Chapter 45

66 11 0
                                        

Gaba dayansu sakin baki sukayi suna kallonsa cikin rashin fahimta shi kuma ya karasa kan kujera gefen Aisha ya zauna tare da sake saka fuskarsa cikin tafin hannunsa gwuiwar hannunsa kan ta kafarsa yana dan tapping kafar tasa a kasa a hankali cikin tashin hankali, a hankali Abdulrahim ya tako zuwa hannun kujerar ya zauna ya dafa kafadarsa yace "Abdul gayamana menene yake faruwa me ya faru a gidan dadyn?" Abdulrahman ya dago kansa ya kalli dan uwansa da idanuwansa da sukayi jajur kamar mai ciwon apolo yace "momy ta rantse indai tana raye bazan auri Amiraba" nan da nan gaba dayansu tashin hankali ya fito karara a fuskokinsu Bello yace "amma me yasa? Laifin me kayi mata?" Abdulrahman yace "tace tunda na daki Usman akan kanwata shima bazan samu tasa kanwarba" da sauri Bello yace "baka gaya mata abinda nata dan yayiba? Baka gaya mata ba kai ka dakeshiba?" Abdulrahman yace "zata saurareni kenan ma, ni yanzu babban tashin hankalina halin da Amira take ciki Bello baka ga yadda yarinyar ta koma daga jiya zuwa yau ba gaba daya kamar wadda ta shekara tana ciwo tayi wani irin baki ta rame kuma Allah kadai yasan abinda ya saka ta koma hakan Allah kadai yasan me sukeyi mata a gidan, yanzu ma dana baro gidan momyn ta saka ta a daki ta kulle da makulli ina tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo ina tsoron abinda zai iya samun Amira ita kadai a cikin wannan dakin" Abdulrahim da tun dazu yake bin dan uwansa da kallo ya mike a zuciye ya fara pacing cikin dakin yana fadin "is she mad? Ta manta halin da yarinyar take ciki da zata kulleta a cikin daki bayan ta bata mata rai? Momy tanaso Amira ta mutune ko me?" kowa dai yayi shiru Aisha ta dan kalli Abdulrahim tace "habibiy calm down please " ya kalleta naturally kuma sai ya danyi relaxing saboda kallon idonta kawai ta cigaba "tana da wani ciwone?" a hankali kamar mai rada yace "sau biyu anayi mata aikin zuciya, tun da aka haifeta bata da lafiya" a tare Aisha da Khadija suka waro idanuwa waje Khadija tace "innalillahi wa inna ilaihi rajiun yanzu ya zamuyi? Yaya Abdulrahman I'm so sorry duk laifinane da ban kula yaya Usman ba da duk haka bata faruba" ta gefen ido Abdulrahman ya kalleta yace "karma ki fara wannan maganar ba laifin kowa bane kaf wajennan haka kaddararmu take idan ma akwai mai laifi jaruce" Khadija tace "jaru kuma?" Abdulrahman yace "eh da bata dauke hankalin baba daga kanmu ya daukomu ya kawo almajirciba da duk haka bata faruba kasancewarmu almajirai shine babban aibinmu shine dalilin da yasa momy bata sanmu shine dalilin da yasa Usman baya sonmu" Abdulrahim ya danyi wata dariya yace "then? Seriously Abdul? A wannan situation zaka fara neman someone to blame kuma someone dinma jaru? Come on! we have to do something about Amira ba tunanin waye mai laifiba, kuma da kake maganar dan an kawomu almajirancine da ba'a kawomunba zakasan Amiran" Abdulrahman yace "to Abdul fadi me kakeso ayi yanzu?" Bello yace "why not mu kira dady mu gaya masa bawai maganar aurenba wannan ba yanzuba amma mu sanar dashi kulletan da akayi komai fa zai iya faruwa" Abdulrahman yace "idan muka gayawa dady tamkar mun kai karar momyne wajensa kasan halinsa akan Amira babu wanda bazai iya batawa raiba, wannan kuma zai kara tunzuratane kawai" Abdulrahim ya zaro wayarsa a aljihu ya fara dialing Abdulrahman yace "Abdul kar fa ka kira dady nace" Abdulrahim yace "ba dady nake kiraba Abubakar nake kira"
Ana daukar wayar Abdulrahim yace "assalamu alaikum yaya Abubakar barka da rana" daga can bangaren Abubakar yace "ahh Abdulrahim ashe ka dawo" Abdulrahim yace "eh wallahi na dawo ya iyali" Abubakar yace "alhamdulillah ya wasannin naku" Abdulrahim yace "alhamdulillah yaya Abubakar wata alfarma nake nema dan Allah" Abubakar yace "to ina jinka" Abdulrahim yace "wallahi wasu yan matsaloline suka faru tsakaninmu da Usman har muka dan dakeshi labarin dai da nisa yanzu dai abinda nake rokonka momyce tayi fishi har tayi rantsuwar indai tana raye Abdulrahman ba zai auri Amira ba sannan ta kulle Amiran a daki muna kuma tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo kasan dai halin da take ciki to shine nace ko zaka lallaba momyn ta bude kofar ku dawo da Amiran cikin mutane kafin koma menene daga baya ayishi" Abubakar yace "subhanallahi menene yayi zafi har haka? Banda abin momy yanzu idan wani abu ya samu yarinyar ba tafi kowa asaraba? Bari kaga zanje gidan yanzu insha Allah babu abinda zai sameta da iznin Allah an bata mata rai kuma an kulleta a daki kai momy" Abdulrahim yace "wallahi muma dai abinda muke ta tsoro kenan indai tana lafiya kowanne hukuncine sai ayi mana daga baya zamu dauka" Abubakar yace "banda abin momy ma ku ba yaraba ai tasan ba zaku daki Usman hakanan ba dole wani abu yayi babba, tun da kuna yara duk abinda yake muku baku dakeshiba sai yanzu? Allah dai ya sauwake bari naje gidan" Abdulrahim yace "yauwa godiya muke duk yadda kukayi mayi waya" sukayi sallama Abdulrahim ya kashe wayar yana kallon yadda gaba daya dakin suka zuba masa ido yace "Abubakar zaije gidan yanzu"
Daganan kowa yayi shiru kamar babu wata halitta a dakin, babu abinda kakeji sai karar ac da ajiyar zuciyarsu akai akai, jimawa kadan Khadija ta katse shirun ta hanyar cewa "yaya?" duk su ukun suka dago suka kalleta dan basusan da wanda takeba, itama kawai sai ta cigaba da maganar ga duk su ukun "ina ganin me zai hana a shigar da iyaye maganarku kai da anty Amira? Ina nufin iyayenka su nema maka aurenta kamar indai dady ya riga da ya bayar ai shikenan an gama magana ko?" Abdulrahman ya girgiza kai "i don't think so" tace "ok idan ma ba hakaba kaga sai asan da gaske ne maganar asan abinda za'ayi akanta dan dai no matter what babu batun hakura gwara ma ko me za'ayi ayishi da wuri" Abdulrahman ya kalli Abdulrahim suka juya suna kallon Bello a tare shi kuma ya dan jinjina kai alamar ya yadda da abinda Khadijan ta fada kafin Abdulrahman din ya bude baki yayi magana Abdulrahim ya kuma dauko waya yayi dialing Abdulrahman ya kalleshi "wa kuma kake kira? Kai Abdul kai me yasa baka bari a yanke shawarane?" daga cikin wayar wanda ya kira ya daga "assalamu alaikum dan baba?" Abdulrahim ya dagawa Abdulrahman kafada sannan ya amsa maganar da mal musa keyi masa "wa alaika salam baba ina wuni" Mal musa ya amsa muryarsa cike da tsoro yace "lafiya kalau Allah yasa ba jikin khadijan bane?" Abdulrahim yayi saurin girgiza kai kamar mal musan yana gabansa yace "ko daya baba jikinta da sauki gatanan ma a zaune ana hira da ita" mal misa yayi ajiyar zuciyar yace "alhamdulillah wallahi gaba daya hankalina a tashe yake tun shekaran jiyan gobe insha Allah zan taho gwara nazo na ganta da idanuna" Abdulrahim ya danyi dariya yace "Allah ya kaimu goben ya kawoku lafiya" mal musa yace "ameen" Abdulrahim yace "yauwa baba dama wata maganace zamu danyi" mal musa ya kuma nutsuwa yace "ina jinka Abdulrahim" Abdulrahim ya cigaba "akan maganar su Amirane mu ke cewa yaushe kake ganin ya dace aje wajen iyayen nasu dama cewa mukayi sai na dawo kuma na dawo din" Mal Musa yace "Alhamdulillah kai amma naji dadin wannan maganar ai mai saukine ko goben idan zan taho sai na taho da Mal sadi da Mal labaran kaga sai mu kwana biyu jibi sai muje ko ya kake gani? Ina fatan ba zasuga kamar anyi musu tutsiye ba" Abdulrahim ya danyi shiru yana tunani can yace "eh to banajin dady tunda shi dama yayi ritaya ba matsala sai dai abban Aisha kasan shi yanayin nasa aikin amma dai zamu sanar dasu sai muji yadda za'ayi ku taho din kawai" baba yace "shikenan ba matsala insha Allah muna nan tafe gobe insha Allah" abdulrahim yace "Allah ya kaimu ga khadijan kaji muryarta tunda yau da sauki tana ta magana" sannan ya mikawa Khadija wayar ya juya yana kallon Aisha yace "habibatiy ya kike gani zuwa jibi zamu iya samun abbanki a gida?" ta danyi shiru tana tunani sannan tace "gaskiya ban saniba" yace "to yanzu dai idan kin koma ki dan tambayar manashi jibi su baba zasuzo insha Allah indai yana gidan idan bayanan ma ba matsala zasu iya bari sai Thursday har Friday ma defending on sanda suka ganshi" ta dan mirgina kai kadan tace "sai dai na gayawa mama ta gaya masa" Bello ne ya fara yi mata dariya yana dage gira daya yace "kunya?" ta dan kalleshi sai kuma tayi sauri ta rufe fuska da tafin hannayenta tana dariya.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Stories to obsess over. Discover now