Chapter 07

55 10 0
                                        

Mutumin na tafe Abdul na binsa har suka zagaya bayan shagunan, wajen da alama shagunan da Yan kasuwar ke ajiyar kayan sune, babu mutane sosai wadanda ke wajenma harkarsu suke dan haka ba wanda ya kula da su Abdulrahman.

Bayan wani shago suka sake bi wajen babu kowa sai shagunan langa langa, zuwa yanzu Abdulrahman ya fara jin tsoro sai zare ido yakeyi, idan yayi tunanin komawa sai wata zuciyar yace masa "N100 fa kullum idan ka yadda nan da nan zaka Tara kudin da yafi wancan ma" dan haka sai ya cigaba dabin mutumin, wani shago suka shiga da alama shima store ne kamar yadda sauran sukayi kama da store din sai dai wannan daga can karshe da kaga har da wata 'yar molalliyar katifa da bagco daga dukkan alama akwai wanda ke zaune a wajen, suna shiga mutumin ya juyo yana kallon Abdul da wannan rubabben murmushin nasa yace "yauwa kaga nan shine wajena idan ka dawo gobe nan zakazo ka sameni kaji?" Da Saudi Abdul yace "eh to yanzu wanne aiki zanyi?" Dan shafe kai mutumin yayi yana sake leka wajen kamar mai tabbatar da babu Wanda ya biyosu sannan yace "ka ganene ina sonka da alkhaine kaima zakaji dadi nima haka sannan ga kudin da zan dinga baka kullum idan aikin ya karbeka har manyan mutane zan hadaka dasu yadda zaka dinga samun kudi sosai dama gaka kyakykyawa da kai dan haka karka wani samu damuwa ko kaji tsoro kaji ko?" Cikin rashin fahimta Abdul yace "yanzu dai menene aikin" dan kallonsa yayi sannan yace "ina zuwa" wajen ya leka ya kara tabbatar da babu kowa sannan ya dawo yace "kasan yanzu yadda za'ayi?wandonka zaka cire sai na muna maka abinda zakayi" da mamaki Abdul ke kallonsa shi dai a saninsa babu kyau mutum ya cire wandonsa indai ba a bandaki yake shi kadaiba dan innarsu tana gaya musu kar su yadda su cire wandonsu a ko ina indai ba su kadai bane saboda Allah yana kona mai yawo ba wando, dan haka ya fara jin tsoro yana ja da baya yace "wandona kuma? Me zakayi da wandona?" Mutumin yana wani sidar bushashshe kuma fashashshen lebensa yace "ba wani abune mai wahalaba babu abinda zakayi ni zanyi komai kai dai kawai ka cire wandonka" idon Abdul ya fara kawo ruwa yace "innarmu ta hanamu tace kar mu cirewa kowa wandonmu babu kyau Allah yana kona masu yawo ba wando" a dan fusace mutumin yace "to idan ka cire cinyeka zanyi? Ina innar taka take anan? Na gaya maka zan baka kudi da yawa da abinci da takalmin karka gayawa kowa babu ma wanda zai san ka cire din" a matukar tsorace Abdulrahman ya fara neman hangar gudu yana cewa "nidai banaso inna ta hanamu banason kudin" amma kafin yakai bakin kofar mutumin ya kamoshi ya shakeshi tare da cewa "kana tsammanin zan barka ka gudune bayan na saka rai? To wallahi baka isaba ko ta karfine sai nayi abinda nayi niyya" shidai Abdulrahman ko fahimtarsa bayayi saboda fitar dashi daga hayyacinsa da shakar ta farayi, suna cikin kokawar ne har mutumin yayi nasarar kunce masa dan yamutsatstsen wandonsa sai jin daukar katako yayi a tsakiyar kansa, nan da nan ya saki Abdul ya rike kansa da  hannayensa saboda ba karamin shigarsa dukan yayiba yana dagowa yayi ido biyu da wani yaro sak wancan yaron da yake shirin lalatawa rayuwa, take kansa ya bashi wannan ne kanin nasa da yace kamarsu daya, da zafin zuciyarsa yayi kan yaron tare da yi masa shakar da tafi wadda ya yiwa wancan wanda har sai da ya saki katakon hannunsa yana neman kwatar kansa sannan ya dagashi sama sai da kafarsa ta rabu da kasa, wutsil wutsil Abdulrahim ya farayi cikin haka wata dabara ta fado masa take ya tattara dukkanin karfin da Allah ya hore masa a gwiwarsa sannan ya sankamar masa babban sashe🙉🙉, ai kuwa karfin dukan yasa mutumin yin mutuwar wucin gadi, dif aka dauke masa wuta a kwakwalwarsa, kafin ya dawo hayyacinsa Abdulrahim ya hankadeshi sannan ya kamo hannun Abdulrahman wanda har yanzu yake sunkuye yana kokarin daidaita numfashinsa sukayi wajen da irin gudun da ake kira gudun ceton rai.
Basu tsayaba sai da suka fito bakin titi sannan suka samu kan wani dan dakali suka zauna suna maida numfashi, kuka Abdulrahman ya saka irin me shake numfashi dinnan jikinsa har karkarwa yakeyi ya kifa kansa akan kafarsa tare da rungume kafafun nasa, Abdulrahim ya rungumeshi saboda karkarwar da yaga jikinsa nayi sannan yana dan dukan bayansa a hankali alamar lallashi, a haka bello yazo ya tarar dasu, cikin tashin hankali shima ya tsugunna a gaban Abdulrahman yana lallashinsa tare da tambayar abdulrahim abinda ya faru.

