Alhamdulilahi jikin Khadija yayi kyau sosai dama yunwace tafi wahalar da ita tunda taci ta koshi yayi mata allurorin da zai mata sai ta sake komawa bacci, Dr baibar asibitinba sai da ya jawa bintu kunne sosai akan ta kula da ita sannan ya fita ya shiga dakin nurses din ward din ya kira wata nurse wadda zatayi aikin kwana ya nuna mata Khadija ya bata kudi yace "sister ga wannan inason da safe ki siyawa waccen yarinyar abinci ki bata da kanki karki bawa mai jinyar dan ba zata bataba cinyewa zatayi idan taci abincin ki bata maganinta tasha kinji plss ki kularmin da ita" nurse din ta karba tana cewa "karkaji komai likita insha Allah zan kula da ita amma likita kasantane?" Ya girgiza kai "ko daya kawai tana bani tausayine" nurse tace "ba matsala karkaji komai zan kula da ita".
Washe gari tun asuba Khadija ta farka ta sauko daga gadon tana dan jijjiga bintu dake kwance ta hangame uban baki tana bacci tace "bantu fo ji ni eh" ina bintu taji iskar fanka batama san tanayiba haka yarinyar ta gaji da magana ta tashi tayi hanyar fita daga dakin danma Allah yasa tana da hankali da a jikinta zatayi, dai dai kofar dakin nurses din wannan nurse din ta hangeta ta fito tace "Khadija ina zaki?" Ita dai Khadija bata santaba sai ta kasa yi mata magana kawai ta rike duwawu tana kallonta dan haka nurse din ta gane abinda take nufi ta shiga ward din ta samo mata aron fo wajen wasu mata ta dorata sannan taje ta dalawa bintu duka, bintu tayi firgigit ta mike tana Sosa inda aka daketa nurse din tace "dallah malama tashi kije ga yarinyar da kike jinya can tana neman ficewa sai ta bata a barmu da wahala kina nan kina uban bacci ki tashi kije kiyi mata tsarki" bintu ta yamutsa fuska tace "ai ita takeyi da kanta zata iya" baki kawai nurse din ta saki tace "waccan yarinyarce ke yiwa kanta tsarki? Lallai baku da hankali maza tashi kije kiyi mata mu ba'ayi mana kazanta anan idan kun koma gida ta cigaba da yiwa kanta" a dole badan bintu tasoba ta tashi ita kuma nurse din ta leka waje ta siyowa Khadija koko da kosai ta kawo mata.
Bintu na ganin abinci ta fara sidar baki ita kuwa sister tana kallonta dan haka ta zauna ta tasa Khadija a gaba sai da taci ta koshi ta tabbatar yarinyar ta koshi sannan ta dauke guntun ta bawa wani yaro nan kusa da gadon khadijan da basu da karfi sannan ta bata magani, Ba karamin shaka bintu tayiba da wannan rowar da akayi mata tana ji tana gani kosan da kokon haka aka bayar dashi.
Haka doctor ya cigaba da rainon Khadija ko bashi da aiki sai ya shigo asibitin kawai dan ya ganta da yake nan cikin quarters din asibitin yake, kullum shi yake bata abinda zataci sau tari da kansa yake zama ya bata a baki abinka da yarinya tasan wannan soyayyar daga Abduls dinta kawai take samu kawai sai ta fara kiransa da abul kamar yadda take gayawa yan uwansa.
Kwananta hudu ya sallamesu suka koma gida sai dai shi da kansa ya daukesu a motarsa ya kaisu har gida da sukazo gidan hakimai ma iya nan mota ke iya shiga sai ya ajiye motar suka daba a kafa dan yace sai yaje ya gano gidan kuma zai dinga zuwa yana dubata yadda idan sun cigaba da zalintarta zai gayawa kungiyar turawannan suzo su kama su.
Suna shiga gidan jaru na baje a gindin bishiya tana faman basgar rake sale da bintu suka shigo, ta daga kai ta kallesu tace "sannu 'yarnan kinsha wuya haka kurum baki haifaba an sakaki zaman asibiti" bintu ta zumburo baki race "ai wallahi innarmu sai naci uwar yarinyarnan shegiya mai siffar aljanu danma bakiga wulakancin da aka dingayimin ba a bata abinci ni kuma a hanani" jaru ta waro ido "horan yunwa suka dingayi miki? Basusan haramun bane ba? To Allah ya isanki Allah ya saka miki" sale ya dora hannunsa kan bakinsa yace "shishsh ya isheku kinmanta da likita mukazo? Allah yasa ya jiku wallahi da turawa yake aiki yace kaiku zaiyi su daure mutum ba abinda ya dameni" bintu ta murguda baki tace "ku kuka nuna masa kunajin tsoron turawa shiyasa wallahi ba turawaba ko indiyawane sai naci uban yarinyarnan idan ta shigo" sale yace "shikenan kiyi tayi innarmu ina baba? Likita yace a turo masa shi yana waje" jaru tace "yana bayana na goya dan rainin wayo" sale ya mike yana saka takalmansa yace "to saiki saukoshi ki mikashi waje" yana gama fada yayi waje ya barta tana masifa "kajimin marar kunyar yaro ni zaka gayawa magana? Zaka dawo ka sameni ke kuma leka can cikin kalgo watakil Baban naku nacan ki kirawoshi tunda wancan dan iskan ya fice" bintu tace "tab na dawo daga asibiti a gajiye kice wani naje cikin kalgo? Kema kinsan ba iyawa zanyi ba ni bacci ma nakeji" itama ta shuri nata takalman tayi daki sukabar jaru da sakakken baki.
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
