Chapter 35

52 8 0
                                        

Yau tun safe Abdulrahman yana tashi ya kudura a ransa koma menene zai faru to tabbas yau sai yayi Magana da Amira insha Allah dan haka ya shirya ya nufi asibiti sai dai kafin ya kai izuwa office dinsa sai daya fara zuwa station dinsu Amira a labour room ya duba duty roster dinsu ya tabbatar tana da aiki da safennan sannan ya wuce yayi round kafin ya shiga office ya fara duba marasa lafiya, 12pm patients dinsa suka kare ya fito ya kuma yin round wa wadanda ya yiwa aiki sannan ya wuce dakin su Amira, tana zaune tana cin meat pie da lemo dan batayi break ba sai yanzu suna hira da sauran yan uwanta ya shiga dakin, dan knocking kofar yayi duk suka dago suka kalleshi sannan suka gaisheshi ita kuwa ta sunkuyar da kai meat pie din data gutsira yaki hadiyuwa ya makale a makogaronta, da murmushi a fuskarsa yace “dan Allah idan babu damuwa ko zaku iya bani aron office dinnan naku na mintina goma kawai” da sauri suka mike suna cewa “ahh yallabai babu damuwa bismillah” da sauri Amira itama tabi ayari suka doso hanyar fita, tana zuwa daidai kofa inda yake yasa hannu ya rike hannunta sannan ya janyeta gefe tuni ta kware da meat pie din da take ta faman rikewa a baki ta fara tari, murmushi kawai yayiwa nurse din data tsaya tana kallon hannunsu sannan ya nuna mata kofa da idonsa da sauri tayi waje har tana tuntube tana fita ya maida kofar ya rufe sannan ya dauko ruwan daya gani a ajiye kan table ya bude ya mika mata.

Bayan ta gama sha tarin ya lafa tace "haba yaya Abdulrahman ya zaka rikemin hannu a gaban mutane so kake su fara gulma ko suyi tsammanin wani abune tsakaninmu" yaja kujera ya zauna sannan yace "ohh da ba wani abunne tsakaninmuba? Beside yaushe rike hannunki ya zama laifi ban saniba?" ta harareshi yayi murmushi har saida hakoransa suka fito yace "God yaushe rabon da ayimin wannan hararar? Nayi missing dinta sosai" ta nemi waje ta zauna tace "yaya Abdulrahman me kake bukata?" yace "soyayyarki" ta kuma harararsa yace "cigaba ba karamin son wannan idon nakeba idan yana harara" a zuciye ta kalleshi tace "yaya Abdulrahman please be serious what do you want?" ya gyara zama yace "i told you soyayyarki! wai Amira me yasa kikemin wannan abin? Me yasa kike azabtar dani kwana biyu? Kinsan kuwa wahalar danasha kwana biyunnan? Wallahi ko bacci banayi ishashshe" ta nemi waje ta zauna tana dauke kai, maganar gaskiya kalamansa ba karamin dadi suke mataba amma ba zata bari ya ganeba.

Ya jawo kujerarsa zuwa gabanta yace "Amira please dan Allah ki tausayamin wallahi ba dan karamin so nake mikiba ki bani dama na tabbatar miki ki bani dama na nuna miki irin son da nake miki, ki bani dama na nuna miki matsayinki a zuciyata ki tausayawa yayanki dan almajirinki ki bashi sadakar zuciyarki kinji?" ta juyo tana kallonsa yana kallon idonta yasan ta fara saukowa idanuwanta sunyi laushi dan haka ya cigaba "Amira kinsani kinfi kowa sanin ina sonki so mai tsanani ta yaya zakiyi kokwanto a kaina? Kinfi kowa sanin wayeni babu abinda na tabaso irinki tunda nake duk abinda zanyi ko zan nema dan ke da Khadija ne ku kadaine mutane mafiya daraja a rayuwata amma wai kece kike kokwanto akan son danake miki Amira please ki yarda dani ki bani dama zan tabbatar miki da abinda ke zuciyata" haka ya zauna ya cigaba da gaya mata kalamai masu dadi da ratsa zuciya kafin wani lokaci ta sake suka fara hira yana cigaba da gaya mata zuciyarsa da irin son da yake mata basu san lokaci ya tafi sosaiba har sai da daya daga cikin nurses din da suka fita tayi knocking a zuciye Abdulrahman ya mike ya bude ya fara masifa "ya akai bugun kofar me kikemin?" ta fara inda inda tace "aa yallabai dama hijabi zan dauka zanyi sallahne anyi sallah a masallaci" yace "sallar me akayi? Kya dai nemo abinda zakiyi" ya juya ya koma mazauninsa ita kuma ta bude jakarta tana neman hijab, Amira ta duba agogon hannunta taga karfe biyu da sauri tace "lahh har karfe biyu tayi?" Abdulrahman yace "agogonki bayayi dai" tace "wallahi yanayi" nurse din da ta dau hijab tace "da gaske karfe biyu tun dazu aka fito daga masallaci" da sauri ya dauko wayarsa ya duba sai kuma ya mike yana cewa "subhanallahi ya akai ban san lokaci yaja hakaba ina da appointment 1:30pm fa wallahi na mugun makara" Amira ta fara dariya ya kalleta yace "duk ai laifinkine kina min fari da idanu kin saka ban san lokaci yaja hakaba" gulmammiya nurse dinnan tayi sauri ta fice tana dariya Abdulrahman ya juya ya kalleta sai kawai yayi dan murmushi sannan ya juya har ya kai bakin kofa sai kuma ya waigo yace "zaki dau wayata yanzu ko?" ta daga masa kai tana murmusbi shima ya tsaya yan kallonta sai kuma yayi yar daiya ya fice da sauri.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Historias para obsesionarse. Descúbrelo ahora