Chapter 10

57 7 0
                                        

Ranar asabar suna makaranta suna karatu sun juya suna kallon bangon da suka jingina allonansu a jiki, Amira ta taho da gudu ta dane wuyan Abdulrahim tana cewa “yaya Abdulrahman ga chocolate dinka inji momy” shiru yayi mata dan yasan ba dashi takeba mistake tayi, ganin bai karbaba sai ta cikashi tana cewa “yaya Abdulrahman momyce tace na ka…” sai kuma tayi shiru tana kallon Abdulrahman din daya juyo ta kuma kallon Abdulrahim ta sake kallon Abdulrahman cikin kokarin tabbatar da waye Abdulrahman din sai kuma ta koma wajen Abdulrahman ta mika masa alawar tana cewa “gashi inji momy” dariya sukayi mata ganin duk jikinta yayi sanyi saboda ba wani shiri suke da Abdulrahimba tsoronsa takeji, Bello yana mata dariya yace “Amira wai da yaya kike banbance Abdulrahim da Abdulrahman? koni har yanzu idan ba wani abin sukayiba bana ganesu” tsayawa tayi kawai tana kallonsa alamar dai ko bata gane tambayar tasaba ko kuma batasan da yadda zata bashi amsaba, keyarsa Abdulrahman ya doke yace “zaka hargitsata dan ba fahimtar wannan tambayar taka takeba” alawarsa ya karba ya raba musu uku kowa ya dauki daya sannan suka juya suka cigaba da karatunsu Amira dake tsaye tana kare musu kallo tace “yaya Abdulrahman yau kayi wanka?” ya juyo daga kallon allon da yake yace “eh nayi” ta bata fuska tace “amma kuma baka wanke kayankaba ka saka masu datti?” yace mata “zan wanke” tace “yaushe?” dariya ya fara sannan yace “gobe” tace “ to idan ka wanke zaka kuma yin wani wankan?” nan ma eh yace maka sai kuma  tace “yaya sauke kafarka” ya mike kafar yana cewa “me zakiyi da kafata?” bata bashi amsaba ta kwanta a gefensa tare da dora kanta akan cinyarsa sannan tace “bacci zanyi”.
Usman na zaune can gefe saboda shi bayason haduwa da almajirai saboda zasu shafa masa datti wannan makarantarma babu yadda bayyiba akan kar a kawosu amma dady ya wani dage ko me zasuyi a makarantar almajirai? Amira ya hango ta tashi daga wajen da ya zaunar da ita cikin mata ta tafi wajen wadancan almajiran daya tsani ya bude idoma ya gansu, ido kawai ya kafa mata yana kallon duk abinda ya faru sannan ta kwanta akan cinyar daya daga cikin wadannan almajiran masu kama daya shi baimasan Hassan dinne ko usaini ba amma dai yaji kamar wani Abdul Abdul ma ake kiransu, whatever! bazai bari kanwarsa ta kwanta jikinsaba koma waye, tashi yayi yaje wajen ba tare da sun kula dashiba kawai sai gani sukayi anyi sama da Amira wadda har baccin ya fara daukarta, gaba dayansu sun tsorata har Amiran ai kuwa ta saka ihu tana neman kwacewa tane cewa “yaya usman ka cikani bacci nakeji” yace “bazan cikakidinba muje wajena sai kiyi baccin acan” tace “ni anan nakeso nayi” nan aka kama kokawa da Usman da Amira ita tana son zamewa shi kuma yana son sai ya dauketa sun bar wajen. Allah ne ya kawo Umar wanda zuwansa kenan makarantar yaga suna fada har Abdulrahim ya fara saka baki suna ‘yar fadi in fada shi da Usman din saboda Usman ya fara wasu maganganu akan zata shafi datti idan tana  shiga cikin almajirai. Dakyar Umar ya raba fadan sannan yace Usman ya kyale Amira yasan dai rigimarta shi zai zauna a wajensu tare da ita, a haka aka karasa karatun umar ya koma wajensu Abdulrahim ita kuma Amira tayi kwanciyarta a jikin Abdulrahman tayi baccinta.

