Kamar yadda Bello yayi alkawari kafin komawarsu sai da ya takurawa prof akan maganar babansa, da fari prof din shareshi ya dingayi sai daga baya da bellon ya fara yin fushi sai kuma prof yaga cewar shi da ya rayu tsahon wannan shekarun yana neman dansa yanzu ya ganshi ta yaya yaron zai nemi wani abu a wajensa sannan ya kasayi masa? Wannan dalilin yasa prof ya yadda da cewar zai janye karar kuma ya fito dashi sai dai da sharadin ba zasu hadu da belloba ba zai fito dashiba sai Bello ya koma California da gudu Bello ya yadda da sharadin baban nasa ya kuma shirya suka koma ya bar maganar akan cewar za’a fito dashi kuma kamar yadda yayi masa alkawari ranar da suka tashi da safe da yamma kuma aka sakeshi.
Bayan komawar su Bello suka cigaba da karatu gadan gadan babu kama hannun yaro yayin da Abdulrahim shi kuma ya fantsama duniyar wasan kwallo, a yanzu Abdulrahim ya zama cikakken dan wasan kwallon kafa na duniya, ba karamin alfahari kuwa Nigeria keyi dashiba sannan yayi wani irin kudi lokaci guda if I said kudi I mean kudi!
A yanzu kaf sun daina wani part-time job saboda kudin da Abdul yayi da kuma irin allowance din da prof ke aiko musu dashi, kuma duk kudin da Abdulrahim yayi bai hana prof turowa hardashiba dan yace dan ‘da yayi kudi hakan baya nufin nauyinsa ya sauka daga kan iyayensa ba, su kuma bawai iyayen Abdulmalik bane iyayen 3abduls ne.
A yanzu ba karamin dadi rayuwa tayi musuba domin wasu turawanma basujin dadin da su sukeji dan sai da suka shiga turawan sannan suka fahimci ba karamar wahala sukeshaba a hakane muke ganinsu kamar masu jin wata uwa, har yanzu cikinsu babu wanda yayi wata budurwa kowanne karatune ya kaishi shi kuma namamajon ya ajiye batun yan mata ya fantsama harkar ball kullum yana cikin training dan haka shima yanzu bashi da lokacin zubarwa.
A haka har bello ya kammala karatunsana tsahon shekaru biyar dan haka ya hado kayansa ya nufo Nigeria ya barsu acan duk da yaso ci gaba da zama sosai sai dai iyayensa sun takura suna son jin duminsa dan ba karamin kokari ma sukayiba da suka iya barinsa ya koma makaranta duk da a cikin shekarar sau biyu suna kawo musu ziyara.
Bayan tafiyar Bello sai ya zamana Abdulrahman ya zama shi kadai dan yanzu Abdulrahim bai fiya zama ba kullum yana wajan training ko kuma suna da wani wasa, abun ya fara damunsa dan bai saba zama shi kadaiba amma shima sai ya yiwa kansa kiyamar laili ya tattara rayuwarsa ta koma library duk da dama rabin rayuwar tasa acan din yakeyinta, kullum yana can har permanent sit ne dashi a wata corner kullum yana can, wannan sai ya dan rage masa kewar yan uwansa sosai har ya fara jin kamar bashi da wata damuwa a halin yanzu.
Wata rana Abdulrahim ya samu Abdulrahman can cikin wani park da yake yawan zuwa idan ya gaji da karatu dan samun fresh air marar algus, park din a bayan building din da apartment dinsu yake yake dan haka basu shan wahalar zuwan sannan sai suka maidashi wajen hirarsu idan apartment din ya ishesu, yana zuwa kuwa ya tarar dashi zaune kan wani swing yana shan lemo kawai yana kallon wasu yara suna wasa, Abdulrahim yaje ya zauna kan kujerar swing din dake kusa da wadda Abdulrahman yake kai yana cewa “yau kuma kallon yara akeyine?” Abdulrahman ya dan yi murmushi yace “kawai sai suke tuno min da lokacin da khadija take yarinya inama a lokacin ma muna da kudin da muke dashi yanzu da tabbas ba wannan park din kadaiba sai wanda ta zaba zatayi wasa cikinsa koda kuwa Monday zatace a new York Tuesday a Chicago Wednesday a Boston ne sai inda ta zaba” Abdulrahim shima ya kalli yaran yace “tabbas idan da Allah ya ara mana irin wannan damar tuntuni da Khadija zata samu everything best, ba manage ba kwauro sai dai ba haka Allah ya tsara ba” Abdulrahman yace “hakane ba haka Allah ya tsaraba ni tunanina ma ko sunsakata makaranta tayi karatu ko kuwa haka suka barta?” Abdulrahim yace “Allah masani amma nafi zaton batayiba dan kasan halinsu mugayene” sai kuma duk sukayi shiru kowa na imagining irin rayuwar da Khadijan tayi ko takeyi cikin kansa.
Can Abdulrahim yayi gyaran murya yace “Abdul wata shawara nakeso muyi” Abdulrahman ya juyo da attention dinsa wajen dan uwan nasa yace “inajinka” Abdulrahim ya danyi shiru zuwa can yace “Abdul account dina yayi nauyi sannan kuma idan muka koma Nigeria muna bukatar gidan zama da wajen aiki tunani nake why not na fara turawa Umar kudi tunda kaga harkar civil engineering yayi yasan kan gini da sauransu inason ya nema mana fili if I said fili I mean fili ba wai dan karamiba wanda zamu gina gidan da zamu zauna ni da kai da Abdulmalik da kuma Khadija sannan mu iya gina asibiti a ciki yadda muna komawa kana da asibitinka idan Allah ya taimaka Amiran ma ta samu nursing din kaga shikenan kuna da wajen aiki ko ya kagani?” Abdulrahman yayi shiru zuwa can yace “Abdul banaso kayi asarar kudinka wajen…” da sauri Abdulrahim ya katseshi ta hanyar daga masa hannu yace “tsaya tukunna kafin ka cigaba wane part dinne a ciki asarar kudi? Gidan da zamu zauna ko kuma asibitin ko nursing din Amiran? Wannene asarar kudin a ciki? kudinnan ba nawa bane ni kadai namune mu hudu ni kai amira da khadija akan wane dalili za’a barni dashi a hannu ni kadai?” Abdulrahman yace “baka fahimceni bane Abdul bawai ina nufin asarar kudi zakayiba I'm sorry da word din da nayi using ina nufin kudinnan idan ka tura aka gina asibiti kai ba harkar lafiya ka karantaba babu abinda zaka iyayi dashi ka gane? why not kayi wani abu wanda zaka iya participating kamar wani business center dai haka” Abdulrahman yace “Abdul na fahimci bakasan nawane a account din nawaba bari ka gani” ya zaro wayarsa ya nuna masa available balance dinsa baki kawai Abdulrahman ya rike tare da zaro idanu cikin tsorata danshi kam wannan adadin kudin ma tsoro suka bashi Abdulrahim ya cigaba “da wannan amount din na tabbata sai ya kammala ginin gidan da asibitin da duk kayan da za’a bukata a asibitin illa iyaka kawai maybe dan Karin da za’a nema shima kafin mu koma gida na tabbata na samu, sannan kana maganar in bude abinda zan participating later idan wannan ya karbu zan bude wani kamfani wanda ni kuma zan yi aiki dashi” Abdulrahman yace “kammafanin me?” Abdulrahim ya gyara zama yana murmushin an tabo masa wajen yace “ka gane Nigeria wata irin kasace wadda mutanen cikinta basusan irin alfarmomi da ni’imomin da ubangiji yayi musu ba nigeria kasace mai cike da shara da datti kuma basusan shi kansa dattin wani arzikin bane, abinda nakeson naje na nunawa Nigerians kenan inaso na bude wani kamfani wanda zai dinga diban shara yana sorting dinta a fitar da renewable daban nonrenewable daban degradable daban haka non degradable suma, zamu maidawa kamfanonin da zasuyi renewing renewable mu binne non degradable muyi generating methane daga organic ones and many more Abdul zakayi mamakin abinda zanyi idan na koma gida da wannan kamfanin but for now kai da Amira nakeso ku kafu Khadija kuma idan tazo sai ta fadi abinda takeso dan inason ta samu abinda takeso komai tsadarsa komai wahalarsa” Abdulrahman yace “to yanzu idan ka karar da kudinnan a asibiti shi kuma kamfanin naka da yaya zaka ginashi?” Abdulrahim yace “ahh business fa akeyi da asibitin kana tunanin bazai fitar da kudin da ake bukataba? Beside” ya dan kashe masa ido yana murmushi yace “har yanzu ban tsufaba da kafafuna biyu da yarintata har yanzu ana damawa dani a duniyar kwallo in fact banma fara cin kudin kwallo ba tukunna”
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
