Chapter 29

73 11 2
                                        

Abdulrahman ya fito daga toilet da dan karamin towel a hannunsa yana goge fuskarsa, da sauri Amira ta mike "yaya Abdulrahman zo mu tafi gida" yace "gida kuma? Me ya faru" ta marairaice fuska "yaya Abdulrahim ne yake wulakantani wai na cika masa kunne da surutu" murmushi kawai Abdulrahman yayi ya dauko sallaya ya fara kokarin shimfidawa, da sauri tasha gabansa "kaima wulakantanin zakayi ka watsamin kasa a ido?" Abdulrahim ya fara dariya "woo an sace mata gwiwa babu wanda ya damu da ita" ta kwabe fuska tana shirin yin kuka da sauri Abdulrahman ya ajiye sallayar "karma ki fara muje mu tafi mubar masa asibitin kuma zai gane kuransa warkewa yayi shiyasa" Bello ma ya mike yana cewa "ba zaku barni nima ya wulakantaba yau naga wani rainin hankali yakeji dashi muje nima gidan dama zani" haka gaba daya suka fice suka barsu yana binsu da dariya.

Bayan sun fice Abdulrahim ya nunawa Aisha kujerar kusa da shi yace "bismillah dan labarin ba dadi zaiyi kina nesaba" dan murmushi tayi sannan ta taso daga mazauninta na dindindin ta dawo kan kujerar robar dake gaban gadon ta zauna tace "to labarin me zan baka?" ya danyi tunani sannan yace "labarinki" da sauri tace "labarina kuma?" yace "eh labarinki shekarunki kannenki makarantar da kikayi everything" ta danyi murmushi tace "ai bani da kanne" yace "to yayyenki" tace "bani da yayye ni kadaice" ya tsaya kawai yana kallonta itama kallonsa takeyi sai can kuma ta dauke kai sannan ta fara "kamar yadda ka sani sunana Aisha Isah Ismail babana dan asalin kano ne cikin unguwar kurmi yana da yan uwa da iyayensa uwa da uba, wani course ne ya kaishi india a can ya hadu da mamana, ban gaya makaba mamana ba yar Nigeria bace Indian ce garin Delhi, marainiyace iyayenta sun mutu daga ita sai kaninta Ahmad, bayan haduwarta da babana suka musulunta ita da kanin nata bayan soyayya sosai ya nemi izinin aurenta amma mamanshi ta tubure tace bazai auri tubabbiyaba kuma Indian ba Nigerian ba, papa yace ansha daga da ita sosai daga karshema babansa da wasu kannensa su biyu su sukaje can suka dauro musu auren ba tare da mama ta saniba sai daga baya aka sanar da ita, a can India aka haifeni amma mamana tana haifata ko ganina batayiba ta rasu a lokacin da ta musulunta Aisha ta zaba sunanta dan haka papa ya maidamin sunanta, sanin mama batason mamana yasa ko da ya kammala wannan course din nasa bai taho daniba sai ya barni a hannun kanin mamana uncle Ahmad shi ya cigaba da rainona shi kuma papa da yazo gida ya gansu baifi wataba ya koma wajenmu, sai da babansa ya rasu sannan ya daukomu muka dawo Nigeria sai dai cikin wani ikon Allah mamana tana ganina Allah ya dora mata kaunata duk da har yau bata son mamana duk da bata duniyar amma haryau ban tabajin ta yabetaba sai dai idan anyi maganarta tabar wajenma gaba daya, inason kakata sosai kamar yadda take kaunata ranar da muka haduma naje gidan papa ne nace acan zan kwana sai da dare yayi ta tubure wai sai na taho, tunda ka kwanta ma kullum sai tayi rigimar zuwa ta ganka to ciwon kafa takeyi sosai sai da sanda take tafiya shiyasa papa yace ta bari sai ka farka tukunna.

Makaranta kuma nayi candy yanzu ina level 1 buk environmental management and toxicology papa yayi aure kusan shekaru biyar da suka wuce amma har yanzu Allah bai bani siblings ba sai dai fata" tunda ta fara maganar Abdulrahim ya kafeta da idanu ko kifatawa bayayi, jin muryarta yake kamar wata busar sarewa har wata iska yakeji tana shigarsa baiso labarin nata ya kare da wuri hakaba.

Jin tayi shiru ya fahimci ta gama sai da yayi gyaran murya sannan yace "Allah ya jikan mama nima tawa ta rasu" ta dan kalleshi ta maida kanta kasa sannan tace "ayya Allah ya jikansu gaba daya" ya amsa da "ameen ya Allah to baki gayamin shekarunkiba" ta danyi dariya "17yrs" yace "tab shekarunki daya da kanwata" tace "Amira?" yace "aa khadija Amira ta girmeku ita 19yrs take Khadija ita kadaice kanwarmu da muke uwa daya uba daya tana zamfara" tace "ku yan zamfarane kenan" kai kawai ya daga mata ta dan bata rai "that's not fair ni na baka nawa labarin kai kana daga min kai kawai bazaka bani ba" ta karasa maganar tana zumburo baki gaba, dariya Abdulrahim ya fara sannan yace "wai meyasa matan yanzu dukkanku shagwababbune? Allah dai yasa ba haka Khadija takeba" Aisha tace "su wa da waye shagwababbun?" yace "Amira itace sarauniyarku gaba daya ban taba ganin shagwababbiyar yarinya irin wannan yarinyar ba kuka fa bayayi mata wahala kinsan dazu da Abdul bai lallabata yace sujeba wallahi kuka zata saka sannan kema gashinan har an fara turomin baki gaba" ya karasa maganar yana kwaikwayar yadda ta turo bakin, da sauri ta rufe fuskarta da hannunta tana cewa "ni wallahi ba haka nayiba ba haka bakina yakeba" yace "to yaya yake" Aisha ta dan kare masa kallo sannan tace "kanaso ka canja topic dinne kuma bazan yaddaba, yadda na baka labarina sai ka bani naka" sai ya dafe ciki "wash Allahna wajennan ciwo yakemin anya basu manta wani bullet din ba wayyo cikina" kawai ta fara kyalkyala dariya harda hawaye shi kuma kawai ya tsaya yana kallonta, ada kallon miskila yake mata marar surutu amma yanzu da suka zauna sai yaji ashe tana magana harda dariyama kuma ba karamin kyau dariya tayi mataba, dariya bata taba yiwa wata kyau a idonsa irin yadda tayiwa humaira ba yes humaira zai dinga kiranta.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Historias para obsesionarse. Descúbrelo ahora