Tun daga ranar kullum Amira tana zuwa zata wuce direct wajensu Abdulrahman tun yayyen suna damuwa suna gayawa iyayen har sun daina yanzu sun kyaleta sai dai kawai dady yace kullum su rinka saka musu ido dan ba zaka bar yarinyarka wajen wanda baka saniba yanzu duniya tayi lalacewar da dan karamin yaroma yasan iskanci, a gida kuwa duk abinda aka siyo sai an siyowa Abdulrahman koda ba’a siyowa Abdulrahim da Belloba sannan da ta tayar da rigima sai da dady ya siyo musu sababbin takalman da yayi alkawari, lokacin da azumi ya gabato kuwa ana ta sayayyar kayan sallah sai da ta saka aka siyo musu wani yadi aka kai musu dinki tana zuwa makaranta kuwa ta basu labarin dady ya kai musu dinkin sallah, zuwa yanzu ta saba sosai da Abdulrahim da Bello duk da dai Abdulrahman shine favourite dinta sannan wani abu dake bawa kowa mamaki shine ko a duhu ta gansu tana iya banbance tsakanin Abdulrahim da Abdulrahman abin da har yau tunda sukazo kano babu wanda ke iyawa ko Bello kuwa.

Kusan sati uku kenan yanzu har yanzu kullum Abdulrahim ne ke kawo musu abinci daga wajen matar nan da shi kadai ya santa, da safe ko da rana yake karbo musu yayi da kullum da daddare kuma suke karbowa a gidansu Amira. Yauma kamar kullum juma’ace bayan sun tashi Abdulrahman da Bello sukaje suka debo ruwa sukayi wanka suna cikin shiryawa sai ga Abdulrahim nan da kwanan abinci a hannu Abdulrahman ya kalleshi yace “ina kaje har munyi wanka bamu gankaba?” yana zama a kasa yace “abinci naje karbo mana kuzo muci sai nima naje nayi wankan” yana fada ya bude rubar da ya karbo abincin, indomie ce taji attaruhu da albasa da dafaffen kwai guda biyar, kallonsa kawai Abdulrahman ya tsaya yi da mamaki yana kallon abincin sannan yace “shima wannan din matarce ta baka?” yace cikin halin ko in kula da yanzu yake yawan nunawa idan ana masa magana “eh itace ta bani” Abdulrahman ya zauna kusa dashi sannan yace “kace ta sanmu ko?” Abdulrahim yace “eh ta sanku shiyasa ma take bani da yawa” Bello Abdulrahman ya kalla wadda shima kawai yake tsaye yana kallonsu sannan ya kuma kallon Abdulrahim da ya fara bare kwan kan abincin yace “amman idan ta sanmu ai tasan mu ukune me yasa ta sako mana kwai guda biyar?” daina abinda yake yayi sannan ya dago yana kallon Abdulrahman ya kalli Bello yana faman bude baki yana rufewa ya rasa amsar bayarwa, ganin bashi da amsa Abdulrahman ya maimaita masa tambayar da cewa “inajinka indai tasanmu me yasa ta bayar da kwai guda biyar ba uku ko shidaba? Sannan ita matarce take sadakar indomie?” shiru ya kumayi dan idea din kansa ta kare Abdulrahman ya cigaba da cewa “karka raina mana hankali Abdul ka gaya mana a inda kake karbo wannan abincin ka kuma kaimu wajen da kake karbowa idan ba hakaba wallahi Abdul bazan kumaciba tunda bansan a inda kake karboshiba sannan idan na mike daganan malam zanje na fadawa shi ka gaya masa" ya juya zai fice daga soron bayan ya dauki kwanonsa da sauri Abdulrahim ya mike ya rike hannunsa yana cewa “Abdul dan Allah ka tsaya kaji wallahi Allah ba abincin haramun bane hakkinkane kasan bazan taba baka abinda zai cutar da kaiba wallahi ba wani abin nakeyiba kuma kazo mu ci wannan zan gayamaka a inda nake samowa zan kaiku gidan da nake karbowa” da kyar ya samu ya dawo ya zauna sukaci abincin, Bayan sun gama sai kuma suka kama hira suna ta fama da Abdulrahim yaje yayi abinda zaiyi su fita kasuwa shi kuma yana makalewa wai yau baya jin zuwa kasuwar, ana cikin haka sai ga wasu samari su uku sun shigo soron kamar an jehosu wata mata na binsu a baya, matar itace wannan matar da su Abdulrahim suka taba kaiwa ajiyar kudinsu ta cinye musu rabon dasu ganta tun ranar da malam yace suyi mata Allah ya isa kuma sukayi matan sai yau, tana shigowa ta fara zazzare ido tana karewa soron kallo har idonta ya sauka kan su Abdul da kwanon abincinsu da basu kai ga daukewaba, ai kuwa ta juya wajen samarin da suka shigo tare tana cewa “kun gani ko daman na gaya muku sune suke zuwa suna sacemin abinci idan na dafa ku dakesu ni na sakaku” kafin ta rufe baki wannan samarin masu fushi da fushin wani sun hada kan su Abdulrahim Abdulrahman da Bello sun rufe su da duka, kaya kaya sai ga malam ya fito yayi musu tsawa kowa ya