Jiki a sanyaye Abdul Rahman ya kamo hannun dan uwansa suka bar wajen, zuwa yanzu har wani jiri yakeji amma bazai nunaba saboda kar hankalin Abdul Rahim ya sake tashi. Waje suka samu suka zauna suna kallon kowa na ta faman alwala wasu har sun tada sallah sai dungurawa suke daga gani babu abinda suka iya, ganin ana Shirin watsewa a barsu a wajen yasa Abdul Rahman kallon Dan uwansa yace "Abdul muma muyi sallar sai mu je muyi baran tunda kaga babu wanda zai bamu abinci idan ma mun zauna ko?" Hankali a tashe Abdul Rahim yace "to yanzu idan munce ma zamuje baran Ina muka sani? Wajen wa zamuje?" Kafin Abdul Rahman ya ce komai wani yaro da bazai wuce shekarunsuba yazo ya zauna a kusa dasu yace "ko kukan jini zakuyi a wajen nan babu wanda zai taimaka muku abinda yafi kawai ku taso muje muyi barar zan nuna muku wuraren da muke zuwa sannan na nuna muku hanyar dawowa, ku taso" kallonsa kawai suka tsaya yi dan basu taba ko ganinsaba balle suce sun sanshi, Dan murmushi yaron yayi yace "sunana Bello nima almajiri ne anan makaranatar kuma na dade dan nafi shekara anan nasan unguwanninnan ku taso muje" juna suka kalla cike da neman shawara sannan kuma suka mike Abdul Rahim yace "Bari muyi sallah" Bello ya kalleshi yace "ai tunda bakuyi da wuri ba kawai kuzo muje idan ba hakaba idan dare yayi ba zamu samuba idan mun dawo sai ku hada da Isha kawai kunsan karfe takwas zamu shiga karatu kawai ku taho" haka sunaji suna gani sukaje suka dauko kwanukan da babansu ya saka musu cikin bagco dinsu sukabi bayan Bello.
Gida gida suka rinka bi suna barar amma duk gidan da sukaje sai dai a basu hakuri har aka fara Kiran sallar Isha sannan suka samu wata Mata ta Basu shima bashi da yawa dan bai wuce mutum daya ya cinyeba, da tsoro a fuskar Bello ya kallesu yace "sai munyi sauri fa an kusa shiga makaranta kuma su labaran duka sukeyi sosai wallahi" jin haka hankalinsu ya kuma tashi suka cigaba da zagaye, har sun fitar da rai sai wani mutum yayi kiransu gidansa ya basu abinci Allah ya taimakesu da yawa dan haka suka zauna suka hada da na wanda suka fara samu sukaci, suna cikin ci kawai Abdul Rahman ya saka kuka duk suka bishi da kallo Abdul Rahim ya taba goshinsa still da zafi amma ba kamar dazunba, cikin damuwa yace "Abdul menene?" Kukansa na kuma karfi yace "Abdul Khadija, nasan Khadija bataci abinciba yanzu nasan tanacan tana kukan nemanmu yau ita kadai zata kwana yau babuko wanda zai daura mata rigar sauro sauro zasuyi ta cizonta" shima Abdul Rahim din hannu ya cire ya zauna sosai ya dafe kai hankalinsa a matukar tashe gashi sunyi nisa da yawa da kanwarsu balle susan halin da take ciki, ko a wanne hali take yanzu? Ya daukarwa kansa alkawarin bazai sake kukaba har sai ya Yi karfin da zaije ya dau fansa akan babansa sannan ya dauko Khadija ko a titi su dinga kwana amma dai yasan suna tare, kudirin da yayi kenan a dazu da babansa mahaifi yasa kafa ya bangajeshi kamar shara.
Haka sunaji suna gani suka kasa ci gaba da cin abincin, babu yadda Bello baiyiba amma sun kasa cire damuwar a ransu, sai kawai ya hakura yaci shi kadai ragowar kuma ya dauko musu yace watakil idan an tashi daga karatu zasu iya ci.
Haka rayuwa ta farawa yan biyun kullum da asuba za'a tashi ayi karatu zuwa karfe takwas sannan sai su tafi bara zuwa goma zasu koma makaranta ba zasu tashiba sai 12pm nan ma zasu tafi wani baran na rana zuwa hudu zasu sake shiga karatu su tashi shida sannan su koma takwas na dare su tashi goma. Kullum abinda sukeyi kenan daga karatu sai bara, kuma da yake sun dan sami karatun lokacin da innarsu na da rai sai ya zamana basu sha wahala sosaiba, babbar matsalarsu a rayuwa shine rashin sanin halin da yar uwarsu ke ciki, yunwa kuwa damanko a gidansu sun saba da ita tunda ba kullum ake basu abincinba idan an basuma Khadija suke barwa saboda kankantarsa.
Washe garin da sukazo garinne suna wajen bara sabon abokinsu yake basu labarin kansa, a zaune suke akan wata baranda sun gaji da bara basu samuba sai suka kwanta suna hutawa, Bello yayi rub da ciki yana kallonsu yace "kamar yadda na gaya muku jiya sunana Bello daga jigawa Mal ya daukoni garin gujungu kunsan garin?" Duk suka girgiza kai sai ya cigaba "wani garine da nisa daganan acan aka daukoni sunan babana muntari dan acaba, tunda na tashi ni dai bansan innataba ban taba ganintaba, babana yace mutuwa tayi amma inna hadiza matarsa tace wai ni shegene babane yaje yawonsa ya haifeni shine ya kawo mata, Inna hadiza ta tsaneni sosai komai nayi laifine kullum tana cikin dukana bata bani abinci, kullum sai ta dinga cemin shege ko Dan cin amana a cewarta amanarta babana yaci, ban san waye mai gaskiya a cikinsuba amma nafi gaskata inna hadiza saboda kusan duk garin abinda suke cewa kenan, babana yana sona sosai fiye ma da 'yayan inna hadiza, idan yazo ya tarar baa bani abinciba zaiyi ta fada ya kama hannuna muje ya siyomin kifi ko awara ko rake wani lokacin har da biscuits, idan bayanan sai inna hadiza tayi ta dukana tana sakani aiki masu wahala shine wani abokinsa rannan ya bashi shawara yace ya kawoni Kano almajiranta zanfi samun sakewa akan can din, da farko ki yayi ya tsorata yace bazai taba yadda na saka kafata a kanoba sai daga baya bansan yadda akayiba mal yana zuwa daukar almajirai sai Baba yace na hado kayana na bishi, shine dalilin zuwana nan" Abdulrahim yayi ajiyar zuciya yace "kuma tunda kazo baban naka yana zuwa wajenka?" Bello ya daga kai sai kuma ya girgiza shi a sanyaye yace "sau daya yazo" Abdulrahman ya jinjina kai yace "kaji dadinka dama mune" Bello yace "tab kajika ni fa ban taba ko ganin innata ba bani da kanwa babane kawai dani ku kuwa kunsan innarku sannan ga khadija kunsanta ko yanzu kuka koma gida zaku ganta" ya sunkuyar da kai kasa yace "kuma idan ya zamana inna hadiza ce mai gaskiya ba babana ba ni fa shegene kenan" Abdulrahim yace "meye shege?" Bello ya daga kafada yace "nima ban saniba kawai dai nasan wani mugun abunne watakil wani ciwonne"
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
