Chapter 32

79 11 4
                                        

Washe gari Abdulrahman yaje ya dauko Amira tazo ta taya Khadija shirya dakinta sannan ta fara koya mata yadda ake amfani da basic abubuwa kamar kunna ac, gas, water heater, tv da sauransu, bayan sun gama komai suna shirya underwares Khadija ta kalli Amira tace "wai anty Amira yaushene bikinku?" Amira ta kalleta tana dariya tace "bikinmu kuma ni dawa? ce miki akayi aure zanyi?" Khadija tace "aa kawai dai kinsan mu a kauye da wuri akeyi mana aure nima dandai innar bintu ta hanane amma da tuni anyimin aure tun tuni" Amira ta danyi dariya tace "zanyi aure tukunna dai maybe sai na fara aiki tukunna" Khadija tace "to ba kin gama karatunkiba? ai zaki iya yin aikin a dakinki ko?" Amira ta samu waje ta zauna kan cushion din dake closet din tace "Khadija kenan ba zaki ganeba yanzu kinga bani da saurayi sai nan gaba, idan Allah ya kawo mijin ai zanyi" Khadija ma ta dawo kusa da ita ta zauna tace "dama yaya Abdulrahman ba saurayinki bane? Nazata soyayya kukeyi har an kusa bikin ko ma anyi baiko" Amira ta kada kai kawai ta cigaba da ninke sikets din da takeyi, Khadija ta matso kusa da ita tace "amma dai ke kina sonsa ko? Shima kuma yana sonki" Amira tace "haka kowa yake kallon abun hatta dadyna haka ya dauka amma ba haka abin yakeba Abdulrahman da wadda yakeso ma daban" Khadija tace "amma kuma yafi nuna yana sonki ba wata dabanba tunda tun sanda nazo garinnan be hadani da kowaba sai ke" Amira ta danyi dariya tace "kinsan abinda ya faru?" Khadija ta girgiza kai Amira ta cigaba "lokacin da na fara haduwa dasu yaya Abdulrahman dashi na fara haduwa shi ya taimakeni na bata na kuma yadda takalmana ya daukoni ya goya sannan yayi ta bin gidaje neman gidanmu yana bani labarinki, daga baya muka fara shakuwa saboda makarantarmu daya a lokacin tsoronsu yaya Abdulrahim nake saboda irin fadan da suka yiwa shi yaya Abdulrahman din sanda muka fara haduwa to sai wannan fadan ya tsayamin a raina nakejin tsoronsu su kuma da muka fara shakuwa sai sukeson su jani a jiki dan haka suke tsokanata ni kuma sai na kama kuka shi kuma yaya Abdulrahman sai ya dinga taremin ko yanzu idan muka zauna idan kika kula kullum hirar kenan su suna tsokanata shi yana taremin kuma har yanzu ina kukan" ta fada tana dariya Khadija ma tayi dariya sannan ta cigaba "dan haka sai ya zama tsakanina da yaya Abdulrahman muna da wata alaka ta musamman wadda tafi wadda nakeda ita da kowa daga nan sai kowa ya fara daukan wai soyayya muke, ke in takaice miki Magana ni kaina ada nayi tsammanin soyayya muke bani da aiki sai maganar yaya Abdulrahman zan aura yaya Abdulrahman ne saurayina blah blah, sanda Ina boarding idan kowa na bada labarin saurayinsa kullum ina cikin bada labarin Yaya Abdulrahman duk wanda ya sanni ya sanshi, amma kinsan wani abu? Duk lokacin da nayi irin wannan maganar sai yayimin fada sometimes ma har fada mukeyi kowa yayi fushi da dan uwansa sai anijima kuma sai mu shirya, daga baya sai na fara tunanin ko dai kunya yakejine shiyasa baya son na dinga fadin hakan? sai na daina nima sannan nake ganin hakan a matsayin abin kunya daga baya sai na fahimci ai har su yaya Bello idan sukace masa ni budurwarsace sai sunyi fada bayason maganar kwata kwata sai na fara tunanin ko dai da gaske shi ba sona yakeyiba? duk da haka ban cire raiba sai da mukaje graduation dinsu a california" Khadija tace "inane kalifoni menene grad menene kikace?" Amira tayi murmushi tace "california wani garine can a wata kasar acan sukayi karatu idan za'aje sai an hau jirgin sama shi kuma graduation shine bikin kammala karatu idan mutum ya gama makaranta anayi masa biki da mutane haka shine to graduation kin gane?" Khadija ta daga kai tace "to me ya faru a wajen?" Amira ta cigaba "budurwarsa ya gabatarmin" baki Khadija ta bude cikin mamaki tace "budurwa kuma?" Amira ta kada kai hawaye na taruwa a gefen idonta tace "budurwa ya gabatarmin Khadija duk da baicemin budurwarsa bace amma tunda nake da yaya Abdulrahman ban taba ganinsa da ko yar ajinsu maceba sai ita dama dai yaya Abdulrahim ne nasanshi akwai zara kowacce kyakykyawa kawarsace ko budurwarsa amma dai yaya Abdulrahim sunan mata biyu na sani a bakinsa bayan innarsa" Khadija tace "dawa dawa?" Amira tayi murmushi irin mai ciwo dinnan tace "Khadija da Amira su kadaine sunan mata da yake kira mu kadaine mata a rayuwarsa da zuciyarsa gaba daya suddenly kawai sai ga wata wai ita Zainab sannan bayan mun dawo ma da ina fushi yaya Bello yace akanta nake fushi bakiga yadda ya hakikice yana tare mataba wai batayimin komaiba akan wane dalili zan dora fushina a kanta blah blah sannan rannan sai gasu suna waya to idan ba budurwarsa bace mecece?" ta share hawayen furkarta sannan ta cigaba "Khadija na bata lokacina ina tunanin yaya Abdulrahman sona yakeyi naki kula kowa shi kawai na sani kuma fa bashi da laifi tunda bai taba cewa yana sonaba bai kuma taba barina nace ina sonsaba amma kawai dai abinne ba dadi" Khadija tayi shiru ita abin gaba daya kwakwalwarta taki dauka can tace "amma ni har yanzu gani nake kamar yana sonki" Amira tace "kowama haka yake gani amma kuma bahaka bane sai kowa ya kawo wanda zai aura sannan zaku yadda" Khadija tace "badai kin hakuraba kike batun kowa zai kawo wanda zai aura" Amira tace "ba dole na hakuraba Khadija idan ban hakuraba me zanyi? nasan da wuya zan kuma sha wahala kafin na iya hakurin amma dole na hakura ko inaso ko bana so" Khadija tace "ni kuma wallahi bazan bari ki hakuraba duk da bansan wacece Zainab dinba ban kuma san menene tsakaninsuba amma ke kikafi cancanta da yaya Abdulrahman ba itaba" Amira kawai tayi murmushi ta mike tana diban kayan da suka gama ninkewa ta zubasu cikin drower dinsu.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Geschichten, die süchtig machen. Entdecke jetzt