Chapter 50 Final

76 11 8
                                    

The end

Washe gari da safe yan biki suka fara watsewa har airport su Abdulrahim suka raka abokansu da sukazo daga California haka sauran bakin da suke daga gida Nigeria suma duk suka fara shirin watsewa, su matan sule ma ‘yan kaura da sukazo suka fara hada kayansu dan gobe talata zasu koma gida suma, wannan yasa gaba daya gidajen da akai bikin sai suka fara sararawa saura yan tsiraru, washe gari ‘yan kaura suka koma suma tare da sha tara ta arziki sai habu kawai da matarsa su aka bari sai kuma su goggo Zainaba suma a ranar wasu maza su biyu daya yayan inna ne dayan kuma shine babban dan goggo Zainaba sukazo da niyyar tafiya da yan uwansu bayan an zauna anyi Magana tsakaninsu dasu Abdulrahim.
A ranar aka zauna da niyyar rarrashin Abdulrahim sannan su nemi yafiyar yaran amma ga mamakinsu shi ya fara tararsu da wasa da dariya yana ta tsokanar inna delu wai amma dai ba da ita za’a komaba dan bata gama cin amarcintaba tukunna, anyi maganganu sosai su goggo Zainaba sun roki gafarar su Abdulrahim su kuma sun yafe musu a karshe ma suka roki dasu bar musu inna delu koda ba duka bane amma sunaso ta dan zauna dasu na wani lokaci koda zuwa lokain tariyar khadijane, ranar laraba suka koma gida da tarin sha tara ta arziki bayan sun bar inna delu akan cewar zasu dawo su dauketa idan sunzo tariyar khadija. Wasa wasa dai yanzu kowa ya gama watsewa saura Zainab kawai itama ranar Friday zata tafi dama Dr da matarsa tuni suka koma gida ita kawai suka bari.
Yanzu gidansu Abdulrahim na cikin asibiti ya koma na habu shi da matarsa suna sama khadija na dakinta baba yana nasa yaransu kuma suna dakin Bello, khadija ce ta dage sai dai su bar mata inna delu duk da da fari so sukayi su tafi da ita gidansu amma dole haka suka bar mata saboda duk abinda takeso shi zata samu ko menene kuwa indai bai sabawa addiniba. Takanas Abdulrahim da Abdulrahman suka tasa khadija a gaba sukace ta fadi duk abinda takeso a rayuwar duniya ko menene shi indai har kudi suna iya siyansa to zasu siya matashi koda kuwa sai sun tattara duk abinda suka mallaka kafinsu sama matashi, kayan daki sukeson siya mata amma sun rasa ma a ina zasu siya duk shagon da sukaje sai suga kamar tafi karfin gaba daya kayan shagon ji sukeyi tamkar su siya mata duniya gaba daya a karshe dai Abdulrahman yace kawai su bar Nigerian aje can wata kasa a siyo mata daidai ajinta sai da ta tubure musu akan ita fa na Nigeria dinnan dai shi takeso ai muma muna da wadanda suka kware akan harkar kayan dakin, sati biyunnan gaba daya a shirin gidanta suka kareshi danko zaman cin nasu angwancin basuyiba burin kanwarsu ta samu komai wanda takeso ta samu komai best tukunna. Ranar da zasuje siyayyar kayan kitchen kuwa atm din Abdulrahim kawai ya basu da password dinsa yace suyi ta siyan duk abinda sukeso har sai sun gaji ko sun tabbatar sun sai komai, ita da hajiya sukaje itata nuna mata komai dama duk shawarar da zasuyi ma itace abokiyar shawarar tasu haka aka sai komai daya kamata sannan sukazo sukayi mata jere itama cikin gidan sati biyu da gama bikin su Abdulrahim aka kai khadijatul kubra gidan Bello (Abdulmalik).
Wani irin zamane ake gudanarwa cike da soyayya da kulawa a gaba daya gidajen uku gidan Abdulmalik Abdulrahman da Abdulrahim kowannensu na matukar son matarsa kuma yana son matar dan uwansa dan ba matansu kawai suke kula dasuba har matan yan uwan tunda ma ai kannensune suma bayan sati da tarewar khadija gaba dayansu tare da Dady, momy, prof, hajiya, mama, malam, mal musa, adi da inna delu suka shirya suka shilla sai kasa mai tsarki dan gudanar da umrar azumi bayan sun gama umrar kuma suka cigaba da zama sai Dady da prof ne kawai suka dawo su kuma suka cigaba da ibadarsu har aka tafi hajji suka shige cikin mahajjata suka gudanar da aikin hajji, tunda suka zo kasa mai tsarki gaba suka tattara hankalinsu kacokam suka maidashi wajen ibada tare da addu’o’i na neman duniya da lahira baki daya haka mahaifiyarsu tasha addu’a itama tunda Allah bai bata ikon zuwa har zuwa yanzu taji dadinsuba to tasha addu’a.