tsaya suna maida numfashi dan dai shi Abdulrahim bai bari an dakeshi a banza ba suna dukansa yana dukansu dan har sai da suka koma kansa gaba daya ganin yana neman fin karfin wanda ke dukan nasa, sai da suka tsaya sannan malam yace cikin fada “lafiya? Dan rainin hankali zakuzo min har cikin makaranta ku rufemin dalibai da duka? Ko me sukayi muku me yasa tunda har kukazo makarantar ba zaku gayaminba? Waye ma ya sakaku?” da sauri matar ta fito gaba tace “Allah ya gafarta malam nice nan na sakasu kuma kayi hakuri rainane a bace shiyasa na dau mataki a hannuna” kare mata kallo malam yayi sannan yace “to menene ya hadaki dasu da har kika biyosu kika sa ake duka?” tace “malam wadannan yaran tun wajen sati uku da suka wuce kullum idan nayi girki sai sun zo sun faki idona sun dauke abincin ko kuma su juye kusan rabinsa to kullum bana sanin wanda ke yi min hakan sai yau Allah ya toni asirinsu suna juyewa na fito naga ficewar daya da sauri daga gidan ina zuwa kitchen kuwa na tarar an juye min indomie din dana dafa hatta da kwan kai basu barminba sai da suka juye shiyasa ni kuma na dauko wadannan yaran makotan mukazo kuma muna zuwa muka tarar sun gama cin indomie gatanan kalli kwanan gabansu ka gani sannan kuma jiya an kawo min kudin adashi dubu goma daga ajiyewa in shiga daki zan dauko hijabi na kaiwa masu kudin wallahi kamar aljanu sai dawowa nayi na nemi kudin na rasa sun daukeshi” kallon su Abdulrahman malam yayi yayin dasu kuma suka juya suna kallon Abdulrahim cikin mamakin dama abinda yakeyi kenan? Dama duk abincin da sukeci na satane? Shi kuwa gogan ko a jikinsa wasa yake da kafarsa cikin kasar soron cikin kwanciyar hankali babu alamar tsoro a tare dashi jin maganar babbace yasa malam cewa su biyoshi shi kuma yakoma cikin gida aka shimfida musu tabarma suka zauna su kuma su Abdulrahim suka zauna daga kasa can gefe, malam ya kalli matar yace “inajinki me da me sukayi miki? Ba kece kwanaki ma kukayi fada anan akan kudin yaranba?” tace “eh malam nice amma kuma a lokacin ai an tabbatar bani na daukaba a lokacin ma karya sukemin” malam yace “an hakura dai bake kika daukaba ba an tabbatarba” ta fara rantse rantse malam ya daga mata hannu yace “an wuce wannan maganar tun tuni ba ita mukeyi yanzuba yanzu dai gayamin abinda yake faruwa” nan ta maimaita masa abinda ta fada tun a soro sannan ta kara da cewa “ni malam ina da tabbas din wallahi su suka daukarmin kudi da abinci saboda ga shedanan na gansu da idona sannan kuma ga abincin da sukacinan shine abincin da suka sacemin dan haka sune suka daukarmin kudi kuma ba nawa bane kawai su biyani” dan shiru malam yana kare musu kallo yayi sannan yace “kai waye a cikinku yake zuwa yana daukar mata abinci kuma ya daukar mata kudi?” duk sukayi shiru yace “idan bakuyi maganaba wallahi zansa ayi ta dukanku” nan ma shiru sukayi su sunsan Abdulrahimne amma kuma ba zasu iya fadadinba sannan shi kuma bai fada da kansaba dan haka malam ya cewa wani yaro da ya shigo “kai ilu maza kirawo min su garbati ko duk kolon da ka gani anan waje” ai kuwa ilu ya fita da gudu zuwa can suka shigo shi da garbati wani gabjejen kolo, suna zuwa ya tsugunna yace “malam gani” malam yace “dauki wannan bulalar ka hada wadannan yaran kayi ta duka har sai sun fadi wanda ya daukar mata kudi” Abdulrahim najin haka yayi saurin cewa “malam ni na dauka kar a dakesu su basusan ma na dauka ba” dan kada kai malam yayi sannan yace “waye ne Abdulrahim ne ko?” Abdul yace “eh nine malam” malam yace “dama ai nasan sai kai fitinenne me yasa ka daukar mata kudi?” Abdulrahim yace “malam ita ta fara daukar mana” malam yace “amma ba saida nace kuyi Allah ya isaba tunda baku da tabbas din itace ta dauka? Wato kai bakasan hakuriba ko? ba za’a baka hakuri kayiba yanzu ina kudinta yake?” yace “malam na kashe” a tsorace matar tace “dubu goman daga jiya zuwa yau?” ba tsoro ko digo a fuskarsa yace “eh” malam yace “karya kake zaka fadane ko sai nasa anyi maka duka a wajennan?” shidai Abdul yace ya kashe, su sarkin kuka har an fara sharar kwalla ya matsa sosai kusa da dan uwansa yace “Abdul dan Allah ka dauko mata kudinta dan Allah karka bari su dakeka” Abdulrahim murmushi kawai ya yiwa dan uwansa ya dauke kai.

