Haka Abdulrahman ya juya yafice daga gidan shima ko abincin bai ciba, ranar wuni yayi a asibiti su kansu patients din sam basu gane kansaba haka abokanan aikinsa gaba daya yau ya koma tamkar wani marar mutumci banda masifa babu abinda yakeyi. Su kuwa su Abdulrahim suma haka suka wuni maganar abin Khadija ta bashi labarin hirar da sukayi da Amira suka kuma wuni suna neman yadda zasu bullowa lamarin domin ba zasu taba bari wata ta kuma shigo musu sama taka ta lalata tsakaninsu da Amiraba. Abdulrahim yace "wallahi Khadija danma bakisan abinda Amira tayi manaba har yanzu bamu samu lokaci mun zauna mun bawa juna labarin yadda mukayi rayuwaba da kinji da sai ranki ya kuma baci, kuma bawai inason Abdul ya auri Amira a kamar matsayin biyan bashi bane bawai inason Amira saboda abinda tayi mana bane ko daya inason Amira a matsayinta na Amira sannan kuma kamar yadda bazan taba badake inda zakisha wahalaba haka bazan taba yadda Amira tasha wahalaba ina kuma ganin Abdul shi kadaine zai iya rikemin amanarta shi kadaine zai iya jiyar da ita farin cikin da nake mata burin taji, bayan Abdul sai ko Bello ko ni da kaina amma duk bamu Amira keso ba shi takeso dan haka abinda takeso shi zata samu"
Abdulrahman bai dawoba sai dare yana shigowa yaje dakinsa ya gama abinda zaiyi sai ya wuce sama yana son danyin bincike akan wani abu, yana shiga yaga Abdulrahman na exercise ya kalleshi kawai ya dauke kai yayi wajen study area dinsa, Abdulrahim shima baiyi masa maganaba har ya gama abinda zaiyi ya tashi da niyyar sauka sannan Abdulrahman yace "Abdul" Abdulrahim ya waigo ya kalleshi ba tare daya amsaba ganin bazai amsaba ya cigaba "gobe su Zainab zasuzo" Abdulrahim ya danyi dariya yace "zasuzo ina?" Abdulrahman yace "nan gidan" Abdulrahim ya tsaya ya kare masa kallo sannan ya juyo ya nufo inda yake yace "me zasuzoyi? Ita dawa? Ina fatan soyayya bata saka ka manta da cewar gidannan mu kadaine a ciki bamu da iyayeba bansan me zatazo yi gidan samari ba" Abdulrahman yace "ba ita kadai zatazoba ita da yayanta da matarsane sun shigo kasar bansan me yazoyiba suka biyoshi shine takeson kawo mana ziyara kafin su koma kuma banajin laifine hakan" Abdulrahim yace "kawo maka ziyara dai ba muba" ya juya zai fice Abdulrahman yace "Abdul ya kamata ku tausayamin ku daina wannan nuna halin ko in kula din da kuke yimin duk cikinku banajin akwai wanda ya kaini cutuwa cikin maganar nan, wallahi inason Amira ban taba son wani abu yadda nakeson Amiraba da soyayyarta na rayu bazan iya tantance ranar dana fara sontaba kawai inajin tsorone" ya fada tare da sunkuyar da kai kasa, Abdulrahim ya jawo kujera ya zauna sannan ya saka hannu ya rufe computer din dake gaban Abdulrahman yace "menene kake tsoro Abdul? Banajin a dictionary din soyayya akwai wata word tsoro" Abdulrahman yace "amma akwai word Care, ina tsoron idan muka fara soyayya da Amira a karshe aka hanamu juna halin da zamu shiga dagani har ita musamman ma ita daba lafiyace ta ishetaba" Abdulrahim yace "wanene zai hanaka Amira akan kuma wane dalili?" Abdulrahman yayi shiru ya kasa ci gaba Abdulrahim yace "kai kasan ko wata ka dauko kace kanaso dady mai shigewa ne gaba yaje ya nema maka ita ko ita wacece kuwa sannan kuma kayi tsammanin zai hanaka 'yarsa ta cikinsa ikonsa?" Abdulrahman yace "ba dadyne zai hanani Amiraba Abdul idan wata na dauko nace inaso shi kadaine zai shigemin gaba amma idan tasa 'yar na dauko nace inaso mutane da yawane zasu bani ita, Abdul kai kasan momy batasonmu ko kadan bata kaunarmu tare da iyalintama balle kuma ace mun zama iyalin nata, yan uwanta basa sonmu zasuyi kowanne irin abune domin su zigata taki amincewa da aure tsakaninmu, Usman baya sonmu kana tunanin bazai iya zuga mutanen da zasu bani itaba? Tukunnama a matsayina nawa zan je nace inason Amira? Zan hada Amira da dady fada da iyalinsune kawai"
Abdulrahim yace "Abdul don't be ridiculous kai kasan duk abubuwan da kake fada doesn't matter, what matters is Amira na sonka dady nasonka sannan baka da wani abu da zaka ce tabone da zaisa ba za'a baka aureba dan kayi almajiranta? Masu kudi nawane a kano da ada suke almajirai? Kai dan halak ne kasan inda iyayenka suke idan ma cewa akayi ka kawo iyayenka I'm sure kodan kudin da kake dashi yanzu ba zasu kasa zuwa nemar maka aureba kuma iyaye na gaske bana aroba, kana da iliminka kana da muhalli da aikinyi sai me kuma?" Abdulrahman ya sunkuyar da kai yace "Abdul ba zaka ganeba" Abdulrahim yce "no Abdul kaine ba zaka ganeba amma wannan ba dalili bane kayi fighting for your love idan ma bakaci nasaraba dai it's worth fighting for, Amira is worth fighting for, ballema banajin zaka kasa nasara sannan kana maganar wai bakason wani abu ya samu Amira saboda ciwonta already she's hurting idan bakayi wasaba yadda kake farke kirjin mutane kana wanke zuciyarsu ba fata nakeba wallahi wataran zakaga Amira kan theater table dinka" Abdulrahman ya bishi da kallo shi kuma ya cigaba "to wai ma tsaya idan kacemin kanason Amira ita kuma Zainab ko wacece ita kuma fa? Me kake mata?" Abdulrahman yace "wallahi babu komai tsakanina da Zainab kawai mutuncine naga da kai muka fara haduwa da Zainab din, fan dinkace sosai" Abdulrahim yace "amma tana sonka dan idanda don taimakon da mukayi matane sannan kuma tana fan dina tabbas da ni zata dinga bibiya ba kaiba sannan ya kamata ka taka mata birki dan dalilai biyu na farko karta shiga soyayyarka da yawan daba zata iya fitaba tunda kace kai ba sonta kakeyiba na biyu kuma saboda mutuncinku na batawa Amira rai, Abdul ka tuna cewa jiya ko sallama bakayi da Amiraba saboda kana waya da Zainab?" Abdulrahman yayi shiru yana kallon dan uwansa Abdulrahim ya mike yace "ni zan wuce kayi tunanin abinda ya kamata kayi dai sannan gobe yaushe zasuzo?" Abdulrahman yace "da yamma" Abdulrahim yace "Allah ya kaimu" sannan ya juya ya fice daga wajen zuwa dakinsa.
CZYTASZ
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Dla nastolatkówLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...