"Habawa malam , bari kaga yadda ake soyayyah" cewar umma da take kokarin tashi daga inda take zaune.
Murmushi malam yayi tare da cewa" indai soyayyah ne , nine kankat koh amaryata"
"Chab me wanna tsohowar take nufi , har ana maganar soyyah ai bata isa tasa baki ba ,"cewar iman, tana hararan umma da wasa
"Amaryata kiyi ki sallameni zan kama hanya , insha Allah"cewar hamma da ya kallah lokaci a agogonsa
"Haba abokina tun yanxu zaka wuce "
Cewar AhmadMurmushi yayi ma Ahmad tare da cewa"abokina hanyar bata da kyau ne gwanda na tafi da wuri kar magrib tamin a hanya"
Umma ce ta taho da leda a hannu , tana cewa"kawai dai kana sauri ka tafi wajen kishiyata ne"
"Haba wa, ni na isa ina tare dana karfen fa" cewar hamma yana dariya kasa kasa
Ledar ta miko masa, yayi godiya tare da yi musu sallama ya kama hanya,
Gida ya rage daga Ahmad , iman,umma da malam.Chan sai malam yayi gyaran murya yana cewa "amarya tashi kije ki shirya kizo kici abinchi"
Tohmmn kawai na fada saboda bana son yin musu, dukda a koshe nake, haka na kama hanyar dakin .
"Bismillah bari na tashi na kawo muku abinchi, kafun ta futo muchi" cewar umma tana kokarin tashi
"Gaskiya kuwa , kaman Ahmad yunwa yake ji" cewar malam dake ta kallan Ahmad Wanda hankalinsa yake wayansa da yake charting da ita
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Maryammmm...mm mm
"Naam hajiya gani nan zuwa " cewar maryam da ke tafiyar sauri ta tadda hajiyan
"Yawwa Maryam je gidan malam ki kirawo yayanku Zan aikeku kasuwa" cewar hajiya dake kokarin zaman a gadonta
"Tohmmm hajiya sai na dawo" Cewar Maryam
"Kigaidasu kice ina ma amaryan malam sannu da zuwa"
"Tohmmm zasuji"
"Assalamu alaikum"maryam tayi sallama
"Waalaikumus sallam" suka amsa
"Lale da zuwa aminiyar arziki" cewar umma tana washe baki
"Sannu na sameku lafiya"cewar Maryam tana raba ido tana tunanin inda zata ga iman
"Lafiya qlau, wa kike nema halan "cewar umma tana mata alamar tambaya
"Hum mm bakuwarku nake nema koh bata karaso bane ?"
"Ayya ta karaso ta shiga yin sallah "
"Okhhh tohmmm ina yaya hajiya ta aiko kiransa, kuma tace tana gaisheku ,tana ma bakuwa sannu da zuwa". Cewar maryam
"Muna amsawa,iman yanxu zata futo ta shiga sallahne, sai Ku tafi tare ma"
"Iman iman iman" umma ke ta kiranta bata amsa sa
Mikewa Maryam tayi tana cewa" bari na kirata"
"Assalamu alaykum" cewar Maryam tana tsaye bakin kofan dakin , shiru taji , ta kara yin sallama shuru ,
~~~~~~~~~~~~~~~~~
Allah gani gareka , Allah yasa ma zamana a Gidan albarka, Allah ka kawomin *sabuwar rayuwa* Allah ka bani karfin gwiwan zama a Gidan nan,
Ohniii yau bazan kwana a Gidan babana ba, Allah ya kawomin dauki, Allah ya bani sa'a , Allah kabani miji na gari Wanda zai kawomin *sabuwar rayuwa*
Sai kawai naji ana jijjigani
Take na sauke wani nannauyan ajiyar zuciya
Tare da huci mai zafiMaryam CE ta kalleni tare da cewa" sis lafiyar ki qlau kuwa na kusan 5min a bakin kofa ina sallama amma baki amsa ba , shine nayi karanbanin shiga , da nasha ko kina sallah ne"
Murmushi nayi mata sanna nace "wallahi kinga na zauna bata lokacina ne,yah kike ?ya Gida,yasu hajiya?
Murmushin ta maida mata tana cewa" suna nan lafiya. Dama ummace tace kizo Mu tafi ki gaida hajiya "
Okhhh muje tohmmm
~~~~~~~~~~~~~~
Wai ina yarannan suka shiga ne , tunda na dawo sallah kika ce an aiko maryam kira na, amma shiru "cewar Ahmad dake tsaye tunda ya dawo sallah
"Nima abunda na gani kenan , bari naje na kirasu"
"Au kaga gasu nan zuwa ma"
"Ni nasha kunbar Gidan ne "
Murmushi sukayi a tare, suka cewa "yaya Mu tafi"
Suka yi ma su malam sallama suka tafi,
Sallama suke tayi a tsakar gida shuru babu wanda ya amsa harda me gadi
Sai kawai suka wuce cikin Gidan side din hajiyaLale lale da zuwan khadijatul iman
Tana murmushi ta duguna kasa tana gaida hajiyar cikin natsuwa "barka da yamma hajiya dafatan kun wuni lafiya"
Itama ta amsa cikin murmushi
"Barkanki dai da fatan kina lafiya ya gajiyar hanya''Alhamdullahi"
Sai ta juya gurin maryam tana cewa ta dakko list din da tayi a parlour,
Ta amsa da "toh"Ahmad kana jina
Ehhh ina ji hajiya"Zakuje yin shopping Dan Allah bance kayima kowa tsawa ba , Dan Allah kuje lafiya Ku dawo lafiya, kuma kuyi sauri" cewar hajiya tana kallonsa Dan tasan halinsa
"Ya amsa da Insha allahu hajiya zan kikaye"
*Uhmmm dama sunansa Ahmad , kai amma ya hadu , gashi mai kyau, amma da ganinsa zaiyi bakin hali, ehhh mana , gashi Dan zaa fita sai hajiyarsa ta rokesa karyayi fada *
"Iman ko bazaki bane"
"Naam zani ".
"Naji ina ta magana kinyi shuru ne"
Sai kawai nayi murmushi*********
Am so sorry kwana biyu kun jini shuru babu update
Amma Insha Allah komai yayi daidai yanxu
********
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......