Chapter 30

50 8 1
                                    

Gidan Mal Musa yana nan a inda suka sanshi babu abinda ya karu sai raguwa da yayi nesa ba kusaba sai daga gefe kuma an kara wasu sassan wadanda daga alama sababbine ginin bulo rufin kwano ginin ba filasta rufin ba ceiling ainahin gidan kuwa banda kara rushewa da yayi babu komai cikinsa, suna fitowa daga motar suka tsaya suna karewa gidan kallo, dan kamasho ya fito ya zagayo side din Abdulrahim yace "nanne gidan gashinan kullum sai kara lalacewa yakeyi kamar bai haifi yaya mazaba kuma 'yayansa maza uku naji ance ma akwai wasu da suka bata ba....." Abdulrahim ya katseshi ta hanyar saka hannu a aljihu ya zaro kudi ya mika masa yace "ga wannan zaka iya tafiya" dan kamasho ya karbi kudi yana kare musu kallo sannan ya fara zabga godiya kamar zaiyi masa sujjada shidai Abdulrahim ya juya yayi gaba ya barshi a wajen, a hankali ya daga dan labulen buhun dake kofar gidan ya shiga ainahin tsakar gidan Abdulrahman na binsa a baya zuciyar kowanne a cikinsu na bugawa kamar zata bar kirjinan nasu ta fito waje, tsakar gidan ba kowa har yanzu bishiyar dake wajen na nan sai dai ita kanta bishiyar kamar mai ciwo tamkar irin bishiyunnan na dajin da bukaye suke haka take ta wani tsome ta lalace, Abdulrahman ya karewa wajen kallo sannan ya fara sallama duk da babu alamar akwai mutane a gidan, gidan yayi shiru kamar makabarta sai hayaniyar yara daga sauran sassan, wata yarinya ta fito daga wani daki wanda daga dukkan alamu wajen girkine saboda bakinsa katangar ta karace wanda ko haduwa sosai baiyiba alamar dai ba kwararre ne yayi taba duk ta bungure ta huhhuje sai tsummokara aka saka aka toshe mafi yawan kofofin sannan aka lulluba mata yan tsummokara dan a kara mata kwari duk da daga dukkan alamu rani na ja za'a zare kararen danyin girki ko wani abu, wani darone a hannunta na karfe da kayan wanki a ciki da alama ma ba wai sallamar tasu ta jiyoba fitowar yin wanki tayi rafi zata, tana gama fitowa sukayi ido hudu da Abdulrahim ta dan tsorata da farko alamar batasan dasu a wajenba sai kuma ta maze sannan ta kalli Abdulrahman tana cewa "lafiya? Suwaye k..." sauran maganar ta makale a bakinta sannan ta saki daron hannunta ta maida hannayen nata ta rufe bakinta dasu tare da zaro manyan idanunta gaba daya, ko ba'a gaya musuba sunsan wannance Khadijansu Khadija kanwarsu da innarsu ta barmusu amana ba karamar kama takeyi da innarsuba tamkar tayi kaki tabbas wannan khadijace, a bangaren Khadija kuwa bawai ganesu tayiba dan ba zata iya tuna kamanninsuba bata ma sansuba sai da aka bata labarinsu, tunda aka bata labarinsu kullum tana cikin fatan dawowarsu kullum tana cikin mafarkinsu abu daya da ta sani shine ance kamarsu daya har ba'a iya banbancesu dan haka tana kallon wadannan zaratan samarin na gabanta ta kalli daya ta juya ta kalli dan uwansa sai taga kamar wancen din dai ta kuma kalla banda banbancin kalar riga babu wani abu daya banbantasu a take ta yanke cewar sune finally dai sun dawo, sune wadannan yayyen nata yayyenta guda biyu jallin jal masu kaunarta a duniya.