Allah ya taimakesu daga Amira har Aisha hutu sukeyi na session shiyasa basu wani samu matsala ba akan dadewar da sukayi suna kammala aikin hajjinsu suka hado kayansu sai gida, bayan dawowarsune akazo daukan inna delu ita kuwa tace ina ai fa ita ta samu wajen zama su dai ‘yayan nata idan sunason ganinta sa dingayo kudin mota suna zuwa dama tunda suka kawo khadija ta dauketa ta koma gidanta, dole suka hakura suka koma gida sai dai waya wani lokacin kuma sai wani yazo ya ganta ko su su dauketa su kaita ta kwana biyu sannan su dawo, ba laifi yanzu idan su Abdulrahim sun hadu da Usman yana dan sakar musu fuska ba kamar da ba duk da har yau bai taba zuwa gidansuba yaya abubakar kuwa da Umar duk sunje aliyu kuwa ba sau dayaba ma yasha zuwa gidan kanwarsa gidan yayyensa, haka momy ma yanzu basu da wata matsala da ita yanzu ta ajiye duk wani abu da takeji akansu ta rungumesu sosai a matsayin ‘yayanta kuma surukanta kamar yadda Dady yaso tayi tuntuni, wata mata suka saka momyn ta samowa mal musa da kyar suka lallabashi yayi aure shima yana nan zaune a tsohon gidansu shi da matarsa haj hauwa kuma matar na da kirki sosai ba karamin kula takeyi dashiba haka suma idan sukaje gidan tamkar ita ta haifesu haka zatayi ta nan nan dasu.
Watanni biyar da bikinsu wata rana suna zaune a gidan Abdulrahman suna dinner dama haka sukeyi kullum a gidan mutum daya za’aci abincin dare kuma indai mutum na gari sai yazo Bello ne ma ya fiya dan tafiye tafiye saboda yanayin aikinsa shima kuma ranar yana gida duk suna zaune suna cin abinci sunyi shiru bakajin komai sai karar cokali da kuma ta ac, Amira ta danyi gyaran murya duk suka dago suka kalleta sai ta dan langabar da kai tana kallon Abdulrahman tace “yayana please I forgot I left a bun in the oven could you please take it out for me? Please” ta sake langabar da kai shi kuma da sauri ya mike yana cewa “sure” ita kuma ta kalli Aisha ta kalli khadija sai suka saka dariya, Abdulrahim ya kallesu ya ajiye cokalin hannunsa yace “me yake faruwa?” Aisha ta dan daga kafada tace “ba komai” yace “wallahi ban yaddaba ku gayamin menene” khadija tace “haba yaya Abdulrahim ka bari zakaji za kuma ka gani koma menene” Bello yace “idan tayi tsami maji idan kuma dariyar an maida mana dan uwa mijin tace an aikeshine kukeyi tom” Amira tace “dama ai mijin kan tace ne bama sai tace din ba” daga kicin suka jiyo Abdulrahim yace “Amira?” sai kuma gashi nan da sauri hannunsa rike da plate din oven da wani abu mai kama da doughnot ciki ya tsaya yana kallon Amira idonsa kamar zai fado kasa yace “Amira what do you mean? Menene wannan” ta daga kafada shi kuma ya maida idonsa kan Abdulrahim da shima yake kallonsa sai kuma ya sake kallon Amiran yace “wait wai ke…” Abdulrahim ya mike ya nufoshi yana cewa “wai menene?” ya leka plate din sai shima ya zaro ido ya kalli Amiran yace “you?” instead of ta bashi amsa sai ta sunkuyar da kai tana murmushi Bello kuma ya warce plate din yana cewa “wai dallah malamai menene haka ne me kuke kallo a jiki” shima dai irin reaction din su Abdulrahim din ya nuna sai kuma a tare suka kalli juna kawai sai kuma suka saka ihu suka rungume juna suna tsalle Abdulrahman murna yake sosai fadi yake “I’m going to be a father”  Bello ya dungure masa kai yake “dalla malam gyara we dai” Abdulrahman yace “yes we we na gyara” sai kuma ya sakesu ya koma wajen Amiran da sauri ya rungumeta yana ta faman dariya suma su khadija sai dariyar sukeyi, Bello ya dan dungurewa khadija kai playfully yace “daku aka shirya wannan abin amma shine ko ku gaya mana ko” ta dan dafe inda ya dungure mata cikin shagwaba tace “cewa fa tayi karmu gaya muku” Abdulrahman yace “amma tun yaushe kuka sani kukaki ku gaya mana?” khadija tace “jiyane fa ba wani dadewa” Abdulrahman ya kalli Amira yace “tun jiya kika sani amma kikaki gayamin?” tace “to ba gashinan bana gaya maka yanzu har yaya Bello na cewa wai na maidakai mijin tace ina aikenka” Abdulrahman yace “indai idan an aikenin note din am pregnant zan dinga gani ai a aikeni sau dubu” duk suka saka dariya cikin farin ciki.
Tun daga ranar gaba daya hankalinsu ya koma rainon cikin dake jikin Amira tamkar a kanta aka fara yin ciki kowa ya bude baki yace “baby” ko “maman baby” idan tace kuwa tana sha’awar abu to har sai ya hau mata kai dan kowa sai ya kawo, tun daga ranar kuma kullum aka koma cin abinci gidan Abdulrahman saboda wai karta wahala wajen zuwa sauran parts din.
Two years later
Abubuwa da yawa sun faru a lokacin kamar haihuwar Amira da namiji mai sunan Dady suna kiransa da Dady sannan Aisha ma ta haihu itama namiji shi kuma sunan cp aka saka masa shi kuma amir suke kiransa khadija kuwa mace ta samu tsakaninsu da Aisha kwana takwas ta haifi bilkisu (Amira) Dady shekararsa daya da wata uku su Amira kuwa suna watanni tara kenan, sannan kuma kusan shekaka guda kenan da a yanzu suka koma zuwa kauran namoda duk karshen wata duk weekenddin karsen wata wajen ginin da Abdulrahman ya taba bayarwa akayi masa na dan karamin asibiti irin na kauye suna charity work komai kuma kyauta da duba marar lafiyar da kuma maganin da za’a bashi kai hatta da kananan test da scanning na masu ciki da kananan yara duk kyauta sukeyi indai suna da kayan aikin a wajen, wannan abun ba karamin dadi yayiwa yan kauyenba suma kuma ba karamin dadin wannan aikin sukejiba dan sunsan koba komai dai Allah kadai yasan yawan ladan da suke samu koba komai suna taimakon mutanensu sannan duk zuwan da zasuyi sai sun tafi da wani likita na mata saboda masu ciki Amira kuma saboda yara duk da bata kammala karatunba amma dai tasan kan aikin, shi kuwa Abdulrahman yana zama general ne maza da mata wadanda ba matsalar ciki ko haihuwa ta kawosuba suma kansu su Abdulrahim ba’a barsu a bayaba dasu akeyin komai duk karshen watan duk da fanninsu bane amma basa rasa abinda zasuyi kullum, a makarantarsu kuwa sun baje wannan manyan zauren da ake karatu a ciki bayan sunyi normal kananan soraye da mutum zaibi ya shiga gidan malam ragowar filin kuwa sai suka gina katon daki guda daya wanda yanzu gaba daya almajiran a ciki suke suke kwana kuma suka bisu da tabarmin leda kanana da kuma barguna irin wanda ake kira da barkon masu gadi dinnan gaba dayansu, lokaci zuwa lokaci kuma suna raba musu kayan sakawa takalma da sauransu sannan a yanzu babu almajirin wannan makarantar da yake bara sai dai idan shi yaga dama amma badai dan yunwaba kayan abinci suke ajiyewa duk wata da kuma mai aiki da aikinta kawai yiwa almajiran girki ta raba musu su kuma kowa ya wanke kwanonsa.
Ayau kuma bayan shekaru biyu Aisha khadija da Amira suke bikin kammala karatunsu kowacce ta samu kwalin degree a fannin da take karanta Aisha environmental management and toxicology Amira kuma medicine pediatric ita kuma khadija tayi saukar alkur’ani mai girma Amira watan ta biyu da kammalawa haka khadija ma tuni ta hade amma sai suka jira Aisha shine yanzu suke walimar a tare, a harabar gidansu sukeyin walimar an hada biki gagarumi yan uwa da abokan arziki duk sunzo tayasu murna haka mazansu ma duk sunyo gayyar abokan arziki a lokacin kuma Abdulrahman ya dankawa Amira department of pediatric dake khadija specialist hospital gaba daya ita kuma Aisha company din da Abdulrahim ya taba maganar budewa shi ya danka mata ta fara kula dashi kafin lokacin da zaiyi ritaya daga wasan kwallo dan tuntuni ya kammala ginin wajen ya zuba kayan aiki ya dau ma’aikata tunda daman field dintane shi koyazo sai dai yazo matsayin dan tayin aiki.
Bayan sun kammala walima ne kuma washe gari suka fita domin rabon sadaka ga mabukata nakasassu da marasa lafiya, a kofar khadija specialist suke yin rabon kudine mai dan kauri da kayan abinci mutane da yawa sunzo gasunan abin tausayi wasu kamar zakayi musu kuka, Abdulrahim na bin bayan Aisha yana mika mata emvelop din da kudin yake ciki ita kuma tana dankawa mabukatan har sun dan wuce sai sukaji matar da suka bawa tace “Abdulrahim?” da sauri Abdulrahim ya juyo ya kalleta kwata kwata bai ganetaba ta dan matso a hankali tace “Abdul baka ganeniba ko? Bintuce” da sauri yace “bintu? Bintu dai dana sani? Menene ya faru me ya kawoki nan?” sai kawai ta saka kuka Abdulrahman dasu khadija suka matso Abdulrahman na cewa “Abdul kai dawa?” Abdulrahim yace “Abdul kalli bintu ce fa” Abdulrahman ya kare mata kallo yace “haba alhaji idonka ya fara samun matsalane? Wannan dince bintu yarinyar da akace tana lagos” matar tace “Abdulrahman wallahi nice na dawo tun tuni” ya kara kare mata kallo khadija tace “me ya sameki kika koma haka yaushe kika dawo?” kawai sai ta fara kuka tace “dije kiyi hakuri ki yafemin nayi kuskure wallahi ba laifina bane duk sharrin shaidanne da kuma zugar inna amma wallahi ba laifina bane, nasan hakkinki na daya daga cikin abubuwan da suka tarwatsa rayuwata taki yin haske ko kadan ni danaje neman kudi lagos sai na bige da zama karuwar karfi da yaji wasu mugayene suka kulleni a gidansu su biyar haka zasuzo suyi abinda sukaga dama dani wani lokacin ma harda duka zasu hadamin satin da naje lagos ban kuma ganin ranaba har sai ranar da sukaga bani da lafiya ina shirin mutuwar musu a gida shine fa suka daukoni suka dawo dani nan garin suka yar akan hanya daga baya aka gayamin ina dauke da cuta mai karya garkuwar jiki yanzu ko abinda zanci bani dashi balle abinda zan nemi magani dan Allah ki yafemin watakil zan samu sassauci” khadija ta goge hawayen fuskarta ta tafi da niyyar rungumeta dan ta rarrasheta irin kukan da takeyi amma sai Bello ya rikota ya jawota baya yace “what do you think you are doing?” tace “love yar uwatace fa” yace “na sani nasan ko wacece amma ina fatan ba rungumeta zakiyi a haka ba so kike ki dau wani ciwon?” tace “babu ciwon da zan dauka a jikin ta HIV ce da ita kuma ba’a daukanta kawai dan an taba juna” Bello yace “whatever badai zaki tabata ba ba yanzuba” Abdulrahman ya kalli bintu shima kamar zaiyi mata kuka saboda irin yadda ta mugun lalace sai hakora da kwala kwalan idanu yace “shikenan ya isa haka daina kukan haka maza yanzu zan hadaki da wani zai kaiki wajen baba yana ciki ki samu kici abinci kiyi wanka idan mun gama zan shigo sai asan yadda za’ayi kinji? Ki daina kuka haka” ta kada kai tana da kokarin goge hawaye shi kuma ya kirawo wani masinja yace ya rakata gidan baba sannan suka cigaba da abinda sukeyi.
