Chapter 43

67 11 2
                                        

Picture of Amira at the top👆

Khadija bata tsaya tunanin a jikin wanda tayi landing ba kawai ta dunkule a jikinsa tare da saka wani irin kuka kukan da ya kuma harzuka tunanin Bello ya sake rufe Usman da duka kamar zai kaishi lahira, har yanzu Abdulrahim na tsaye a gefe ya dunkule hannunsa into fist clenching and unclenching his jaw, so yake ya fara controlling kansa kafin yayi komai amma da yaga irin dukan da Bello keyiwa Usman din shi kuma ya kasa kare kansa sai ya nufesu da sauri ya zagaye hannayensa a kugun Bello ya fara jansa baya yana cewa "Abdulmalik stop it ya isa haka" Bello ya fara kokawar kwace kansa yana cewa "Abdul ka barni na kashe dan iska" Abdulrahim yace "Abdulmalik yaron dadyne Usman dan dadyne yayan Amirane" kiran sunan dady kadai ya isa ya saka duk su ukun daina abinda sukeyi duk zafin da zuciyarsu tayi tayi sanyi a hankali ya tsaya ya daina kokawar da yakeyi amma da ace mugun kallo na kisa da tuni Usman ya dade a lahira dan irin kallon da Bellon yakeyi masa, Bello ya daga hannu ya murza dan yatsansa yayi kara yana nuna Usman dashi yace "wallahi kaci darajar masu daraja amma ka tabbata ko kallon Khadija idan ka kumayi sai ranka ya mugun baci" yana gama fadin hakan ya juya ya nufi wajen da Khadija take dunkule jikin Abdulrahman tana kuka shi kuma ya rungumeta tsam a jikinsa yana jin tamkar zai maida ita cikinsa yadda babu wanda zai kuma yi mata wani mugun kallo balle ya tabata, Abdulrahim ma juyowa yayi zuwa wajen su khadijan duk suka tsugunna a gabansu gaba daya sun rasa abinda zasuce mata sun rasa bakin da zasu rarrasheta dashi, laifinsune da suka bari take kula Usman shiyasa har ya sami damar taba lafiyarta, laifinsune da basu saka ido akansaba laifinsune da basu ja masa mummunan warning ba amma anyi an gama bazai kuma ganintaba ma balle ya yi tunanin kara tabata.
Zuwa wani lokaci ta daina kukan da takeyi sai ajiyar zuciya har lokacin kuma suna zaune sun tasata a gaba Abdulrahman kuma bai sassauta rikon da yayi mataba, a hankali Abdulrahman ya dagota yace "sweetie tashi mu koma ciki kinji jikinki har ya fara daukan zafi" a hankali ta fara kokawar mikewa ya taimaka mata ta tashi sannan ya kamota tamkar yana ganin kafafunta ba zasu iya daukartaba su kuma su Abdulrahim suka biyo bayansa bayan Bello ya sake waigawa ya kalli Usman da haryanzu yake kokawar mikewa ya kasa, suna hawa kan baranda din gaban gidan Khadija ta fara wani irin haki kamar numfashinta zai dauke sai da Abdulrahman ya kuma riketa sosai amma duk da haka ta kasa kaiwa cikin falo, ganin haka Abdulrahim ya matso da sauri ya dauketa bridal style Bello ya bude musu kofa suka shiga da sauri Abdulrahman ya nuna masa kujera yace ya kwantar da ita shi kuma ya saka hannu yayi cupping fuskarta bayan ya kwantar da itan yana cewa "Khadija Khadija kalleni ki tsaya ki daina wannan abin ki kalleni" bata iya daina kokarin kai numfashi cikin nataba amma ta kalleshin ta maida dukkan hankalinta kansa, Abdulrahman yace "yauwa yanzu ki ja numfashi da karfi cikinki" ta ja yace "sakeshi to" haka yayi tayi mata har saida yaga numfashinta ya dan daidaita sannan ya kwantar da kanta kan filo din da Abdulrahim ya ajiye mata ya zauna a kasan kujerar da take yace "juyo ki kwanta sosai akan hannunki na hagu" shi kuma ya saka mata hannunta kasan kanta sannan ya saka babban dan yatsansa daidai saitin zuciyarta yace "Khadija yanzu dan rike min numfashinki" ta fara kokarin rike numfashin ta saka kuka ya dafa kanta da dayan hannunsa yana shafawa a hankali alamar rarrashi yace "i know i know it hurt but kiyi trying na yan seconds kawai" da kyar ta samu ta rike numfashin nata sai dai ko seconds 5 batayi cikakke ba ta fara wani irin tari da yasa dole ta saki numfashin har tana zamowa kasa daga kan kujerar, Abdulrahim banda yamutsa gashin kansa da zagaye a falon babu abinda yake haka Bello ma sunajin sun zama kamar wasu marassa amfani tana fara tarin suka zagayesu Abdulrahim ya yi kitchen da sauri ya dauko mata ruwa Abdulrahman na dan dukan bayanta sai da ya dan lafa sannan Abdulrahim ya tsugunna yana kokarin cire hannunta daga bakinta yana cewa "sannu ungo wannan dan sha" amma kememe taki cire hannun nata sai da ya saka mata karfi yana raba hannunta da bakin numfashinsu gaba daya ya kusan bakin jikinsu sakamakon abinda suka gani, jinine a hannun nata da gefen bakinta da sauri ta mike tayi kitchen dan shine yafi ko ina kusa da ita ta kunna fanfan jikin sink ta fara wanke bakinta da hannun nata hawaye na bin fuskarta.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang