Aisha 👆
A gajiye sosai Amira ta shiga gida dan daga asibiti wajen Khadija makaranta ta wuce danma test zasuyi da ba zatajeba a yadda taga wannan jikin na Khadija, tana shiga falo tayi sallama gidan shiru kamar babu kowa har ta kama handle din kofar dakinta zata shiga taji momy tayi kiran sunanta, ahankali ta juya momyn na tsaye kofar kitchen da faranti a hannunta Amira batasan ko menene a cikiba ta juyo tana dan murmushin wahala tace "momy barka da gida na dawo" momy ta kalleta fuska a yatsine tace "daga ina kike?" itama Amira ta dan yamutsa fuska cikin confusion tace "momy makaranta mana" momy tace "to muje yayanki ba lafiya ki dubashi" da sauri Amira ta saki handle din da har yanzu yake hannunta tace "wanene ba lafiya me ya sameshi?" ba tare da momyn ta bata amsaba kawai ta dau hanyar dakin su Usman din, Amira ta rufa mata baya gabanta na faduwa tana tunanin wanene ba lafiya kuma me ya sameshi? suna shiga ta kalli inda gadon Usman yake yana kwance da sauri ta karasa gabansa tana kare mai kallo tace "subhanallahi yaya Usman menene ya faru da fuskarka haka?" ta tsugunna a gabansa momy kuma ta zauna gefen gadon tace "ga tea din tashi kasha" da kyar ya mike sai da Amira ta taimaka masa saboda tsamin da jikinsa ya kuma yi ya zauna sosai ya karbi tea din daga hannun momy Amira ta kuma cewa "wai dan Allah menene ya faru da kai accident kayi?" Usman ya harareta momy kuma tace "wanda kika fifita akan yan uwanki na jini wanda kikafi so sama da mu shine yayi masa haka" Amira ta sake yamutsa fuska tace "wa kenan momy" momy ta harareta tace cikin daga murya "wa kenan kuwa banda ubanki Abdulrahman" Amira ta kalli momy ta juya ta kalli Usman ta sake kallon momy sannan tace "yaya Abdulrahman dai?" sai kuma tayi yar dariya tana cewa "yaya Abdulrahman din da ko yatsa ka saka masa baya cizawa shine zaiyi wannan aikin?" Usman yace "ai bashi kadai bane duk su ukunne shi da Abdulrahim da Bello" Amira ta sake kallonsa ta kalli momy sannan tace "wallahi karyane" bata gama rufe bakintaba momy ta sauke mata kyakykyawan mari a kuncinta tace "wanene yake karyar ni ko Usman din? Eyeh nace waye sa'an wasanki da zaiyi miki karya tsakaninmu ko kuwa rubutun da yayi ya gama shanyekine har yasa kin daina banbance uwar da ta kawoki duniya da dan uwanki? Gashinan ke kina nan kina wulakanta yan uwanki akan bare su kuwa kalli dukan da suka hadu sukayi masa akan tasu kanwar kawai saboda yace yana sonta saboda su sunsan muhimmanci dan uwa ba kamar ki ba, kaima Allah ya kara duk yawan yan matan dake garinnan ka rasa wacce zakaso sai wannan yar kauyen na kuma ganinta a gidannan shegiya mai ido irin na aljanu" Amira wadda hawaye ya wankewa fuska tace "momy dan Allah kiyi hakuri ni ba nufina kinyi karyaba amma momy su yaya Abdulrahman ma fa suna asibiti kan khadijan wacce ke kwance rai a hannun Allah wallahi bakiga halin da take cikiba momy ta ina zasu samu time din tsayawa dukan yaya Usman?" momy tace "to shine kenan yayi miki karyar?" kai kawai Amira ta kama kadawa sannan ta sunkuyar da kai dan tasan momy ba zata taba saurarontaba, mutane da yawa na ganin kamar itace yar gaban goshin momy saboda irin son 'ya mace da ta nuna da kasancewarta mace kuma auta amma duk wanda ya kwana ya tashi a gidannan yasan momy tafison Usman basu kuma san daliliba ita dai tana ganin ko dan yafi kowa fitinane? sannan halinsu yafi zuwa dayane? A hankali ta kuma kallon Usman tace "to yaya Usman me kayi musu sukayi maka haka? Nasan ba zaku taba dukanka hakanan ba tare da kayi musu wani babban laifiba" Usman ya harareta kamar idonsa zai fado yace "shi dalilin da momy ta gaya miki baiyi mikiba wani kikeso?" Amira tace "amma yaya Usman watanku nawa tare da Khadija? Duk tsahon wannan watannin basu taba dukanka akan ka kula musu kanwaba sai yanzu?" wata muguwar harara ya watsa mata kawai ya cigaba da shan tea dinsa ita kuma momy tace "to shikenan Amira tunda masoyinki baya laifi ai shikenan munyi masa karya amma ki sanar dashi nace yadda ya dokarmin d'a akan kanwarsa wallahi ya cire rai da samun tasa kanwar gwarama yaje can wani waje ya nemi matar da zai aura badai kanwar Usman ba" ido Amira ta zazzaro ta bude baki gaba daya kwakwalwarta ma ta kasa processing abinda ya kamata ta gayawa momyn sai da ta dau kusan minti guda tana kallonta baki bude amma sauti yaki fita sannan tace "momy me kike nufi? No momy ba ruwan fadansu da soyayyarmu momy ni ban yadda da saka hannun yaya Abdulrahman ba kwata kwata momy dan Allah ki zanye wannan maganar" kallonta kawai momyn tayi tace "tashi ki fice ki bani waje tun kafin ranki ya baci" Amira ta rike kafar momy maimakon ta fice din kamar yadda akace mata ta fara kuka tana cewa "momy please kar muyi haka wallahi babu ruwan yaya Abdulrahman na sani zan iya dafa alqur'ani akan ko dan yatsansa bai tababa momy kiyi bincike wallahi basu suka dakeshiba" Usman ya mike a zuciye ya nunata da yatsa "wai ke dan ubanki ni sa'an wasankine da zaki dinga karyatani? Ina harka da yan daba ne ko kuwa me kikeso kice sannan kema kinsan da ace mutum dayane da sai dai mu daki juna ko Abdulrahim dinne da kike ganinsa a mummurde bai isa yayimin wannan dukanba hadarmun sukayi su uku" momy tace "kajiba dama can niyyar kasheka sukasoyi banda haka tayaya zasu hadar maka su uku kai kadai?" Amira ta jijjiga kafar momy tace "momy please ki kalleni momy ni zanyi bincike akan maganar wallahi babu ruwan yaya Abdulrahman momy karkice na rabu dashi shine farin cikina bazan iya rayuwa babushiba" momy ta mike tsaye ta kalli Amira wadda har yanzu ke tsugunne a kasa fuskarta emotionless tace "then sai ki mutu ai ba ke kadai na haifaba tunda dan shi kike rayuwa" tana gama fada tayi waje ta bar yarinyar wadda gaba daya kukan ya dauke da kansa kamar anyi ruwa an dauke hatta numfashinta a hankali yake fita saboda tsoratar da maganar momyn tayi mata.
ESTÁS LEYENDO
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Novela JuvenilLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