Bai wuce mutum biyar suka sake wucewa ba aka kuma kiran sunan Abdulrahim ya kalli wadda ta kira sunan nasa yace “to ke kuma wacece? Jaru? Dan nasan tunda akaga bintu kuma ai sai jaru” matar itama gaba daya saura kashi a jikinta ta wani irin yin baki rabin fuskarta a kone yayi baki kirin sannan babu kafafu duk biyun akan wani katako take ta saka kuka itama tace “Allah sarki ashe kuwa zaka ganeni duk lalacewar da halittata tayi nice Abdulrahim nice babarku jaru dan Allah nima ku taimaka min” Abdulrahim ya tsaya ya kare mata kallo sai kuma yayi wata dariya yace “akan wanne dalili? Karki rainawa kanki hankali babarmu a ina can kije ki nemi ‘yayanki bamuba kuma ki tashi daga kofar gidannan wallahi ko ranki yayi mugun baci” ta kalli Abdulrahman dake kallonta tace “Abdulrahman nasan kai ba zaka gujeniba nasan kai zuciyarka irin ta mahaifiyarku ce na tabbatar zaka yafemin dan Allah ku yafemin kamar yadda kuka yafewa yar uwarku” Abdulrahman ya saki hannun Amira ya matsa kusa da jaru ya tsugunna a gabanta yana kare mata kallo yace “ayya ke kuma menene labarinki? Ina kafafunki me kuma ya samu fuskarki?” jin ta fara samun kansa ta dan sake matsowa tana zubar da hawaye tace “wallahi ranar dana bar zamfara da niyyar bin bayan bintu kano na fara shigowa sannan na hau mota da niyyar nufar lagos amma ko kura bamu bariba mukayi hatsari a wajen na rasa kafafuna na koma rasa rabin fuskata bayan nasha dakyar tun wancan lokacin nake yawo a kano ina bara a tasha ma nake kwana ko wajen zama bani dashi abinda zanci kuma sai na barato ina cikin almajiran dake yawo a danja suna bara cikin rana ruwa ko sanyi dan idan ma ban fitoba babu wanda zai bani abinda zanci dan Allah dan Annabi nasan idan har mahaifiyarku tana raye zata yafemin dan haka nake rokonku tare da fatan zaku yafemin kuma dan Allah ku yafemin ku kaini wajen mal musa shima na nemi yafiyarsa ko na dan samu sassauci” Abdulrahim ya dan karkada kai yace “subhanallahi Allah ya kiyaye gaskiya kinsha wahala amma kinsan wani abu? Ita bintu da kikaga nace a shiga da ita ciki keda bakinki kin fada ‘yar uwarmuce kanwatace dan haka zan iya taimaka mata a kowanne lokaci sannan kuma bata kashemin mahaifiya ta kuma rabani da mahaifina ba dan haka zan iya yafe mata a koyaushe ke kuma fa? Da kike cewa kinsan inna zata yafe miki ai ita daban mu daban zuciyar ba iri daya bace kuma itama baki kashe mata uwa kin rabata da uba ba shiyasa kike tunanin zata yafe miki bara kuma shekarunmu goma kikasamu bara anan kan titin nan kan danjar da kikeyi yanzu dan haka munsan exactly abinda kikeji gara ma ke kekika jawa kanki dan haka ki tattara sauran cinyoyinki kibar wajennan idan ba so kike nayi miki abinda suma zaki rasasu kamar yadda kika rasa kafafunba” ya dago daga tsugunnun da yayi ya kalli wani security yace “kai garba kalli wannan matar idan da hali ma ka dauki hotonta ka nunawa gaba daya sauran securities din asibitinnan wallahi wallahi wallahi idan har ta kuma shigowa cikin asibitinnan a bakacin aikin duk wanda yake on duty ke kuma” ya juyo ya nuna jaru yace “idan kika sake muka sake hada ido dake ko anan asibitin ko a gidanmu ke ko a kaurane kika kuskura na kuma ganinki wallahi sai kin rasa wani abin a jikinki bayan kafafu da fuska kinji na gaya miki” yana kaiwa nan ya juya yayi ciki ko sadakar ma bai tsaya a karasa ba da sauri Amira tabi bayansa su Bello ma binsa sukayi shi kuwa Abdulrahim tsayawa yayi yana kallon jaru yadda take kuka da idonta yace “shi dama sharri dan aikene duk daran dadewa sai ya dawo ga wanda ya aikeshi, kinga abinda Abdulrahman ma yayi miki shi da kike cewa yana da zuciya irin ta inna ni kuma me kike tsammanin zanyi miki? Tunda ya gama yanke hukunci bari na kyaleki amma ki sani idan shi yace zai cire miki wani abu idan ya kuma ganinki to ki saka a ranki ni ranki zan tabbatar ya bar jikinki idan na kuma ganinki, zan kasheki saboda kin kashe min mahaifiya a addinance kenan a duniyance kuma ina da kudi kudin da zan iya gujewa hukuma so na kashe banza wallahi dan haka kiyi ta kanki” shima ya kama hannun tasa matar ya juya ya bar mata wajen.
Sun manta duk abinda ya faru tsakaninsu da bintu sun taimaketa dama ga dan uwanta nan cikin gidan ga kuma mal musa da matarsa dan haka itama aka bata daki cikin gidan sannan suka sakata ta fara karbar magani tare da kula da dukkan abinda ake bukatar taci ko wani exercise da ake bukatar tayi kafin wani lokaci kuwa tayi bulbul da ita ta murje wani lokacin ma har gidan khadija take zuwa ta dan yi weekend ta tayata da aiyukan gida duk da tana da mai aiki amma haka take zuwa tayi tayi mata ‘yan aikace aikace duk da ita khadijan bata jin dadin hakan. Bayan komai ya natsa sun yaye yaransu sai suka barwa bintun a gida tunda ga adi ga kuma matar baba suka dau hanya wai sun tafi honeymoon din da basujeba karatu ya tsayar dasu daga nan kuma sai ciki amma yanzu tun kafin wani cikin yazo gwara suyi sauri suje.
Saudia suka fara tafiya sukayi umra tare da jaddada godiyarsu ga Allah a yanzu dai basu da wata matsala suna kuma fatan Allah ya kade musu duk wata matsala da zata iya taso musu nan gaba, sunyi karatu iya karatu sun samu aikinyi aiki mai kyau ga abokan rayuwa na gari masu sonsu ga ‘ya’ya kyawawa sai dai fatan su zama masu albarka basu da wani makiyi a yanzu sai dai wanda ba’a rasaba dan rayuwa bata yiyuwa sai da makiya, momy ta koma tamkar zata goyasu don so dama can Usman ne yake zugata yanzu kuwa ta daina daukar zugar tasa shi kuma Usman har yanzu bai gama sakin jiki dasuba duk da dai idan sunje gidan Dady sun tarar dashi suna dan taba hira amma ba kamar Umar da Aliyuba, Umar yayi aure ya auri wata tsohuwar budurwarsa khadija taso ya auri Zainab kamar yadda da ya nuna yana sonta amma Allah baiyiba dan tuni ma Zainab din tayi aurenta har da babynta ‘yar watanni biyu, Usman ma ya fara shirin aure amma dai da saura dan ya tsaya shima ruwan ido, dadin da Dady yakeji ta hannun su Abdulrahman kuwa ko mahaifinsu mal musa bayajin ko rabinsa komai burinsu suyi masa ko yaya ya dan motsa zakaga sun rufeshi da tambayar abinda yake bukata shiyasa kullum yake cewa “da na kowane bakasan wanda zaiji kankaba” kamar yadda ya saba, khadija ta zama cikakkiyar ‘yar business woman amma daga gida dealer ce ta kaya kala kala dan haka ita aikinta kawai waya tace a kaiwa wane a kaiwa wane tana da yara da suke mata hakan ita dai tana daga gida Aisha ma daga gida take gudanar da harkar company din mijinta  a sati bai wuce taje sau daya ba shima sai bukatar hakan ta taso Amirace kawai take aikin fita shima tare suke fita ita da mijinta su kuma dawo tare indai ba a wani asibitin zaiyi aikiba ita kuwa ya hanata karbar aikin kowanne asibiti idan ba nasuba yace yasan stress din baya mata fatansa.
Ranar da suka kammala umra su Abdulrahman sun taho daga masallaci zasu taho gida Abdulrahim yace “wai har yanzu bamu yanke inda muka nufaba daga nan” Abdulrahman yace “cewa akayi zamuje kasashe uku su Amira ne kuma zasu zaba” Abdulmalik yace “nidai na zabarwa khadija Nevada California” Abdulrahim yace “bamu yaddaba ka batta ta zaba da kanta ba wani nevada” Bello yace “alkawari fa nayi mata” Abdulrahim yace “sai ka bari daga baya sai ka kaita koma inane amma mu dai yanzu ba zaka kaimu wani nevada ba ehe” Bello yace “ai kuwa sai dai a raba tafiyar haka kawai ku matanku zasu zabi inda sukeso ni tawa ace ba zata zaba ba” Abdulrahman yace “ shikenan munji neveda it is” suna zuwa gida kuwa aka zauna shawara khadija tace “yaya Bello nidai inda ka taba cewa zaka kaini dinnan lokacin da bani da lafiya can nakeson zuwa” ya kalli Abdulrahim yayi masa gwalo shi kuma ya dauke kai kawai, Abdulrahman ya kalli Amira yace “kefa” ta dan mirgina kai tace “inda muka taba zuwa da graduation dinka” Abdulrahman yace “can dai khadija ta zaba” Amira ta kuma mirgina kai tace “ok shikenan na canja korea” Abdulrahman ya kalli Aisha yace “Aisha saura ke” Aisha ta danyi murmushi tace “india inaso na kaiku wajen yan uwana na can na nuna muku kasarmu” Bello yace “kasarsu dai ke yar Nigeriace” Abdulrahim yace “ina ruwanka idanma chad tace kasarsu?” khadija tace “wannan dai da anty Zainab kake”.
