Chapter 48

70 10 8
                                    

🚫Not edited

Har dady yakai bakin kofa momy tace "dady" muryarta na rawa alamar kukan da takeyi bai kulataba yayi waje ita kuma ta mike da sauri ta biyo bayansa tana cigaba dayi masa magana, suna fitowa ya juyo a fusace batayi auneba sai ji tayi ya dauketa da kyakykyawan mari wanda sai dataga wucewar wuta a idonta ta kuma zube a wajen, dady ya nunata da yatsa. Yace "mariya me nace miki? Me nace miki akan yarinyarnan?" da gudu Abubakar yazo ya riketa tace "wallahi Allah dady zuwa nayi na gaya mata na yadda na tarar da ita a haka wallahi na yadda a aura matashi" cikin fushi dady yace "na gaya miki ina bukatar yaddarki? Bana bukatar yaddarki idan kinso ki mutu amma insha Allahu sai na aurawa Amira Abdulrahman ko kinaso ko kinaki kuma daga yau tabar gabanki dauketa zanyi gaba daya sai kin sake ganinta sannan zaki nemi kashemin ita tunda ke bakya sonta mu muna sonta kuma da kike maganar sun daki danki ke kin binciki dalilin da yasa suka dakeshin? To kanwarsu yace yanaso duk da sunsan ba sonsu yakeba suka yadda shine ya zagesu a gabanta ta tare musu ya daketa, ko aurenta yakeyi kuwa ya saka hannu ya daketa wallahi ko ni ubansa sai na kashe auren bayan ya kwana a hannun yan sanda mutuniyar banza kawai gani kikayi ana lallabaki shiyasa" Umar ya rike hannun dady yana cewa "dady please ya isa haka dan Allah ku daina" dady ya juyo ya kalli umar yaxe "umar ai an daina ba za'a kumaba ba sai tana gidan sannan za'a kumaba? Idan tabar gidan ai banma gantaba balle nayi mata magana" umar ya kara kankame hannun dady su Abdulrahim ma duk suka taso suna bashi hakuri ana haka Usman ya shigo sai kuma ya tsaya yayi dim yana kallonsu momy na kasa tana kuka su kuma duk sunyi wani tsarko carko, da hanzari ya karaso wajen momy yana cewa "subhanallahi momy lafiya menene ya faru?" ya daga kai yana kallon abubakar yace "yaya menene yake faruwane?" Abubakar ya dafe koshinsa saboda wani irin sarawa da yake masa yace "Amirace" Usman ya kalli kofar dakin Amira ya kuma kallon Abubakar yace "tayi me?" Abubakar yace "ta sami attack ne" Usman ya kuma kallon kofar dakin Amiran sannan yayi wata yar dariya yace "wallahi karya take pretending ne" ai kuwa kamar ya ballo dam din daya cika yake shirin ballewa da kansa, anger din da ba'a bari dady yayi releasing akan momyba ya juye masa dan rufeshi kawai yayi da duka kamar wanda Allah ya hallicceshi purposely dan ya dakeshi.
Gaba daya gidan suka fara kokarin rike dady yayinda Abdulrahim ya janye Usman daya tsugunnun da dady bai barshi ya mikeba momy kuwa ko motsi batayiba sai kara sautin kukanta da tayi, dady yace "kai wanne irin tantirine Usman? Kaine silar komai amma ba zamaka ji tausayin yar uwarkaba ta kusa mutuwa sannan kace wai pretending take? Wato bata dameka bama ko tayi rai ko ta mutu ko?" dady na cikin wannan fadan Aliyu ma ya shigo da earpiece dinsa a kunne dan baisan abinda ke faruwaba sai daya shigo yaga mutane a tsaye tsarko tsarko da sauri ya zare earpiece din yana binsu da kallo, ga masu kuka nan nayi (momy da Khadija) ga kuma masu tashin hankali rubutuce a fuska tamkar zai fara diga kasa dan yawa, jiki a sanyaye ya karaso dakin koma menene yasan ba abin arziki bane yake faruwa ya kalli umar da yafi kusa dashi kamar me rada yace "what's going on?" fuskar umar kamar zaiyi kuka yace "Amira ce..." ai Aliyu baiji karshen zancenba ya fara kiran "innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbiyallahu wa ni'imal wakil" kawai sai yayi dakin Amiran da gudu shima umar ya bishi sai a ciki ya samu ya kamoshi suka fito har ya fara hawaye kira yake "yaya Umar me ya sameta ba abinda ya sameta ko tana raye ko? Innalillahi" dady ya dan dauke kansa yace "hmm" sannan ya kalli Usman da shima ya fara hawaye yace "kagani ko? Kaga yaran arziki masu son juna ko? Baima tsaya an gama gaya masa abinda ya sametaba amma hankalinsa ya tashi babban tashin hankalinsa ace wani mummunan abu ya sameta amma kai da yake shedanne a kanka abinda ka farayi shine dariya ka kumace wai pretense ne, wallahi banda kai a gida aka haifeka na rantse da Allah da cewa zanyi kai ba dana bane musanye akayimin dan gaba daya komai naka ya fita daban ka fita daban da yan uwanka ba abinda zance maka sai dai Allah ya shiryeka ya nuna maka hanyar daidai" yana rufe bakinsa ya juya ya fice daga gidan, su Abubakar dai babu mai bakin magana sai zagaye momy da suka sakeyi harshi Usman din shi kuwa Abdulrahman juyawa shima yayi ya fita harabar gidan sai kuma ga su Bello sun biyo bayansa duk suka samu waje kan baranda suka zauna kowa yaza uban tagumi.
A cikin falon kuwa bayan momy ta sassauta da kukan da takeyine su Abubakar sukayi tayi mata nasiha bayan sun sanar da Aliyu abinda ya faru a lokacin take sanar musu itafa dama can ta hakura ta yadda da aure tsautsayi shiga tayi ta gaya mata ta yadda taje ta tarar da ita yadda take amma ta yadda Amira ta auri Abdulrahman ko ma wanda baikai Abdulrahman din bane indai shi yari yar keso ta yadda, shi ma Usman sukayi tayi masa fada har aka koma nasiha shi dai baice kalaba har sukayi suka gama.
Wajen 12am babu yadda Abdulrahman baiyi dasu Abdulrahim su tafi gidaba amma kowa yaki Khadija har gyangyadi takeyi amma itama taki tafiya, momy ta leko wajen tace "Khadija ya kuke zaune anan akwai sauro fa ku shigo ciki mana kizo ma ki kwanta haka" suka taso suka shigo falon momy tace "muje dakina sai ki kwanta ga idonki nan bacci kikeji" Khadija ta kalli Abdulrahman yayi mata murmushi yace "kije ki kwanta muma munanan babu inda zamu" momy da idanunta suke kumbure sosai saboda kukan da tasha ta danyi mata murmushi tace "dan kinga Amira bata da lafiya shine kike abu kamar bakuwa? Yau kika fara kwana a gidan? Muje maza ki kwanta" haka momy ta kai Khadija har dakinta ta shiga toilet tayi abubuwan da zatayi tana fitowa momyn ta bata wata doguwar rigar bacci ta saka sannan ta kwanta tare da jan bargo ita kuma momyn tayo alwala ta hau kan sallaya.
Su Abdulrahman kuwa dakin umar suka shiga suna shiga Abdulrahman yayo alwala shima ya tada sallah dan haka gidan gaba daya babu wani wanda yayi baccin arziki ita kanta Khadija dake kwancen bacci na fara daukanta sai taji kamar hayaniya sai tayi firgigit ta farka dady kuwa na cikin mota tun sanda ya fita sai wajen 2am ya dawo ciki shima ya tada sallah haka har asuba sannan duk suka fito da nufn tafiya masallaci, suna fitowa Abdulrahman ya kalli kofar dakin Amira sai ya kamo hannun Aliyu yace "Aliyu zo muje ka rakani na duba ko ta farka" ba musu ya bishi da sauri, a hankali Abdulrahman ya tura kofar dakin dan kar tayi kara suka shiga har yanzu bacci take amma ta gyara kwanciya sannan daga yadda numfashinta yake sauka kasan lafiyayyen bacci takeyi, ya dan duddubata sannan suka fito suka nufi masallaci gaba dayan.