Basu samu damar yi masa bayaniba sai da Abdulrahman ya tsagaita da kukan da yakeyi sannan suka bashi labari, bello ma yaji tsoro sosai duk da basu San takamaimai me mutumin yayi niyyar yi musuba amma dai sunsan cutar dasu yayi niyyar yi dan haka suka yanke shawarar ba zasu kuma bin wani wani wajeba idan ance suzo su karbi sadaka komai kuwa yunwar da suke ji.

Da farko Abdulrahim yaso sukai kara wajen malam amma sai suka hanashi sukace idan sun gayawa malam ma fada za'ayi musu yace me yasa suka yadda sukabi mutumin ko kuma ma yace babu abinda za'ayi musu me yasa basu tsayaba? Tunda basu da tabbas din cutar dasu din za'ayi, wannan yasa sukayi alkawarin babu wanda zasu gayawa kamar yadda babu abun da zasuyi.

Haka rayuwar ta cigabar musu da takalmi daya ganin abun bana kare bane Abdulrahman yayi wani tunani dan haka da aka tashi daga karatu sai ya tafi wani shago anan kusa da makarantarsu yacewa mai shagon dan Allah ya bashi kwali idan yana dashi mai shagon ya dauko empty kwali ya bashi yace "N10 kenan" da mamaki Abdulrahman yace "dama sayarda kwalin kukeyi?" Ba magana kawai mai shagon ya miko hannu ya kwace kwalinsa ya jefa zaman kayan da ya dauko shi,  hadiye wani Abdul yayi da ya tsaya masa a makogaro sannan yace "ka bani kwalin zan baka idan naje bara na samo kudin" mai shagon yace "kaga malam idan baka da ita ka bani waje" cikin tashin hankali Abdulrahman yace "kaga dan Allah bani da takalmin da zanje dashine idan ka bani nayi bara zanje wallahi zan kawo maka kudinka idan na samo" kallon banza mai shagon yayi masa yace "dan ma ka raina min hankali da kwalin zakayi takalmin?" Abdulrahman yace "kai dai ka bani nasan yadda zanyi" ci gaba da harkarsa mai shagon yayi yana cewa "baka da hankali"

......................

Karku manta da comments da vote

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Stories to obsess over. Discover now