A hankali hawaye ya fara zarya a kumatunta, wasu hawaye masu sanyi ba masu zafi kamar yadda suka saba zubaba, wadannan hawayen farin cikine ba na bakin cikiba kamar yadda ta saba zubarwa, ta fara takawa a hankali tana cigaba da kallonsu daga wannan ta maida idonta kan wannan, dayan idonsa shima ya cika da kwalla a zuciyarta tace Abdulrahman dayan kuwa a bushe idonsa yake sai dai cike yake da kauna da farin cikin take tace Abdulrahim.

Basu bari ta karaso inda sukeba suka tareta midway a tare suka rungumeta sannan ta saki kuka a jikinsu, suka kankameta tamkar zasu tsaga jikinsu su sakata ko kuma ance musu idan suka saketa za'a kuma rabasu da ita, kuka Khadija takeyi sosai a ranta tanajin wahalarta tazo karshe yayyenta masu tare mata fada masu bata abinci a baki suyi mata wanka su shiryata sun dawo daga yau babu mai kara dukanta babu mai kuma zaginta.

Abdulrahman na rike da su Khadija da Abdulrahim yanajin duk wata damuwarsa na zagwanyewa a wajen yaji ta fara tari yasan sun yi mata rikon da zai iya hanata numfashi ishashshe dan haka ya sassauta rikon da yayi mata yana dago kanta sai dai maimakon ta dago sai ta kuma dunkulewa a wajen still hannunta akan bakinta tana cigaba da tarin, da saufi Abdulrahim ma ya saketa suka fara jera mata sannu kowa na kokarin shafa bayanta wai ko kwarewa tayi, suna haka har dai tarin ya lafa sannan ta dago jajayen idanuwanta tana kallonsu fuskarta da murmushi amma su basu maida mata murmushinba saboda abu mafi tsoratarwa da suka gani a hannunta da gefen bakinta, Abdulrahman yayi saurin dago hannunta yana duba ciki yace "Khadija menene wannan? Tun yaushe kike wannan tarin?" tayi saurin janye hannunta ta jawo wani zani cikin kayan da zataje wankewa ta goge hannun da bakinta tace "ba wani abu bane ba fa na saba babu abinda yake mun" Abdulrahim yace "ba maganar kin sababa dama can kinayi? Tun yaushe?" ta danyi shiru alamar tunani sannan tace "an dade" Abdulrahman yace "innahi wa inna ilaihir rajiun" duk suka kalleshi yace "ina mutanen gidan?" Khadija tace "ina daki baba ya bata jikinsa ina canja masa kaya ban saniba ko inna ta fita nan dai na barta da zan shiga dakin" kamar amsa ga maganarta sai ga jaru nan ta fito daga dakinta tun na da wanda ya koma tamkar wanda yayi sinking saboda nutsewar da yayi cikin tsakar gidan, tana fitowa tace "ke dije wai ke da ubanwa kike magana ne yar me da tari kamar mai ciwon sida kin debomin ruwan ko kuwa?" da sauki Khadija ta mike tana cewa "yanzu zan debo inna na canjawa baba kayansane" jaru tace "wai suwaye wadannane? Ko kwashe kwashen naki har cikin gida ya koma?" Khadija cikin farin ciki tace "inna yaya Abdulrahim ne da yaya Abdulrahman" jaru tace "su waye hakan? Ke kinga ba ruwana da ko su suwaye kizo ki debomin ruwa nace ko?" kafin Khadija ta bada amsa sule ya fito daga kewayensa a zuciye yana cewa "ina dijen take dan ubanki ina wankin da na sakaki kike tsaye anan? Ni sa'an uwarkine?" ya daga hannu da niyyar marinta da sauri Abdulrahim ya shiga tsakani sannan ya tare hannun nasa ya kuma murdeshi baya, sale ya saka ihun da ya jawo hankalin kafanin mutanen gidan gaba daya suka