Bayan sun dawo suka tarar da momy a falo ta gaishe da dady amma sai kawai yayi kamar baijitaba amma da yaram suka gaisheshi duk ya amsa suka gaisheta itama ta amsa musu kamar zatayi sannan Abdulrahman ya kuma yafitar Aliyu suka koma dakin, har yanzu tana kwance amma idonta a bude yake ta kurawa waje daya ido, da sauri suka karasa shiga dakin abinda ya janyo hankalin sauran kenan suma sukayi dakin gaba daya, Abdulrahman ya tsugunna a gabanta ta kare masa kallo idonta ya kawo kwalla tace "yaya Abdulrahman" yace "shshh kar ki fara kuma kuma mana daga tashi? Ya kikejin jikin naki" murya na rawa tace "da sauki" ya duddubata ya kuma yi mata tambayoyi akan yadda takejin jikin nata duk ta amsa ya tabbatar babu wata sauran matsala sannan yayi mata murmushi yace "to maza a tashi aje ayi sallah" ta yunkura ta tashi zaune sai kuma ta karewa yan uwanta da suka cika dakin da kallo ta tsayar da idonta kan Abubakar tace "kai yaya Abubakar anan ka kwana?" shima ya tsugunna a gabanta yace "princess kin tsoratamu ba dole na kwana anan ba?" sai kuma ta dan tabe fuska kamar mai shgwaba dinnan tace "I'm sorry" yayi saurin kamo hannunta yana cewa "hey it's ok amma karki kuma tsoratar damu haka kinjiko? Allah ya baki lafiya" duk dakin suka amsa da ameen sai kuma ta kalli dady ta mika masa hannu tare da cewa "dady" yayi saurin kama hannunta ya zauna bakin gadon yana cewa "naam princess ya jikin naki" ta sake kyabe fuska cikin shagwaba tace "da sauki" yace "babu abinda yake miki ciwo yanzu ko" ta daga kai ya kama fuskarta da hannayensa yana kallon cikin idonta yace "princess ki kwantar da hankalinki karki kara saka wani abu a zuciyarki har wani abu yazo ya kuma samunki duk abinda kikeso shi zaki samu kinji?" ta daga kai sai kuma ta kalli momy ita kuma tayi mata murmushi tare da jinjina kai itama Amira sai ta maida mata murmushin. Nan fa kowa ya zagayeta kowa burinsa yaji ya jikin nata yake sai da kyar Abdulrahman ya koro kowa yace a kyaleta ta huta.
Tun daga lokacin kowa na gidan dady hankalinsa na kan Amira burin kowa ta samu duk abinda take bukata burin kowa tayi farin ciki, mutane na ta zuwa dubiya duk da ba asibiti aka kwantar da itaba Abdulrahman ne ke dubata sosai tare da asalin Dr din da take gani duk da shi sau daya ma yazo ya dubatan sai yace ba matsala ai tunda gata a babban likita. Har yanzu momy ta kasa samun courage din tunkarar dady tayi masa magana so take ta bashi hakuri ta kuma tabbatar masa da dama fa can tayi nadama yanzu ita kam tana son wannan auren 100% amma ko fuska yaki ya bata balle ma ta gwada.
Satin Amira guda yan uwa suna zuwa dubata wanda yayi dai dai da biki saura sati uku, har yanzu yan uwanta nata lallabata suna daukarta a matsayin marar lafiya a kuma ranar ne da daddare anty zulai ta fito zata tafi gida suka fito ita da Amiran daga dakinta tana cewa "ki koma kiyi kwanciyarki mana uwata ina zaki haka? Akwai sanyi fa a waje" Amira tace "ai ba har can waje zanjeba" suna fitowa sukaga dady a zaune a falo anty zulai ta karaso wajensa tana cewa "au yaya ashe ka shigo" yace "yanzu ai naga motarki a waje nake cewa baki tafiba kenan har yanzu" ta zauna kujerar kusa dashi tana cewa "wallahi kuwa yanzu dai zan tafi" suka sake gaisawa sannan dady yace "ai namaji dadin tarar dake da nayi dama ko kin tafi gobe zan biyoki saboda yarinyarnan inaso ki tafi da ita can gidanki idan an tashi bikinma inajin kawai ayi acan ko gidan hajiyarmu" anty zulai ta kalli Amira data sunkuyar da kai ta juya ta kalli momy itama data fito daga kitchen amma tanajin maganar da akeyi sai ta sunkuyar da kai kasa, ta juyo tana kallon yayan nata tace "yaya menene yayi zafi haka? Me yasa ba za'a barta anan dinba barin gida zatayi a barta ta karashi tare da mahaifiyarta" dady ya zauna sosai akan kujerar da yake yana kallon anty zulai yace "zaki tafi da itane ko na kaita gidan hajiya? Nace kene saboda dama ke kike shirin bikin" anty zulai ta girgiza kai tace "yaya anty Mariya tayi nadama ta yadda da auren ka sake bata dama dan Allah" dady ya kalli momy a kofar kitchen kai a kasa amma yan iya hango hawayen dake bin fuskarta yace "zulai mariya munafukace ba wata nadama da tayi ba zata taba nadamaba indai Usman na nan saboda bazai taba bari tayiba" da sauri anty zulai ta kalli Amira wanda itama kuka take tace "uwata shiga ciki maza" Amira ta kalli dady pleadingly sannan ta mike ta koma dakinta, tana shiga anty tace "haba yaya haba yaya ta yaya zaka zaki uwa a gaban danta? Ko me anty mariya tayi uwar Amira ce bai kamata ka zageta a gaban Amira ba sannan kuma wallahi ba munafuncinci bane na yadda da nadamarta ka bata dama wallahi tana kara misbehaving ni da kaina zanzo na dauke yarinyar" dady yayi murmushi yace "kina tsammanin idan ta cigabaa da misbehaving din kullumne zamuzo mu tarar da Amira a raye? Abdulrahman fa yace ba'a fiya samun wanda yayi dadewar da tayi a halin da take kuma ya tashiba yawanci mutuwa suke shiyasa itama har yanzu bata gama warkewaba ko basu mutuba kansu na tabuwa to wacce zaki dauka? Gawa ko mahaukaciya?" anty zulai tayi shiru ganin ba zata amsaba ya cigaba" kawai ki gayamin ba zaki tafimin da itaba nasan inda zan kaita" anty zulai tace "haba yaya ta yaya zance bazan tafi da Amira gidanaba? Amira 'yatace gidana gidansune amma kaga yanzu bata shiryaba gobe da kaina zanzo na dauketa kaga sai mu shirya a tsanake" kada kai kawai yayi dan yaga alamar batayi niyyar daukan Amiran bane shi kuma zaisan inda zai kai' yarsa dan bazai bari sai ta mutuba tukunna.
Washe gari tunda sassafe anty zulai ta hado kan yaranta dana dady gaba daya sukazo gidan tunda wuri suka tasa dady a gaba haka momy ma ta fito Amira ma haka gasu Abdulrahman da Umar ya kirawo gaba daya suka tasa dady a gaba da ban hakuri da lallashi a karshe dai har sai da ya hakura ya kumace zai sake bawa momy dama ta karshe tunda ta rantse tace ta daina yanzu tana goyon bayan auren. A karshe dai momy tafi dady har daki tayi ban hakuri da kuka sosai sannan ya yafe mata komai ya koma daidai.
(a gurguje 🏃‍♀️🏃‍♀️)
Tun daga lokacin komai ya koma normal aka cigaba da shan soyayya tsakanin amare da angwaye haka Bello da Khadijansa duk da sunce sufa ba zasuyi aure tare dasu Abdulrahman ba nasu sukeso su kadai, yan uwan ta koina sun fara shigowa haka habu ma ya dauko matarsa sun da niyyar idan an gama biki ita zata koma gida shi kuma zai fara aiki a asibitin su Abdulrahman, baba ma yazo yan uwansa kuma sai ana e gobe daurin aure zasuzo da wadanda ya gayyato daga can, biki saura sati biyu aka kai kayan lefe kowacce amarya set uku uku komai iri daya hatta da kalolin akwatunan banbanci kawai size ne, hajiyar Belloce ita da yan uwanta sukaje sukakai kayan gidan kowa su sukayi duk abinda iyaye mata keyi.
Haka shirye shirye suka cigaba da gudana Bello da Khadija sune organizers komai a hannunsu yake tare sukeyin komai suna kuma zuba tasu soyayyar, a haka har satin biki ya kama, gidan bello gaba daya aka kasheshi saboda abokansu da sukazo har da na Stanford University nan shine ya zame musu masaukin baki wani hotel kuma suka bawa kwangilar abinda bakin zasu dingaci komai a wadace, a yadda suka shirya bikin kowacce amarya zatayi nata events din da takeso su kuma zasu hada musu walima wacce take ta mata zallah an gayyato malamai masu fada aji da zasuyi jawabai sosai akan zaman aure ranar alhamis kenan juma'a kuma zasuyi event babba guda daya na kowa da kowa maza da mata dangin Amira da na Aisha dasu kansu nasu dangin wannan shine mafi girman event da zasuyi asabar kuma da daddare zasuyi dinner shi kuma nasu su da abokansu da amrwnsu sai yan matan amarya lahadi daurin aure sai kai amare da daddare.

................
Hi angels
Don't forget to vote and comment.
Thank you

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant