Chapter 40

14 0 0
                                    

Washe gari da sassafe suka fara shirin tafiya zamfara harda Bello za'a tafi suna fitowa daga masallaci yayi knocking kofar dakin Khadija tazo ta bude masa da katon hijabi a jikinta da alama itama yanzu ta idar da sallar Bello yayi mata murmushi itama ta maida masa sannan ta sunkuya ta gaisheshi ya amsa fuskarsa kamar babu wani abu daya faru jiya yace "karfa ki koma bacci kiyi sauri ki shirya kinsan da wuri zamu tafi" Khadija ta daga kai kawai har ya juya sai kuma ya dawo ya kalleta yace "me ya sami idonki?" nan da nan hawaye ya kuma ciko idonta ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannun hijab din jikinta, Bello yayi ajiyar zuciya yace "badai kwana kikayi kina kukaba?" hawayen ta ya zubo ta saka hannu tana gogewa yace "oh my God daga magana sai kuka? Dan Allah ya isa haka goge hawayen kar ki kuma yin kuka kinji ko? Maza kije yanzu ki shirya karki makara kar fa ki kuma yin kuka kinji ko?" ta kada masa kai yace "yauwa to share hawayen na gani" ta saka hannaye biyu tana sharewa ya kuma cewa "yauwa my love yi murmushi na gani" ta fara dariya tana rufe fuskarta shima yayi murmushin yace "yauwa kokefa maza jeki ki shirya" ta juya ciki shi kuma ya koma kitchen ya fara hada musu breakfast, wajejen 7am Abdulrahman ya sauko da jakarsa a kafada yayi knocking dakin Khadija ta amsa sannan ya shiga tana kan stool din gaban mirror ta gama saka kaya tana daura dan kwali tana ganinsa tayi zumbir ta mike tsaye take jikinta ya fara rawa amma ga mamakinta sai taga ya saki murmushi yace "wow lallai Amira aikinta na kyau da kanki kikayi wannan kwalliyar?" jiki a sanyaye ta daga kai yace "gaskiya kinyi kyau bari na daukeki hoto na turawa Abdul" ya zaro wayarsa ya fara daukanta pics sai kuma ya danyi frowning yana kallon wayar yace "hotonma baiyi kyauba kin wani hade rai kina zare ido kiyi murmushi mana" ba shiri ta fara murmushin tana sunkuyar da kai yace "yauwa that's my sister koke fa" sai daya gama yace "ina jakarki da fatan kin dauki duk abinda zakiyi amfani dashi" ta daga kai ya kuma hade rai yace "wai ciwon baki kikeyine?" da sauri ta girgiza kai ya tsaya yana kallonta sai kuma tace "a'a" yayi 'yar dariya yace "koke fa ina jakar?" ta nuna masa jakar da ta saka kayanta kala biyu kawai a kan gado ya saka hannu ya dauka ya rataya a kafada sannan ya fita yana cewa "kiyi sauri fa ga abinci can Bello ya hada kizo muci mu tafi" ta biyo bayansa tana cewa "ai nama gama"
A wajen cin abincin ma haka sukayi ta janta ita kuma ta kasa sakin jiki gani takeyi kamar har yanzu Abdulrahman fushi yakeyi da ita dukanta zaiyi, karfe 8 suka dau hanya harda guzurinsu na snacks da lemuka wai zasu iya jin yunwa a hanya, Abdulrahman ne mai driving sai Bello a gaba baya kuma Khadija da mal musa, tunda suka taho ake kiranta a waya gashi bata iya saka wayar a silent ba sai data gaji kawai ana sake kiranta tayi rejecting zata kashe Abdulrahman ya miko mata hannu "ban wayar" ba musu ta mika masa a daidai lokacin da ake sake kira a take Abdulrahman ya dauki wayar ya saka a kunnansa Usman da baisan wayeba ya fara magana "kubra my God me yasa ina ta kiranki ba zaki daukaba? Are you ok? Ina fatan babu abinda sukayi miki" Abdulrahman yace "bata taba gaya maka sunanta Khadija kubra sunan innarta bane?" Usman ya danyi jimm sai kuma yace "Abdulrahim? Ina take bata wayar" Abdulrahman yace "eh to zaka iya zuro hannu ka shakeni maybe idan naji ina shirin bakuntar lahira sai na bata wayar sannan kuma ba Abdulrahim bane Abdulrahman ne, marin da Bello yayi maka jiya bai gamsar dakaiba kenan ko? Ka shiga hankalinka Usman ina ganin tsananin mutunci dady banason ko gabansa ya fadi balle ransa ya baci dan haka ka kama kanka wallahi idan ka kuma ko kallon kanwata sai naci mutuncinka duk da i doubt idan kana da mutuncin sakarai kawai" yana gama fadin haka ya kashe wayar ya ajiyeta yana faman kwafa, Mal Musa yana daga baya yace "Abdulrahman nasan duk abinda zakayi akan kanwarka ba zakayi abinda zai cutar da itaba amma dai shawarace a dinga hakuri a kuma dinga duba abinda zaije yazo Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" duk suka amsa da ameen kawai banda Khadija da ta kuma dunkulewa a waje daya tana sharar hawaye, juyowa Bello yayi ya ganta tana hawaye kawai ya tsaya yana kallonta wani irin zafi yakeji zuciyarsa tanayi masa ya tsani ya ganta bata murmushi balle kuma yaga zubar hawayenta a hankali ta dago fuska suka hada ido sai kawai yayi mata murmushi sannan ya mata nuni da ta goge hawayenta jiki a sanyaye tayi abinda yace sai kuma ya sake mata nuni da tayi murmushi da hannunsa sai da yaga tayi murmushin sannan ya juya shima yana tayata Abdulrahman ya kalleshi kawai yayi tsaki tare da dauke kai ya maida kan tukin da yakeyi.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon