Chapter 21

47 9 0
                                    

Washe gari da sassafe suka baro Abuja, suna zuwa ramuwar bacci suka fara dan sai dare sannan zasuje gidan gwamnati dan haka suka kwanta sukayi baccci har la'asar sannan suka yi wanka suka fita neman kayan sakawa dan zuwa gidan gwamnati sai da kayan yan gayu, wani hadadden boutique suka shiga na yan gayu suka nemi kaya masu kyau Abdulrahim wasu kaya ya dauka masu kyau sosai dan da ya saka a cikin shagon sai ya koma tamkar anyi transforming dinsane, tamkar ba Abdulrahim ba tamkar wani dan hamshakan masu kudi, tamkar wani hamshakin mai kudi, tamkar wanda yakare rayuwarsa cikin daula gaba dayan rayuwarsa tamkar bai taba sanin wani abuba waishi yunwa balle almajiranta, Abdulrahman na ganinsa kawai ya saki baki yana kallonsa bai ma san hawaye na bin fuskarsaba sai da Abdulrahim din ya goge masa yana cewa “bansan da yadda kake rarrashin Amiraba idan kaima kana wannan koke-koken  bansan wanda zai dinga rarrashin waniba kai ko ita ko yaran da zaku Haifa” da sauri Abdulrahman ya doke masa hannu “dalla can ya isheka na gaya maka banaso Amira kanwatace karma ka bari taji kuma ai bana kukan a gabanta sai a gabanka idan ma kace mata ina kuka karyataka zatayi” Bello ya leko ta bayansu yace “ohhh kanwako? Muma ai kanwarmuce ko Abdul” sai kuma suka kwashe da dariya a tare suka bar Abdulrahman na kallonsu kamar wani dolo, haushi yaji ya juya zai bar musu shagon gaba daya suka rikoshi da sauri suna bashi hakuri amma still da dariya a fuskarsu da yaga mahaukaci sukeson maidashi kawai sai ya wuce ya barsu a wajen, Abdulrahman ma da Bello sun dau kaya masu kyau tunda ance kowa zai iya gayyatar yan uwansa.

Bayan sallar magriba sukayi wanka suka shirya 8pm za’a fara program din dan haka 8pm din a kofar gidan gwamnati tayi musu, Abdulrahman, Abdulrahim, Bello, dady, Abubakar da Umar babu yadda basuyi da Usman ya biyosuba amma ya tubure yace wallahi yafi karfin almajiri ya gayyaceshi wani waje bazaijeba, Aliyu kuma baya gari yaje gidan anty zulai da yake dama shi dan gidantane, momy ma ta goyi bayan danta dan har yanzu ba wani sakin jiki takeyi da yaranba musamman da suka zama sanadin rabata da ‘yarta sai ta kara jin haushinsu ta kuma sake janye jiki dasu.

Bayan sun shiga cikin hall din da aka tanada dan taron nan yan jarida sukayo kansu suna faman daukan hotuna sannan suka janye Abdulrahim din suka lillibeshi da tambayoyi, wani usher yazo wajen su dady sannan ya jagorancesu zuwa table dinsu ashe gaba daya players din kowa da table din da aka tanada musamman dan yan uwansa sannan kowa da waiter guda daya wanda zaiyi attending dinsu su kadai ba tare da ya raba attention dinsa da wasu ba, suna zama aka cika musu gabansu da kawan tabawa kafin a fara taro.

8:30pm aka fara gabatar da taron bayan shigowar mai girma gwamna da ‘yan malisarsa gefe ga manya manyan yan wasan kwallon kafa na kano da wasu ma daga sauran makotan jahohi wadanda sukazo domin taya yan uwansu kanawa murna, ga kwamishinoni na ilimi na wasanni na matasa da sauransu.
An fara da bude taro da addu’a daga wani babban malami sannan aka fara jawabai na nuna farin ciki da nasarar da kano ta samu da jinjinawa yan wasan a bisa namijin kokarin da sukayi dan babu wanda yayi tsammanin zasuci nasara idan akayi la’akayi da irin kwarewar opponents din nasu, yan arewa bamu bawa wasanni muhimmanci ba kamar yadda yan kudu suka bayar dan haka babu wanda yayi tsammanin wannan wasan sada zumunci da gwannatin tarayya ta hada wai wata jaha daga arewace zataci balle kuma ayi tsammanin kano ce wannan jahar.

Anyi jawabai bayan jawabai daga bakuna mabanbanta anyi addu’o’I sosai ga yan wasan  sannan mc ya kira mai girma gwamna domin ya yi nasa jawabin tare da gabatar da irin kyaututtukan da jahar kano zata gabatar ga yan wasanta, bayan mai girma gwamna ya tashi ya yi dogon jawabi sosai a bisa girma da wannan wasa ya jawowa kano a idon kasa baki daya ta fannin harkar wasanni sannan ya cigaba da cewa “da gaskene kano bamu taba tsammanin zamu sami nasara akan wannan wasanba duk da bamu cire rai ba domin mun yadda da yan wasan da muka tura sannan kuma mun yadda da irin horo da kuma kwarewar da suka samu, al’ummar kano na cikin matukar farin ciki domin duk tashar da ka bude maganar da akeyi kenan haka social media haka idan ka fita cikin mutane maganar kenan team kano team kano wai wayema Abdulrahim ne?” ya tambaya yana kallon side din da yan wasan suke nervously Abdul ya mike tsaye mai girma gwanna ya cigaba “karfa kuce kishi nake yadda ake kiran sunansa cikin kwanakinnan a jihar kano ko sunan gwamna banajin ana kira” gaba daya wajen aka kwashe da dariya shima Abdul yayi murmushi yana komawa ya zauna, bayan an natsa mai girma gwanma ya cigaba “akwai matasa da yawa irin wadannan wadanda gasunan dai zaka gansu cikin unguwa tamkar ordinary yara amma bakasa talent dinsuba sai ka gwadasu, kuma wannanne yana daya daga cikin abinda gwannatinmu da ku iyaye mukeson mu hada karfi da karfe muyi aiki a kansa mu zakulo irinsu muyi encouraging dinsu mu mori baiwar da Allah ya basu a bisa hakane gwamnatin kano ta shirya kyaututuka na alfarma ga wadannan yan wasa domin mu tunzuro sauran matasa suma su tashi su nunawa duniya baiwarsu, gwamnatin tarayya ta riga da ta basu scholarship wanda munso ace mu muka dauki dauyin karatun dalibanmu amma duk da haka muna godiya da gwamnatin tarayyar ta dauka duk dayane as long as sunyi karatun, dan haka gwamnatin kano zata bada kyauta ta kudi naira million….. ga kowannensu da motoci sababbi kirar ….. sababbi shima ko kowanne daya daga cikinsu za kuma mu basu abinda muka sakawa suna lucky card, kowa guda uku uku kunsan me zasuyi da lucky card dinnan?” kowa ya kada kai aa sannan ya cigaba “zasuyi amfani dashine a lokacin da suke tsananin bukatar gwamnati tayi musu wani abu tamkar alfarmace gwamnati ta yadda koda ternua dinmu ta kare suna zuwa da lucky card dinsu just consider it done ko meye, sannan abu na karshe shine gwamnatin kano ta daukesu aiki daga yanzu sun zama official players na jihar kano zasu cigaba da karbar horo a hannun ma’aikatanmu za kuma su cigaba da yiwa wannan jaha wasa har illa masha Allahu” nan da nan waje ya dau tafi raf raf kamar hall din zai tsage kowa cikin tsananin farin ciki yake, wannan uban kudade wannan dankareriyar mota da wani abu waishi lucky card da mutane basu ma san dashiba players har da masu kuka haka family dinsu basai na gaya muku halin da mutumin ke cikiba😜😜.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon