Chapter 23

63 8 0
                                    

Shirye shirye sosai ya kankama na tafiyar su Abdulrahim lokaci kawai suke jira, motar da FG ta bawa Abdulrahim suka siyar sukaje suka bude account sannan aka yi musu visa da passport komai dai ya kankama sai jiran lokaci, sanda hutun su Amira ya kare da kyar ta yadda ta koma makaranta shima sai da akayi mata alkawarin idan zasu tafi za’azo har makaranta a dauketa ta rakasu har airport ko kuma suzo har makarantar suyi mata sallama amma duk da haka sai da tasha kuka kafin ta koma.

Ana e gobe zasu tashi sukaje makarantarsu Amira da kyar suka samu aka yadda aka basu ita aka kuma jaddada musu cewar gobe su tabbatar sun dawo da ita, tunda suka taho take zumbure zumbure ita sai sunyi mata alkawarin zasu dinga zuwa duk shekara, babu irin lallashin da basuyi mataba amma taki yadda dole sukace shikenan zasu dinga zuwa duk karshen session abinda sunsan suma kawai sun fadane dan su kwantar mata da hankali amma hakan ba yiyuwa zaiyiba.

Washe gari jirgin karfe biyu zasu hau anan airport din mal aminu kano international airport dake kanon dabo, tun safe da suka tashi sukayi wanka suka shirya dama kowa ya shirya trolley dinsa guda daya da suka zuba kayansu sai backpack itama kowa daya da ta danganci takardu da dan abinda ba za’a rasaba, sauran kayansu sun rabarwa almajirai yan uwansu, wadanda sukeso kuma sun kai ajiya gidan dady, dakin da suke haya sun saka wasu almajirai yan makarantarsu su cinye sauran kudin shekarar da suka biya idan yaso idan shekarar tayi zasu ci gaba da zama sai su biya idan ba zasu cigaba da zamaba sai su tashi su bawa mai gida wajensa, kayan cikin shagonsuma sun sayar dashi tas wanda yayi saura sai sukayi da wani mai shagon suka sayar masa da komai sai suka hada kudin sukayi sayayyar da sukayi.

A gidan dady sukayi break yau da yake tafiya zasuyi momy ta dan sakar musu fuska ba kamar daba, Amira na makale jikin yayanta ko motsi batason yayi ji take kamar idan ya tafi bazai dawoba shi kuma ya biye mata sai lallabata yake yana rarrashinta, dady ma ranar bai fitaba dan yanason raka ‘yayan nasa airport har sai yaga tashinsu.

12:30pm suka fita a motocin dady da yake yanzu motocinsa biyu da wadda yake amfani da ita da kuma ta gida, kusan kaf gidan babu wanda baije rakiyarba sai Usman wanda da ya fitoma yaga suna cin abinci hakura yayi da cin abincin yayi ficewarsa ko sallama bai tsaya sunyiba. Sai kuma yaya Abubakar da bayanan sun tafi excusion da makarantar da yake aiki amma har momy sai da ta rakasu har airport din.

Tunda suka shiga Amira ke kuka, da fari kukan hawaye kawai takeyi sai da taji an fara kiran yan jirginsu sannan ta kuma bare baki take ta famanyi, ta kankame Abdulrahman kamar zata shige cikinsa su tafi tare, tun suna mata dariya har suka ga dai abin nata da gaskene suka fara aikin rarrashi, sai gasu Abdulrahim anyi zaman dirshan ana rarrashin Amira tare da alkawarirrika kala kala.

Momyce ta gaji gashi har suna neman makara taje ta fara janta tana masifa “dallah malama sakesu ke da bakisan zuruba sai zuru zuru wuce mu tafi” da sauri Abdulrahim ya rike dayan hannun Amiran yacewa momy “momy please ki bari mu gama sallama sanda za’a rabamu da khadija ba’a barmu munyi sallamaba ki barmu muyi da Amira please” momy tace “Abdul sallamar takuce ba karewa zatayiba kunason ku makarane? Tun dazu ake kiranku amma kunanan kunsan halinta” dady yace “ki barsu suyi sallama shekaru bakwai ba wasa bane” dole ta kyaleta a karshe dai da kyar ta sakesu suka tafi sunayi suna waigen juna har suka shige departure hall.

Bayan kammala screening da komai jami'in gwamnati da yazo rakiyarsu ya gama musu komai sukayi sallama sannan suka shiga waiting area suka tarar har fasinjojin ma sun kusa kammala boarding sai kawai suma suka hau layi, a jirgi dai kam an kusa yin abin kunya danma dai Allah yasa kujerunsu gaba daya a jere suke da juna Abdulrahman na jikin window sai Abdulrahim sai Bello a bakin hanya ai kuwa Abdulrahman ya kankame hannun Abdulrahim su kuma suka dinga yi masa dariya sai da aka fara tashi sai shima kuma Bello ya kankameshi suka sakashi a tsakiya kamar zasu yaga.

Abdulrahim shima a tsorace yake amma kuma da yake yafisu dakiyar zuciya sai baiyi komaiba ya shanye tsoron nasa ya rike hannayensu yana kokarin comforting dinsu sai da suka daidaita a sama sannan suka sakeshi ai kuwa ya fara tilliga musu dariya kamar shima baiji tsoronba, Abdulrahim ya leka window yana cewa Abdulrahman “wow Abdul kalli window ka gani” yana juyawa yayi saurin rufe ido ya dauke kai “dallacan menene abin wow anan abin tsoro bazan iya kallaba” Abdulrahim yace “shikenan dawo nan ni na koma nan dan kallo zanyi” tun suna hira suna kalle kalle da dan kauyencinsu har suka gaji sukayi bacci.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora