Haka Abdulrahman ya juya ya tafibadan yasoba sai dan ya tabbatar mai shagon ba bashi zaiyiba haka yayi ta yawo shago zuwa shago haka yayi ta yawo amma kowa sai yace sai ya bashi kudi sannan zai bashi har sai DA ya core rai ya jiya da niyyar komawa makaranta yasan yanzu abdulrahim nacan yana nemansa sannan Allah yasa ya shiga wani shago yacewa mai shagon kwali yakeso mai shagon ya dauko masa sai da ya karba sannan ya CE masa "dan Allah nayi hakuri bani da kudi takalmin zanyi dashi nake bata idan na dawo zan kawo maka" kallonsa mai shagon ya tsaya yi sannan yace "me? Me zaka kawomin" abdulrahman yace "dama Wai kudin kwalin nake nufi bani dashi yanzu amma wallahi zan kawo maka idan ban kawobama a makarantar malam..." Katseshi mai shagon yayi sannan yace "ba sayarwa nakeba jeka kyauta na baka" ai kuwa nan abdulrahman ya fara hero masa addu'a har kamar zai ari baki. Da Saudi abdulrahman ya dawo makaranta ai kuwa ya Tatar da abdulrahim da bello hankali a tashe suna ta nemansa na suka tambayeshi ina yaje? Sai ya muna musu kwalin proudly yace "wannan nake Neman" cikin rashin fahimta abdulrahim yace "me zakayi dashi" waje ya samu ya zauna sannan yace "takalmin zanyi dashi" ya zauna ya yayyanka kwalin ya nannade kafarsa sannan ya zaka zare da allura ya dinke sai yayi kamar takalmi, fada sosai abdulrahim yayi masa yace "kasan dai wannan babu abinda zaiyi maka zagewa zaiyia banza akan wanne dalili zaka wahalar da kanka akansa?" Dan murmuhi abdulrahman yayi masa sannan yace "idan ya yace sai in kuma zuwa na memo wani kuma kwali daya ma ai ba zai kare kullum ba" badan abdulrahim yasoba dole ya kyaleshi a haka ranar yaje barar da zaij.
Bayan sun dawo daga barar suka shiga karatu sun tashi kenan abdulrahim ya tafi samo musu kwankwanin da zasuje su debo ruwan alwala shi kuma bello ya shiga soron ajjye musu allunansu abdulrahman kuma yana zaune a kofar makarantar tasu ya hango wata yarinya, gaba daya yarinyar ba zata wuce shekaru ukuba yana tafe yana kuka kafarta babu takalmin sai dai da alama Nata rashin takalmin ba irin nasa bane dan batayi kama da yaran dake shan wahalaba domin kayane irin na yan gayu riga da wando na jeans da dan hijabi a jikinta, duk da rana yayi sanyi sosai amma tafiya take yana dangale kaga saboda zafin da kasar yayi sanda ranar take dama, kallon ta abdulrahman ya tsayayi sai kuma wata zuciyar yace masa 'wannan yarinyar fa ba zata wuce sa'ar sannan da alama bata saba da zafin ranar ba watakil ma bata yayi dan haka yana bukatar taimako' kai ya dauke yana cewa "wani ya taimaka matan nima taimakon nake nema" kamar amsa ga maganarsa wannan barim dai na zuciyarsa ya kuma ce masa 'Khadija na bukatar taimako wata sanyi ko idan ka taimaka mata wani ya taimakawa taka kanwar' dajin haka ba tare da wani tunaniba ya mike tare da dosar Inda yarinyar take yana zuwa ya tsugunna a gabanta yana murmushi kallonsa ta tsaya yi fuskarta fall hawaye da magina, dan murmushi yayi mata yace "me akayi mini kike kuka?" Bayan hannunta ta zaka ta goge hawayen tare da shabunan magina yace "Yaya nake Neman kuma banga takalmin ba" yace "a ina kuka ajiye takalmin baki" kalle kalle ta farayi alamar dai bata saniba daukanta yayi sannan yace"kunsan hangar gidanku?" kai kawai ta daga masa yace "inane to?" Da dan hannunta ta nuna wani loko tace "canne" goyata yayi tare da bin lokon da ta muna masa yace "ku rinka nunamin kinji?" Tace "To" run yana muna masa hanya har ta rikice ta rasa ina kuma zasuyi dan haka sai ya fara yawo da ita yana tambaya ko wani ya Santa ko kuma ita zata game idan sunzo amma har aka fara fitowa daga masallaci babu alamar ma hangar sukayi dan haka ya uya koma makaranta, ai was suna zuwa suka tarar abdulrahim ya cika yayi fam yana ganinsuya fara masifa " Wai kai Abdul wannan wanne irin wulakancine da zaka rinka tafiya ba zaka gayawa mutane ba Anyi ta nemaka? Kasa gabana sai faduwa yakeyi na zata wani abunne ya same ka ina ma kaje ? Wacece wannan" ya tambaya yana kallon yarinyar da ta dauko daga bayan abdulrahman amma kuma ta buya a bayan nasa yana leken abdulrahim tsoro rubuce a fuskarta, dan murmushi abdulrahman yayi yana shafa manta da akayi mata parking yayi kamar acuci a cikin hijabin Nata yace "wallahi bata tayi na tsinceta..." Abdulrahim bai bari ya karasaba ya katseshi da cewa "sai kuma kaga cewar mu iyayen marayune da zaka daukota ko? Muma ta kanmu mukeyi balle ka kara dauko mana wani aikin" abdulrahman yace "hakanma bazai faruba yanzunnan zakaga iyayenta ko kuma mu kaita wajen malam kaima kasan baka wajenmu zamu ajiye ta ba, ka kuma yi hakuri na tafi ban gaya makaba na zata zata gane gidansu shiyasa naje kaita kafin ku dawo amma ta kasa ganewa" sannan ya tsugunna a gabanta yana mata murmushi yace "ya sunanki?" A hankali tana kallon abdulrahim kamar mai gudun kar ya daketa tace "amira" yace "eyyeh sunan Yan gayu" tayi murmushi ya cigaba "ni kuma sunana abdulrahman wannan kuma " ya nuna abdulrahim "kaninane sunansa abdulrahim sannan ina da kanwa yar karama kamar ke kin San ya sunan ta?" Ta girgiza kai yace "sunan ta Khadija" amira tayi yar dariya tace "zan dinga wasa da ita itama za'ayi wasa dani?" Yace "sosaima amma yanzu batanan" tayi yar dariya sai kuma ta kalli kafarsa tace "ina takalminka? Ko kaima ka batar dashi?" Shima kafar tasa ya kalla sannan ya maida idonsa kanta yace "ni ba batarwa nayiba tsinkewa yayi" tace "to ka saka wani mana ko ka kai a gyara maka" yace "ai bani da wani kuma bani da kudin kaiwa a gyara min" ta kare masa kallo sannan ta wani yamutsa dan hancinta tace "kuma bakayin wankama ko?" Ya kalli jikinsa wasu kodaddun kayane run wadanda suka taho dasu daga gida dama gashi sun gama tsufa tun a can dan haka duk sun yage sunyi baki tunda ba wani wanki suke samuba sannan ya maida idonsa kanta yace "me kika gani?" tace "gashinan kayanka sunyi datti kuma sun yage" tunani ya fara tunanin rabonsa da wanka ko wanki yana tunanin zai kamar sati biyu kenan rabonsa da wanka shima wancan da yayi da ruwane kawai babu sabulu fan basu da sabulun, murmushin dole ya kirkira dan ba karamin kunya yajiba yace "inayi mana" tayi dariya tace "karya ba zagin allah kuma mai karya dan wuta kan a jima ya mutu" ta fada tana wani watsa hannu kafin ya tattaro amsar da zai bata yaji daga bayansa ana "amira amira" da sauri suka waiga a tare shi da amiran sukaga wasu samarine daya bazai wuce sa'an su Abdul ba dayan kuma babbane sosai dan zai wajen 18yrs, yana ganin su yayi wajen su da gudu ta rungume kafafuwan babban yana cewa "Yaya abubakar kaga Yaya Usman ya tafi ya barni ko? Ina ta kukashine Yaya abdulrahman ya goyani mukaje bamuga gidaba muka dawo ina tambayarsa me yasa baya wanna? Yaya danshi almajiri ne shiyasa baya wanka?.." kai Wanda ta kira da Yaya abubakar ya dungure mata yana cewa "to zaku duk ban tambayeki wannanba ina kikaje Usman din yayi a nemanki bai gankiba?" Tace "takalmina yara suka dauke shine na tafi nemansa ban ganshiba kafata zafi ina ta kuka shine yaya abdulrahman ya goyani mukaje neman...." Hannu abubakar ya daga mata yace "ya Isa amira kin bani wannan labarin Yaya abdulrahman ya goyani kunje bakuga gidaba ko?" Ta fara dariya yace "eh kuma Yaya abubakar Yaya abdulrahman bashi da takalmin nasa ya tsinke danshi almajiri ne bashi da wani zaka bashi naka?" Yace "eh zan bashi yanzu dai hau bayana mu tafi dan nasan zamu iya kwana anan kina magana baki gajiba" ya tsugunna ta haye bayansatana dariya sannan ya juyo wajen abdulrahman dake jinsa tamkar tsirara a gaban wadannan Yan gayun yace "da alama kaiine Yaya abdulrahman din ko?" Abdulrahman na yar dariya yace "eh nine dama na gantane yana kuka kuma bansan gidanba munje bata ganeba shiyasa muka dawo nan ko za'azo nemanta" abubakar ya sanyi masa murmushi tare da muka masa hannu yace "to mun gode sosai kaga shashashan da ta biyo shi kuma ya tafi ya su momy nacan hankali a tashe ba'aga princess ba" wanda tun da sukazo baice komaibane ya doke hannun da abdul ya miko wa abubakar sannan ya bishi da wata muguwar harara yace "haba yaya almajirine fa kake Neman shaking hannunsa itama wannan sai ta ji wanna mai kyau ma kuwa banza harda wani murna ya goyata kaima kuma ka kuma goyata ba tare da Anyi mata wankaba duk kun kwashi kazanta" keyarsa abubakar ya tallake yace "eh amma a haka yayi saving kanwarka kai kanacan kana haukan banza dalla can wuce muje" sannan ya kuma mikawa abdulrahman hannu yana murmushi yace "mun gode fa sosai " murmushi kawai abdulrahman ya maida masa amma bai kuma gigin sake muka masa hannuba, ganin bazai mikoba yasa abubakar dauke sannan sa sannan yace "OK sai anjima " shima abdulrahman yace "sai anjima" amira dake baya ta fara daga masa hannu yana cewa "bye bye Yaya abdulrahman" shima ya daga mata sannan suka juya suka tafi suka barshi tsaye shi kadai yana jin tamkar ya bisu.
...........................
I'm sorry jiya kunjini shiru ba lallai hannu na dinga posting kullum ba kiyi min afuwa
What do think about Amira?
Comment & vote
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
