Chapter 31

62 11 0
                                    

Da sauri Abdulrahman ya sha gaban Abdulrahim sannan ya daga hannu ya kwada masa marin da shi kansa sai da yaji zafinsa, yana dagowa ya kuma dora masa wani wannan karon sai da Abdulrahim din ya kai kasa sannan Abdulrahman ya danja baya yana kallonsa hawaye na zuba a idonsa ya fara magana kamar mai magana da kansa ba dasuba yace "I'm so sorry inna, na kasa rike amanar da kika bani ba zan iyaba inna i give up on your son bazan iyaba, yafi karfina zuciyarsa tayi taurin da bazan iya lankwasataba bansan me yakeson ya zamaba bansan me yakeson yayiba amma kiyi hakuri yafi karfina bazan iyaba i give up" Abdulrahman ya saka hannu ya rufe fuskarsa yana kuka a hankali can ya bude fuskar da niyyar ci gaba da magana amma sai maganar ta makale a makoshinsa taki fita ya bude baki da ido gaba daya ya zubawa Abdulrahim su wanda ya mike tsaye kansa a kasa hawaye na bin fuskarsa, a hankali ya zame ya dira guiyoyinsa a kasa yana ci gaba da kuka ya fara magana muryarsa na rawa "Abdul dan Allah Abdul idan kace kayi giving up on me rayuwata Abdul rayuwata zata zama bata da wani amfani zan zama bani da alkibla zan zama ni kadai wasted please Abdul kar kayi fushi dani karka cire kanka daga rayuwa wallahi bazan sake abinda bakasoba bazan kuma musu da kaiba bazan kara yin abin da zai bata rankaba bani da kowa bayanku Abdul please" kuka yaci karfinsa dole ya rufe bakinsa ya kife kansa kan cinyarsa yana ci gaba da kuka sosai, jiki a sanyaye Abdulrahman shima ya tsugunna ya kamo dan uwansa ya rungume shima yana kukan (dama ya lafiyar kura😜😜) sai da suka dau dogon lokaci a haka tun Abdulrahman na tayashi kukan har yayi shiru sai ajiyar zuciya da yakeyi shi kuwa Abdulrahim tamkar yanayin dukkan kukan da bai samu yi bane tsahon wannan shekarun kuma dalilin da yasa Abdulrahman din ya kyaleshi yayi iya yinsa kenan yana ganin harda rashin kukan tun yana yaro ya kuma sakawa zuciyarsa take a kekashe banda Allah yasa mai barkwancine tabbas da Allah kadai yasan irin rayuwar da zaiyi.
Da kyar ya samu yayi shiru sannan ya kamashi ya zaunar kusa da khadija wadda itama taci nata kukan ta koshi sai ajiyar zuciya take, yana zama monitor din jikin malam musa ya fara beeping da karfi, da sauri Abdulrahman ya cika Abdulrahim din yayi kan mal musa sai ga wani Dr wanda abokinsune tun a California yau ya shigo garin dan shirye shiryen office dinsa da kuma tayasu shirin bude asibitin da za'ayi ranar monday, yazo wucewa zai tafi gida ya jiyo beeping din monitor din dan haka ya shigo dakin da sauri, yana zuwa Abdulrahman yace masa "cardiac arrest" da sauri Dr ya karaso ya janye Abdulrahman din ya fara performing CPR shi kuma Abdul din ya koma baya yana maida numfashi, kuka khadija ta fara tana tsoron abinda yasa su Abdul duk hankalinsu ya tashi batasan abinda yake faruwaba amma dai tasan babanta yana cikin tashin hankali rayuwarsa tana kila wa kala, Abdulrahim ya riketa yana rarrashinta yana kuma gaya mata babu abinda zai samu babanta insha Allah, Dr Bashir da Abdulrahman kuma suna kan mal musa wanda da kyar suka samu ya dawo sai dai yana dawowa kuma ya shiga coma.

Abdulrahman ya mikawa Dr Bashir hannu yana cewa "thank you Dr i really appreciate your help thank you" shima Dr bashir din yayi masa murmushi bayan ya bashi hannu yace "always Allah ya bashi lafiya" sannan ya juya ya fice shi kuma Abdulrahman ya juya wajen su Khadija yace "ku tashi muje zan nemi wanda zai kwana dashi ya kamata muje mu kwanta kuma haka" Khadija tace "yaya baba bai mutuba ko?" yayi mata murmushi yace "Khadija babanki bai mutuba yana da ransa bacci yakeyi yanzu muje gida kinji?" ta kada kai tana goge hawayen fuskarta, Abdulrahim yace "jinin fa?" Abdulrahman yace "bansan yadda za'ayiba zan daije nayi wanka na ci abinci tukunna sai na fita ko zan samo akwai wanda na sani a lab din murtala maybe a samu" Abdulrahim yace "zan bayar" Abdulrahman ya tsaya ya kare masa kallo sannan ya girgiza kai "no Abdul karka takurawa kanka akan abinda na fada na fadane kawai saboda abinda kayi badan jinin da ka hanaba ka barshi kawai" Abdulrahim yace "aa ba dan abinda ka fada nima zan bayarba dama can nayi niyyar bayarwar kawai nayi abinda nayine saboda inajin kamar an doramin wani abu mai nauyi a kirjina kuma idan nayi hakan zai sauka kuma ya saukan dalilin da har na iya yin kuka kenan dan haka zan bayar a yanzu inaji a jikina maybe just maybe zan iya yafe masa ma zan iya yafe masa komai" Abdulrahman ya rungume dan uwansa yanajin shima wani nauyi na sauka daga kan mafadunsa sannan ya sakeshi ya kamo hannunsa har sunje bakin kofa sai kuma ya juyo yace "to amma wa ka barwa wannan makarar?" Abdulrahim ya fara murmushi yace "gaskiya sai dai ka nemo wani ya dauke wallahi da nauyi bazan iya daukewaba" Abdulrahman yace "amma ai ka iya daukowa" daganan lab sukayi suka jira har aka dau jinin leda biyu sannan Abdulrahman ya tafi ya sakawa Mal Musa ya bar khadija wajen Abdulrahim sannan ya kira wani mutum daya taba tambayarsa aikin leburanci a asibitin dan nan makotan su dadyne ya sanshi tun yarinta yace zai kirashi shi ya kira ya tambayeshi idan babu abinda yakeyi yazo ya kwana da Mal Musa zai biyashi da gudu kuwa mutumin ya yadda kafin su gama abinda suke sai gashi yazo, Abdulrahman yace masa "yauwa tukur patient ne dani aminity room 3 a emergency yana coma babu abinda zakayi masa kawai dai inason wani ya kwana dashine incase wani abu ya faru ka kirani da gaggawa akwai jini na saka masa idan an jima zan dawo na canza ka kula fa" tukur yace "ba matsala yallabai" har ya juya sai kuma ya juyo yace "yauwa tukur ka duba cikin store dinnan na nurses station akwai barguna sai ka dauka kayi amfani dashi" tukur ya kuma cewa "to yallabai sai da safe" Abdul yace "Allah ya kaimu" ya juya zuwa lab suka hadu dasu Abdulrahim suka wuce gida.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Where stories live. Discover now