Chapter 25

73 10 3
                                        

Tun ranar da prof ya bawa su Abdul labarinsa da kuma kasancewar Bello dansa tun ranar Bello ke kulle a cikin daki yaki kula kowa ya kuma ki yiwa kowa Magana, babu yadda su Abdul basuyiba dan ya saki jiki amma hakan yaki yiyuwa idan sunyi masa Magana ma eh ko aa shine kawai amsarsa idan ya ga doguwar amsa suke bukata sai yayi musu shiru har sai sun gaji sun kyaleshi, Amira ta tattaro kayanta ta dawo gidan prof tace tunda su bazasu koma gidan dadyba kuma ba zasu dinga zuwaba saboda Bello to ita gwara ta taho wajensu ba zata koma gidaba har sai sun tafi.

Tunda sukazo basuje ko inaba saboda ba zasu iya fita su barshiba shi kuma yaki zuwa ko ina, dakinma sun baro nasu dakunan sun dawo dakinsa tare suke kwana, intentionally sai wannan ya dora masa kafa wancan ya kama munshari amma har su gaji suyi baccin gaske bazai ce uffanba. Abin yana matukar damunsu babban abinda suke bukata shine ya bude baki yayi magana, yayi kuka ko masifa koma menene amma yaki ya zama kamar wani gawa ko mai paralyze.

Mahaifiyarsa babu irin lallashi da kukan da batayiba, kullum sai tazo ta rokeshi akan yayi mata magana ko zataji dadi amma sam yaki haka zata gaji ta koma cikin gida, kullum tana cikin yi masa girke girke duk dan ta samu ya saki jiki amma tunda suka dawo tea ne kawai abincinsa shima sai yaga ransu Abdulrahim ya baci sannan yake sha.

A haka har sukayi sati da zuwa kuma dama sati uku sukayi niyyaryi, wata rana suka addabi rayuwarsa akan dole sai ya fito waje ya sha iska dan ko waje baya fitowa, da kyar ya biyosu suka shiga garden din gidan suna hira duk da bawai dashi suke hirarba amma yafi babu, suna zaune Amira ta shigo wajen da tire a hannunta da yan kanana plates a kan tiren, ta fara ajiyewa kowa a gabansa tana cewa "sponge cake hajiya ta koyamin kuci kuji idan yayi dadi?" Abdulrahman ya saka cokalin dake cikin plate din ya gutsira ya kai baki duk idonsu a kansa sai ya fara murmushi ya kalli Amira da tayi tsuru tsuru yayi mata alamar thump up da hannunsa, numfashin da batama san tana rikewaba ta saki sannan ta kalli Abdulrahim tace "saura kai" shima ya saka a baki nan da nan ya yamutsa fuska ya tofar yana kakarin amai
Fuskar Amira kamar zatayi kuka tace "baiyi dadiba ko?" Abdulrahman yace "Abdul bana son sharri" shima yace "abinda nakeson gaya maka kenan, zaka saka tayi tunanin yayi dadi wannan idan baki nayi ta kawo musu wannan abin ai bazan kuma fita wajeba dan kunya" tace "dan Allah ku gayamin yayi ko baiyiba waye yake fadin gaskiya waye yake tsokanata?" Abdulrahman yace "yayi dadi" yayin da Abdulrahim yace "baiyi dadiba ko kadan" a tare sukayi maganar sai kuma suka kama dariya ita kuma ta zumburo baki tace "yaya Bello nasan kai zaka gayamin gaskiya ci dan Allah kaji" ya tsaya yana kallonta ta kuma marairaice murya tare da langabe kai tace "please?" dole ya dan gutsira ya kai bakinsa su kuma gaba daya suka zuba masa ido suna jiran amsa amma mai makon ya bude baki yayi magana kawai sai hawaye.

Kai Amira ta kifa akan table din dake tsakaninsu Abdulrahim kuma ya fara kokarin rike dariya sai da yaga da gaske kuka Bello yakeyi sannan ya koma serious, ganin sun kura masa ido sai ya mike da sauri ya juya musu baya yayi dan tafiya kadan sannan ya tsugunna a wajen ya saka kansa tsakanin kafafunsa ya cigaba da kukansa har da sheshsheka, Abdulrahman ya mike zai bishi Abdulrahim ya yi saurin rike hamnnunsa yace "ka kyaleshi"
Daga wannan kukan da Bello yayi sai kuma ya dan ware bayan sun dawo daki har da dan taba hira sannan ya wuce yaje ya kwanta, su kuma waje suka koma sukayi ta hira da Amira sukayi ta musu akan cake din dazu sai daga baya Abdulrahim yace wasa yake mata "so kawai nake naga hawayenki dan babu abinda kika iya irinsa nasan dan karamin wasa ya isa ya sakaki kuka shiyasa" sai da dare yayi sannan hajiya ta kirawota tace ta dawo gida haka dare yayi, su kuma suka koma part dinsu kowa yayi dakinsa, bayan Abdulrahman ya gama abinda zaiyi ya kwanta sai ga Abdulrahim nan ya tsaya a bakin kofa yana kallonsa, Abdulrahman yace "ya dai?" Abdulrahim yace "anan zaka kwana?" Abdulrahman yace "eh" Abdulrahim yace yana karasa shigowa dakin "nima anan zan kwana dan ba zaka barni daga ni sai Belloba idan ya cigaba da kukan bansan me zance masaba" ya nemi waje ya zauna a bakin gadon duk sukayi shiru sai can yace "wai Abdul tsaya Bello zamu dingace masa ko Abdulmalik?" Abdulrahman yace "wannan decision ne nashi da iyayensa duk abinda suka zaba shi zamu cigaba da gaya masa whether Bello or Abdulmalik" Abdulrahim yace "Allah dai ya sa su barmasa Bellonsa, kowa yafi sabo da Bello kuma takardunsa duk shine a jiki sannan idan aka canja masa sai mutane sun fi tambayar abinda ya faru beside Abduls din zasuyi mana yawa" Abdulrahman ya kwanta yana cewa "lallai kana da reasons da yawa but unfortunately it's not your call to make" Abdulrahim ya tafi da baya ya fada kan gadon yana cewa "whatever".

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Des histoires addictives. Découvrez maintenant