Haka suka shirya daga Saudi Arabia sai Korea, satinsu Abdulrahim biyu a Korea babu inda basujeba a wuraren tarihi na korea sune jeju island, gwanghwamun gate, seoul tower, hallyeo maritime park, bukchon hanok village and many more. Sunyi yawo iya kacin yawo Amira jinta takeyi tamkar a cloud 9 dan jin dadi yaudai gata a kasar masoyanta taso haduwa da wasu daga cikin celebrities dinsuma amma hakan bata samuba, daga korea kuma sai india gidan uncle ahmad suka fara zuwa dake new delhi da suka ce ma a hotel zasu sauka fada yayi tayi yace ga gidansa nan kuma hotel din me zasuje? Shima anan sunsha yawo sosai sune tajmahal, red fort a birnin new delhi, gateway of india a Mumbai, mecca masjid na hydrabad sune har amer fort na birnin jaipur india ma sati biyu sukayi daganan sai Nevada new port, ananma sunsha yawo daga wannan waje su tafi wannan sune har Utah da oregun makotan jahohin Nevadan sunji dadinsu sosai sunyi bulbul dasu.
Wata rana Bello ya fito waje kan yashin beach yana zaune yana shan iskar wajen yana kuma kallon mutanen dake surf a cikin ocean din kawai tunanin rayuwa yakeyi wanene ya taba hasaso wai su almajirai sune zasu zama haka? Su kansu basu taba kawo ko abuja zasu taba zuwa a rayuwarsuba balle USA kuma wai su din yan garine acan din, yana zaune yaji kamar ana kallonsa ya juyo side din suka hada ido da khadija tana tahowa daga wajen guest inn din da suka sauka ya sakar mata murmushi itama ta maida masa tana karasowa ya dan bubbuga tsakanin kafafunsa alamar tazo ta zauna ita kuma sai ta waiga side din data taho ta tabbatar su Abdulrahim basu biyotaba ta kuma kalli wajen da mutane ba laifi sai dai kowa harkarsa yake Bello yayi dariya yace “yar kauye babu ruwan kowa dake a wajennan ko kallonki babu maiyi come on wani labari zan baki” sai kuma ta dan sake yin murmushi ta karaso inda ya nuna mata ta zauna ta jingina bayanta a kirjinsa suna pacing ocean din gabansu yace “kinsan tunanin da nakeyi?” tace “sai ka fada” yace “rayuwa! Tunanin rayuwa nakeyi sweetie irin wahalhalun da mukasha a rayuwarmu cikin mu shidan nan zan iya cewa Aisha ce kawai tayi rayuwar dadi tun daga farko kowanne ciki yasha wahala babu wanda acikinmu yayi tsammanin zai zama abinda ya zama yanzu amma cikin ikon Allah kalli matsayin da muke dashi yanzu kalli a inda muke dan haka babu abinda azamu cewa ubangiji sai godiya ya bamu komai ya bamu kudi abokan rayuwa na gari iyaye uwa uba kuma lafiya sai dai godiya da fatan ya cigaba da bamu zuri’a kyawawa masu albarka” khadija ta kuma kwanciya a jikin bello tana tuna irin rayuwar da tayi bata taba tsammnin wai zata kai ranar da zataci abinci ta koshiba balle wai har ta zabi abinda zataci amma yanzu sai dai ta taimaki wasu da abin dake aljihunta ita kadaima ba sai ta nemi taimakon ‘yan uwanta ko mijintaba ada kullum tunani takeyi zata auri wani manomi wanda zai dinga tasata a gaba suna zuwa gona suyi noma sannan idan an girbe anfanin gonar tayi sussuka tayi sirfe tai daka kafinta sama musu abinda zasuci shi kuma watakil ya dinga zuwa birni ci rani idan damuna ta wuce irin wannan fatan tayi tayiwa kanta dan burinta kawai shine tabar gaban su jaru itama ta samu yancinta amma shi ubangiji da ya tashi bata abinda ya tanadar mata sai ya bata miji wanda ko girkinma idan taso ba zatayiba ya kuma dawo mata da yayye wadanda cin abincin ma idan taso sai dai a bata a baki dan haka kullum take cikin godiyar ubangiji akan ni’imarsa gareta ita da yan uwanta da mijinta.
