Chapter 15

64 10 0
                                        

BAYAN SHEKARU BIYAR

Wannan rana tayi dai dai da cikar su Abdulrahman shekaru tara da zuwa kano shekaru biyar a secondary school shekaru goma sha tara a duniya,
Ayaune makarantar rumfa collage dake sabuwar kofa ta kano ke bikin yaye dalibanta da suka kammala karatunsu wannan shekarar wata guda kenan da ya wuce suna jiran sakamako, dama makarantar ta saba duk shekara tana gudanar da irin wannan taron na bikin yaye wadanda suka kammala makarantar sannan kuma ta bawa sauran dalibai da suka cancanta kyaututtuka.

Makarantar tasha decorations sosai ga stage da podium akai ga wajen zaman manyan baki da wajen zaman iyaye ga wajen zaman dalibai da sauran al'umma, kowa yasha kwalliya kamar babu gobe daga malaman har iyayen kowa ka kalla fes dashi sannan fuskar kowa da murmushi mai nuni da farin cikin da kowa keyi da wannan rana.
Abdulrahman, Abdulrahim da Bello suma suna cikin daliban da suka ci kwalliya da kwani yadi fari mai kyau wanda dady ya dinka musu cikin kyaututtukan da yayi musu na candy, suna daga gaba gaba sai yashe baki sukeyi cikin tsananin farin ciki ko babu komai sun taka daya daga cikin steps din da suke ganin zai kaisu ga zuwa su dauko 'yar uwasu don komai sukeyi don khadija sukeyi.

Manyan malamai sun gudananr da bayanai da jawabai sosai akan amfanin ilimi da kuma illar rashinsa, sun fadi irin wahalar da da yawansu suka sha kafin suka kai inda suke sannan suka bawa daliban da zasu fita da sauran dalibai shawarwari akan karatu sannan da jaddada musu cewa no matter what kar suyi giving up akan karatunsu, dan sun sha wahala karsuce sun fasa saboda shi dama karatu abinda ya gada kenan idan ka fadi to ka tashi ka karkade jikinka ka cigaba da tafiya komai yawan kayoyi da kwazazzaban dake hanyar domin a karshe akwai lambu mai cike da 'yayan itatuwan ilimi masu tsananin zaki da dadi.

A haka har akazo gabar da za'a rabawa yara kyaututtuka, daga js 1 aka fara kowanne aji aka bawa na daya zuwa na uku a haka har zuwa ss3, dalibin shekara aka fara kira Mal Shehu wanda shine vice principal shine da loudspeaker a hannunsa ya fara kamar haka "a yanzu kuma zamu gangaro zuwa dalibinmu na shekara kamar yadda muka saba kowacce shekara, Ladies and gentlemen a big round of applause to our student of the year in person of Abdulrahman Isa kaura from ss3A" gaba daya wajen aka dau tafi kamar za'a tsaga makarantar gaba daya, a hankali Abdulrahman ya tashi daga wajen da yake zaune cikin yan uwansa ya yana tafe har hardewa yakeyi kamar zai fadi saboda yadda kowa na wajen ya zubo masa ido cike da alfahari.

Kowa na wajen ji yakeyi inama dai wannan dan sane daliban kuma na jin inama sune a matsayin Abdulrahman din, a hankali ya taka har kan stage din sannan Mal shehu ya cigaba bayan tafin ya lafa "yanzu zan gayyato commissioner of education alhaji Mansur Mahmud kuma former principle na wannan makaranta mai albarka domin ya mikawa dalibinmu kyautarsa yallabai bismillah" dady dake zaune kan kujera daya cikin kujerun dake layin gaba a mazaunin manyan baki, cikin murna da alfahari dady ya tako har zuwa inda Abdulrahman da Mal shehu suke yana zuwa yaja Abdul jikinsa ya rungumeshi sannan ya karbi kyautar daga hannun Mal wadda wani dan frame ne na katako da rubutu a jiki kamar haka: Award of Excellency To The Student Of The Year Abdulrahman Isah Kaura For being the most talented student this school has ever had. Bayan ya raba Abdul din da jikinsa ya mika masa aka daukesu hoto sannan ya kuma rungumeshi tare da fadin "am so proud of you Abdulrahman am really proud of you" mic din hannun uncle ya karba bayan yayi sallama ya fara kamar haka "a gaskiya yau ina cikin matukar farin ciki sosai ma kuwa saboda wannan yaron da kuke gani tamkar d'a yake a wajena ko kuma nace wannan yaro da kuke gani danane, amma da fari bari na fada muku wani abu game da wannan yaron da kuke gani; akan Abdulrahman na tabbatar da cewar genius exist, Abdulrahman baiyi nursery ba kamar da yawa daga yaran dake zaune a wannnan wajen sannan baiyi pri 1,2 and 6 ba bai kuma yi js1 ba ya shiga makarantane a lokacin da yake da shekaru goma sha daya a wannan shekarun js 1 ya kamata ya tafi amma kunsan inda ya shiga? Pri 3 cikin yara yan kanana amma hakan baiyi discouraging insaba, jumping din da aka dingayi masa baisa ya koma baya a karatun nasaba sai gaba da ya dingayi yanzu gashi ya kammala karatun kuma ya fito a matsayin dalibin da ya fi kowanne a wannan shekarar sannan kuma daya daga cikin dalibai na musamman da aka tabayi a makarantarnan tunda aka kafata, ina farin ciki sosai tare da fatan ubangiji ya cigaba da bude masa kwakwalwa ya cigaba a bashi sa'a a duk abinda ya saka a gaba har karshen rayuwarsa da sauran dalibai baki daya, sannan ina shawartar gwamnatin jihar nan da ta tallafawa wannan yaro idan ba hakaba ba karamar asara za'ayiba domin bashi da mataimaki wahalhalun wannan rayuwar zasu iya saka shi yin giving up kar gwamnati ta sake ta bar wannan yaron a haka dan ba yarone da za'a kalleshi ayi murmushiba yarone da za'a kalleshi sannan a kama masa hannu domin ya mike, yarone da gwannati zata iya investing dukiya akansa domin zata fanshi abinda ta zuba ta hanyar alfanun kwakwalwarsa, yarone wanda Nigeria zatayi alfahari dashi a duk inda ya shiga, ina fatan al'umma zasu miko hannayensu mu taru mu zamewa yaranmu masu kwakwalwa marasa galihu gata"

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Stories to obsess over. Discover now