan ba kowa ne zai kirasa ba bayan mubarka ,

Matsowa yayi ,ya mata side hug da peck a kumatu ,yace "wifey saina dawo ,me zan kawo miki?"

Tunani ta fara sannan tace"ice cream,da dambun nama, a dawo lafiya"

Da Amin ya amsa ,sannan ya wuce yana daga mata hannu .

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now