Sun dade a haka suna kallon waves na ocean kafin su Abdulrahman suka fito kowa da matarsa a gefensa Khadija na daga kai ta hangosu ta mike tafi opposite side din da suka taho da sauri har tuntube takeyi Bello ya saki baki yana kallonta sai kuma ya juya ya kalli Abdulrahim dake gaba yace “dallah malam me ya fito da kai yanzu kawai ina enjoying rayuwata ni da matata kazo ka korarmin ita” Abdulrahim ya tsaya a kansa yace “tunda na fito nayi muku magana balle kace na koreta” Bello yace “to ai kunyarka taji” Abdulrahim yace “wannan kuma ku kuka sani” sannan ya juya yayi bakin ocean din yadda ruwa zai dinga tabashi shi kuma bello ya mike a hankali yana zuwa bayansa ba tare da sanin Abdulrahim dinba ya dane bayansa suka fada cikin ruwan, da sauri Abdulrahim ya mike yana goge fuskarsa ya kalli Bello fuska a hade cikin masifa yace “menene haka dallah malam” Bello yayi masa gwalo yace “hukuncinka kenan na kunyata min mata” sannan yayi cikin rowan da gudu shi kuma Abdulrahim ya bishi suka kama yar watse watsen ruwa. Abdulrahman ya zauna kusa da Amira da Aisha da suke zaune yana cewa “Allah ya shiryeku bansan sanda zaku girmaba” Amira tace “sai su Dady sun fara raba su tukunna” Khadija ma ta gama bulayinta sai kuma gata ta dawo ta zauna gefen Aisha sunayi musu dariya, su Abdulrahim kuwa sai da suka gama kaca kaca da jikinsu sai kuma Bello yace “kai tsaya kaji wata shawara” ya matso yayi wa Abdulrahim din rada a kunne duk suka kallo Abdulrahman a tare sai kuma suka  danno da gudu yana ganin haka ya mike yana cewa “wallahi duk wanda ya shafamin ruwa ransa zai baci” Abdulrahim yace “au shafawa kawai?” baiyi auneba sai ji yayi sunyi masa cali cali sai cikin rowan sukayi sa’a kuwa wata wave ta kawo kawai suka jefashi a ciki yana dagowa wannan zai kuma dunbulashi idan ya sake dagowa wannan ya maidashi sai da sukaga yana neman shidewa sannan suka kyaleshi suna masa dariya yana dagowa ya daki rowan da hannunsa yace “aish” suma suka daki ruwan suka maimaita “ash” sai kuma aka kamayar watse watsen ruwa suna dariya suma su khadija suna gefe suna faman yi musu dariya.
*_THE END*_ .

....................
Hi angel
Happy new year 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Allah ya yafe mana kurakuren da muka aikata a wannan shekarar ya kuma hadamu da alkahirin dake wadda ta kama ubangiji kar ya maimaita mana wata shekara irin 2020 har gaba da abada ameen.

So finally almajiri ma da ne yazo karshe an gama may just maybe zanyi epilogue amma ba tabbas.
So ya kukaji? Ina fatan almajiri ma da ne yayi muku dadi kun nishadantu kun kuma karu ina fatan da yawa daga wadanda suka karanta almajiri ma da ne zasu canja yadda suke kallon almajirai zasu kara kaimi wajen taimakon almajirai za kuma su dinga jansu a jiki koyayane, ina fatan idan kunga kowanne yaro ko a hanyane ba lallai sai almajiri ba zaku ji cewa shima 'dane kuma 'da na kowane kamar yadda dady ya fada.

Na sadaukar da littafin *almajiri ma da ne* ga dukkanin wasu almajirai na duniya ina mai addu' ar Allah ya tallafi rayuwarsu ya saka haske cikinta.

Na gode sosai da hakuri da kukayi dani na tsahon watanni duk da kailulata kuka cigaba da bina bakuyi fushiba duk da lacking da nake a fannin rubutu dan wani lokacin ni kaina ina rasa wai ina na dosa amma still kukayi hakuri kuke biye dani na gode sosai Allah ya biyaku da mafificin alkahirinsa ya kareku daga sharrin social media.

Bye zanyi missing dinku zanyi missing fitsarar Abdulrahim zanyi missing surutun Amira da Khadija zanyi missing damben Bello da Abdulrahim zanyi missing gaba dayan characters na almajiri ma dane.
Allah ya hadamu cikin alkhairinsa ameen.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Where stories live. Discover now