Garbati malam ya saka yayi ta dukan Abdulrahim har saida bulalar da take ta fatar rago ta tsitstsinke amma uffan baiceba balle su sakaran zai fadi inda kudin yake, su Abdulrahman da Bello da basu ake dukaba sunyi sharkaf da hawaye da magina suna rokonsa yayi Magana amma kamar da dutse suka fuskarsa emotionless, ganin dukan na neman yi masa illa sannan kuma shi kansa mai dukan ya gaji yasa malam yace “kaga garba kyaleshi sakaminshi a dakin mari” kafin ya rufe baki su Abdulrahman sunkuma rushewa da wani kukan suna rokon malam afuwa (dakin mari wani dakine a gidan malam mai tsananin duhu wanda in dai aka kai mutum cikinsa ko hannunsa baya gani yawanci ma sai mai babban laifi ake kaiwa cikinsa ga sauro da cinnaku kamar kasa a ciki dan haka kowa tsoronsa yakeyi) amma malam yace ba daga wajensu yake sonjiba sannan ya juya wajen matar yace “yanzu dai baiwar Allah kiyi hakuri kinga dai yadda mukayi da yaron ya yadda shi ya daukar miki kudinki da abincinki amma yace ya kashe wanda munsan indai shi ya dauka din to karya yake amma yanzu zamu sakashi a dakin mari har sai ya fadi wajen da kudin suke ke kuma kiyi hakuri ki koma gida idan ya fada zamu kirawoki insha Allah” haka badan tasoba tayi godiya ta tasa samarinta a gaba wadanda suka gama tsorata da irin taurin zuciya na Abdulrahim suka fice shi kuma malam ya saka aka dauki Abdulrahim aka sakashi a dakin marin dake soro na karshe aka kulle.

.........................
Gosh ina son abdulrahim inason mutane marasa kunya masu kuma taurin zuciya akan gaskiyarsu kodaza'a kashesu

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Historias para obsesionarse. Descúbrelo ahora