fito suna kallon ikon Allah, Abdulrahim ya kalli sule tun daga sama har kasa fuskarsa kamar sakon mutuwa, ya ga ya kara lalacewa ya tsofe zakayi tsammanin ya bawa hamsin baya yace "abinda dama kukeyi mata kenan? Jakace ita ko baiwa? Kai yanzu ba kunya ba tsoron Allah sai ka daga hannu ka daki wannan yar yarinyar? Gaskiya kaji kunya wallahi kai ba namiji bane babban banza kawai" ya hankadeshi gefe tare da cika hannunsa sai da sale ya kai har kasa saboda karfin hankadar, Abdulrahim ya juya yana kallon yan gidan daya bayan daya da suka fiffito sukayi tsarko tsarko suna kallon ikon Allah yace "wato gabaki dayanku hada kai kukayi kuna zalintar marainiyar Allah saboda bata da galihu bata da mai tare mata ko? Kunsan kuwa hukuncin wanda ya zalinci maraya? Ko da yake banajin zaku sani saboda gaba dayanku taron jahilaine taron tsintsiya ba shara babu abinda zaku iya saboda jahilaine suka haifeku suka kuma raineku abinda suka koya muku kawai shine cin zali, amma ku kwantar da hankalinku daga yau ta kare dama zuwa mukayi mu tafi da ita sai kuma abi wani sarkin a nemi abon Victim" yana gama fadin haka ya juya wajen Abdulrahman daga rike da Khadija yace "Abdul muje" kafin ya bashi amsa jaru ta taso da sauri "kuje ina? Wallahi babu inda zaku kaita bamusan ko ku suwayeba sai kawai kuzo ku dau yarinya babu inda zaku kaita dan su Abdulrahman din dana sani ba haka sukeba" sai ta fara kukan karya "su yarane masu tarbiyya masu yafiya basa zagi ba zasu taba dukan yayansuba ba kuma zasu taba zuwa su tafi basu tsaya sun taimaki innarsuba ko babanku baku ganiba fa me ya sameku waya canja min 'yayana?" ta cigaba da kuka harda fyatar magina da gefen zani "Allah sarki babu inda bamuje nemankuba kullum sai nayi kukan rashinku karku tafi ku barmu dan Allah ku tsaya ayi magana" Abdulrahman na shirin yin magana Abdulrahim yayi sauri ya rigashi yace "gwara ma ki maida wannan kukan munafurcin naki mu ba 'yayanki bane ba zamu taba zama 'yayankiba sannan bama bukatar zama dama ita mukazo dauka kuma ita zamu dauka mu juya" jaru tace "shikenan tunda kunce ni ba innarku bace amma ita dijen aini innartace tunda naci fitsarinta naci kashinta ai nayi mata komai, tsahon wannan shekarun ina kuke? Kunsan cinta ko shanta? Kunsan lafiyarta ko cutarta? Duk nice dan haka babu inda zaku da ita" wani kululun bakin cikine ya tsayawa Abdulrahim ya bude baki amma ya rasa abinda zaice sai kawai ya juya ya kama hannun Khadijan da niyyar fita, tirjewa Khadijan tayi ta fara kokawar kwatar hannunta ya juyo yana kallonta tace "baba! bazan iya tafiya nabar baba ba, bashi da lafiya ni kadaice nake jinyarsa ko tashi baya iyayi dan Allah karmu tafi mubarshi" hawaye ya fara bin kuncinta, jiki a sanyaye Abdulrahman yace "yana ina?" ta nuna wannan rushashshen dakin da ta fito dazu daga ciki shi kuma ya nufi dakin, bangon dakin bakikirin alamar dai da gaske da girki akeyi a ciki haka rufin baki har wani kututu kututu yayi, amma kasan maimakon mutum yaga su murhu da tukwane aa kayane daure cikin buhu sai kuma wata shamulalliyar katifar rimi da wani yamushashshen tsoho akai wanda ke jan numfashi da kyar, gaba