Page 40

263 12 1
                                    

   Zaro idanu tayi waje, cikin matuk'ar firgita, waye yayi magana kaman qalbee , jikinta sai 6ari yakeyi takai dubanta kansa.

      Wata wawuyar ajiyar zuciya tasaki, '' qalbee ! Yaushe kadawo?".

       Kashe mata ido d'aya yayi , yana wani k'asaitaccen murmushi,matsowa yayi ya rumgumeta,yana mata wani irin kallo "wifey na dawo kina bacci ,mommy ta hanani tadaki ,wai har yanxu zazzabin ne?"ya fada cikin sanyin murya .

Kai ta ,girgiza masa alaman aaa
Dayaga alama kaman har lokacin tana fushi
Sai kawai ya fara bata abinchi ,karba ta rungayi kuwa , Ahmad tayi mugun basa mamakin yadda taci  abinchi ,kallonta kawai yake, be Kai da mamaki ba sanda ta gama shan tea ,ta fara nuna masa fridge,kuma taki magana ,mikewa yayi ya wuce wajen fridge din wani side ta fara nuna masa , alamar ya dakko mata drinks ,ya dakko coke tace no, haka dai yaya dakko wa tana cewa no har ya dakko cinger drink din .

Budewa tayi ta sha ,sanna tace masa thanks .
Dazun amai take ji ,data bude baki tayi magana amai zatayi .

Ahmad ikon Allah ya tsaya kallo .bashi da abun cewa ,Sai Sannu kawai yake mata taki amsawa .
Sai data dawo normal Sanna tace masa sannu da dawo wa , ruwa ya bata Tasha sanna ya dagata , zuwa tsohon part dinshi. Be jiyeta a faloba yanufi d'akinsa kai tsaye da ita, yasan yayi laifi dolene yayi lallashi.

Ko ina tsaf yanata tashin k'amshi, saboda gyaran da yayi masa daya dawo ,danshi mutum ne Wanda baya son datti ko daya,
Jallabiyan jikinsa ya cire daga shi Sai  boxer ya haye gadon.

     Jawo iman yayi , Sai fushin shagwaba take masa  jikinsa, tanata tureshi itakuma alamar karya ta6ata.

        Cikin sigar tsokana yace, "matan qalbee dinta, Ai fushin ya isa haka tunda  nadawoba koh, Wallahi kayanne aka samu matsala dasu ".

        "ina alkwawarin da aka min idan na dawo ......

       "Umh wani alkwawari kuwa , yakatseta da Sauri, zata k'ara magana ya d'ora bakinsa akan nata🤫...

🏃‍♀🏃‍♀.( Ohniii halimatu jikan halimatu ,Ahmad dinnan bashi da kunya fah😏)

~~~~~~~~~~~~~~

Bayan Komai ya lafa sunyi wanka sun futo ,Ahmad ya taimakawa iman suka gyara gidan ,har girki tayi yau(dama nasan missing Ahmad ne yasa ko girki bakya iyawa)

Bayan sun gama yace mata taje su hada kaya kallonsa tayi tace "qalbee wani kaya kuma , Ai mommy tace bazan koma ba😂😂"

Wani irin mugun kallo ya mata yace "yarinya idan muka koma za kiyi bayani kuwa"
Dariya tayi tace"Bari dai mommy ta dawo"

Bari tun yanxu na fara hukuntaki kafun mommy ta dawo din ,
Mikewa yayi zai kamota ,ta ruga da gudu haka suka ta zagaye falon suna jifa da pillows din kujeru , kaman wasu yara ,sunyi Kacha kacha da palour din ..........

Mommy ce ta dawo tun dazun take sallama Amma babu Wanda yaji ta  , iman kokari take ta rama jifan da ya mata ya mata ,shikuma Sai gudu yake ,

Ta taho da gudu wani irin jiri ya 'dibeta shuuuuuuuu😢

Ahmad maza yayi ya tallabeta ,ta suma , idan hankalin Ahmad da mommy yayi dubu ya tashi

Wani mugun kallo mommy tayi masa sanna  tace "Kai Sai ance maka ta dauke ta mu tafi hospital "

Rudewa yayi ya rasa Ina zaiga key din motarsa  , mommy ce ta mika masa nata tace su wuce ,

Daukan iman yayi ya sakata a motar ,sannan  ya tada duka tafi asibinti Murtala , nanne suke da Kati .

Suna zuwa direct office din wani abokinsa suka wuce aka karbesu hannu bibbiyu ,
Aka kwantar da ita a Gadon marasa lafiya , aka ce su Ahmad da mommy su fita .

Waya mommy ta daga ta kira daddy ta sanar da shi
Ahmad Sai zagaye yake duk hankalinsa ya tashi ,ya rasa me zaiyi gaba daya .
Ana cikin haka daddy yazo ,
Yake tambayar meya same iman dinn

Cikin fada da bacin rai mommy ta fara cewa"yarinya ba lafiya gareta ba ,wannan yaron yazo ya sata guje guje ,kilan gajiya tayi gashi kuma mara hankali yaki barinta ta huta ,sunyi mun kacha kacha da palour ,Sai kace auta 😏"

(Kai mommy Sai kace ba Matarsa ba 😂😂, yi hakuri kar kijini ki sauke haushin Ahmad a kaina 🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️)

Daddy kuwa da jin Haka Sai ta bashi dariya ,yasan kwanar zancen Sai yayi wufff tace"ke hajiyata Dan yayi guje guje da matarsa mene , kawai dai abu yazo da tautsayine Allah ya tsare dai ,Allah ya bata lafiya..."

Kafun mommy ta kuma cewa Komai Sai ga doctor ya futo.................................


     

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now