daya jikinsa a yamushe yake sai fata kawai dan wannan ko ruwa baza'a samu a jikinsaba balle jini ko tsoka, a hankali Abdulrahman ya karasa kusa dashi ya tsugunna yace "baba?" Mal Musa ya bude ido da kyar yana kallonsa sai kuma hawaye dan ko karfin bude baki yayi magana bashi dashi, Abdulrahman yace "sannu baba Abdulrahman ne ka ganeni?" mal musa ya dan daga kai yana ci gaba da kuka Abdulrahman ya saka hannu yana goge masa hawayen fuskarsa yace "ya isa haka baba ka daina kuka yanzu zamu tafi da kai asibiti zaka samu lafiya insha Allah" Abdulrahim daya shigo yanzunnan yace "what? What do you mean? Badai mune zamu kaishi asibitinba ko?" Abdulrahman yace "mune ko akwai wani wanda ya cancanci ya kaishi asibiti bayanmu" Abdulrahim yace "gasucan 'yayan so su ya kamata su kaishi asibiti ba muba daukan Khadija ya kawomu kuma ita kadai zamu dauka, don't try to change the plan please" Abdulrahman yace "Abdulrahim karkayi haka mahaifinmune ko ka manta" Abdulrahim yace "ta yaya zan manta bayan shine mummunar kaddara ta farko a rayuwarmu" Abdulrahman ya kada kai kawai kamar zaiyi magana sai kuma ya kalli Mal Musa sannan ya juyo ya kamo hannun Abdulrahim suka fice daga dakin, suna fitowa tsakar gida yan gulmar da suka taru a kofar dakin suka watse suka basu hanya Abdulrahman bai kulasuba yaja Abdulrahim har kofar gidan jikin motar da sukazo da ita suka tsaya, Abdulrahman yace "Abdul kar muyi haka da kai banason mutane suji muna musu banason irin kuma maganganun da kake fada a gaban Baba da Khadija, baba yana bukatar mu bashi da lafiya kana ganinsa ko kai da ba field dinkaba kasan yana bukatar kulawa ta gaggawa balleni sannan Khadija da alamu na ciwo a zuciyarta karmu dinga maganar da zata bata mata rai har sai mun fahimci menene yake damunta" Abdulrahim ya katseshi da cewa "wai tsaya duk ba wannan dogon bayaninba ni kawai abinda nace shine bazamuje ko ina da Mal Musa ba Khadija kawai mukazo dauka ita kawai zamu dauka, su 'yayan da yakeso din me yasa basu saka masa soyayyar da yayi musu sun kula dashiba? Mu bar musu ubansu zasu san yadda zasuyi dashi" Abdulrahman yace "kaima ubankane nima haka ba nasu su kadaiba Abdul babu ruwan ubangiji da me baba yayi mana hukuncinmu daban nashi daban saboda littafinmu daban da nashi, ka manta cewar ubangiji zai iya hukuntamu hukunci mai tsanani idan muka tafi muka barshi a halin da yake yanzu? Mu tafi dashi mu kula dashi idan ya warke sai mu dawo musu da kayansu" Abdulrahim yace "mu kuma fa? Amfaninmu kenan muzo muyi jinyarsa?" Abdulrahman yace "mu kuma sai mu jira hukuncin ubangiji shi yasan abinda akayi mana ya kuma san me mukayi" Abdulrahim yama rasa abinda zaice kawai ya juya ya kifa kansa saman mota yana ajiyar zuciya, ya tsani Mal Musa ada yayi tunanin komai ya wuce amma zuwansa yasa ya fahimci lafawa yayi babu abinda ya wuce har sautin digar jinin innarsa daga kan gadonta zuwa kasa yakeji a kunnensa yana kallon fuskarta cikin idonsa irin zafin jiki dana zuciyar da takeji alokacin maganganun da mal musa ya fada mata gaba daya suna dawowa cikin kansa fresh.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora