Chapter 41

61 7 0
                                        

Abdulrahman na gama abinda zaiyi a cikin gidan ya fito yana neman yan uwansa can ya hangosu suna ta hirarsu suna ta kyalkyala dariya, kallomsu kawai ya isa dalilin da yayi replacing frowning da smiling a fuskarsa yaji cewa wannan view din kawai ya isheshi farincikin rayuwa ya tabbatar Abdulrahim ma na farin ciki sannan ga Khadija da Bello na farin ciki haka Amira then babu abinda kuma zai nema sai fatan gamawa da duniya lafiya ubangiji yayi masa komai ya cika masa kowanne buri nasa. Yana zuwa wajensu ya zauna yana cewa "dariyar me kukeyi ne haka?" Bello da dariya a muryarsa yace "ka tuna wannan matar da muka taba bawa ajiyar kudi ta cinye mana?" Abdulrahman ya daga kai Bello ya cigaba "ita nake bawa love labari shine take dariya" Abdulrahman ma yayi murmushi yana tuna drama din da akasha a wancan lokacin Khadija tace "kai yaya Abdulrahim yayi wallahi" Abdulrahman ya kalleta yace "ohh saboda fitinenne ne shi shine yayi?" Khadija tace "aa kawai inason mutanen da basa bari a cucesu ne kaga ai ya kwatar muku yanco" Abdulrahman yace "ya kuma sha wahala ba" Khadija ta kuma kwashewa da dariya tana hasko yayannata cikin dakin mari.
Abdulrahman ya kalli Bello yace "ya Bello mune ka rakani wani waje mana" Bello ya mike daga kashingidar da yayi yayna cewa "ina fatan dai baka manta garinba dan karmu tafi mu bata a hanya" dariya kawai Abdulrahman yayi masa sannan ya kalli Khadija yace "sweetie zamuje mu dawo ki koma gida ki jiramu" Khadija ta daga masa kai kawai su kuma suka dau hanya har sai da ta daina hangksu sannan ta nade carpet din ta maidashi cikin mota ita kuma ta koma wajen mal musa a cikin gida.
Zama sukayi ita da babanta suna ci gaba da hirarsu a barandar dake kofar dakin jaru, kamar daga sama sai ga jaru ta shigo gidan kamar an jehota tana faman zare idanuirin na rashin gaskiya, mal musa da Khadija suka daga kai suka kalleta itama su take kallo mamaki rubuce a firgitacciyar fuskarta kallonta ya koma kan kafafun mal musa dake tankwashe ta kare masa kallo sannan kuma ta fara kokarin gyara fuskarta tana cewa "mal? Sannu da zuwa ashe kune kuke tafe?" mal musa ya kare mata kallo yace "wannan kuma ai sai dai muyi miki sannu da zuwa ba dan mu kam har mun kwana mun hantse" cikin mamaki ta zauna gefen tabarmar da suke kai tace "au tun jiya kukazo? Ku dasuwaye?" mal musa yace "wannan ba abinda ya shafeki bane" ya dauke kai sai kuma ya sake kallonta yace "daga ina kike?" da sauri jaru ta kalleshi tace "naam?" mal musa ya kuma hade rai yace "cewa nayi daga ina kike?" jaru ta dan karkace tana ta faman bude baki amma ko kalma daya taki fitowa daga bakinta saboda bata da abin kare kan nata, ganin ba zatayi maganaba mal musa yace "shikenan tunda baki da abin fada sai ki juya ki koma inda kika fito na sakeki saki daya saki biyu saki uku" ya fada yana lissafa sakin da 'yan yatsunsa, hannu jaru ta dora aka tare da zunduma ihun da ya saka gaba daya 'yayanta fitowa wadanda basuma san da dawowartaba.
Jaru na yunkurawa kawai taci kwalar mal musa tana fadin "wallahi mal baka isaba na rantse da Allah ban sakuba kai har ka isa kace zaka sakeni? Wallahi tallahi baka isaba duk abubuwan da nayi saboda kai? Duk wahalar da nasha saboda kai sannan kace wai ka sakeni aradun Allah baka isaba?" su habu sakin baki kawai sukayi cike da tashin hankali da jin wannan magana ta mahaifiyarsu wai babansu ya saketa.
Sale ya matso yana kokarin rabata da jikin babansu sai daya samu ta saki baban sannan yace "baba menene yake faruwane? Menene yake faru?" mal musa ya gyara kwalarsa yana shafa wuyansa dan ba karamar shaka jaru tayi masaba yace "cewa nayi na saketa saki uku" habu ya matso da sauri yace "mene? Baba me kake fada me tayi maka daga shigowarta?" mudi yace "me kuwa zatayi masa ba 'yayansa sunyi kudiba? Dole ya yar da inna kuma dai duk arzikin da sukayi itace rufin asirinka dan ita ta zauna da kai lokacin da' yayan naka basu dashi" mal musa yace "kuma ta nakasani ba nakasar da banajin har na bar duniya zan warke dan haka na kuma maimaitawa na saketa saki uku dan bazan sake zama da itaba" jaru na gunjin kuka tace "azzalumi maci amana wallahi babu inda zani sai dai kai kabarmin gidan dan naci gadonsa wallahi azzalumi kawai" mal musa yace "ke yanzu jaru har kina da bakin kiran wani da suna azzalumi? Zalinci har yakai na ki shiga malamai ki raba masoya sannan ki raba uwa da 'yayanta sannan ki azabtar dasu 'yayan? Kuma idan nace rabawa ina nufin kisa har lahira? Ke ai jaru kisa ne hukuncinki ba sakiba gida kuma sai kin barmin gidana dan na gama raba gadona ban kuma bar miki ko alluraba" Ba 'yar karamar danbarwa akasha da jaruba kafin' yayanta suka samu suka jata zuwa wajensu suna rarrashinta ita kuma banda rantse rantse na sai ta nakasa 'yayan nasa ba abinda takeyi, a daren mal musa ya samo wasu yara suka fito da kayan jaru kaf daga dakinta shi kuma ya gyara dakin yayi kwanciyarsa.
Su Abdulrahman kuwa da suka fita gidan hakimai suka tafi inda Abdulrahman yaje har gidan dagacin kauyen bayan sun gaisa yace "ranka ya dade baka shaidaniba ko?" mai gari ya kare masa kallo yaxe "gaskiya kam ban shaidaka ba" Abdulrahman yace "ranka dade Abdulrahman ne na gidan mal musa can hayin gebe yan biyunnan Abdulrahman da Abdulrahim da aka kai almajirinci" mai gari yace "masha Allah sai yanzu na gane Abdulrahman ina kuka shiga babu irin neman da babanku baiyi mukuba amma bai samekuba ina Abdulrahim din?" Abdulrahman yace "ranka ya dade Abdulrahim yana America" mai gari ya bude baki yace "America can garin turawa?" Abdulrahman yace "eh ranka ya dade" mai gari yacr "ikon Allah ai kwanakin baya naje duba baban naku sai ake cemin kunzo kunga halin da yake ma kun tafi dashi can kano jiya kuma mal basiru yace min baban naku ya dawo ashe tare kuke" Abdulrahman yace "eh tare muke amma mu gobe zamu koma shi dai yana nan zai dan kwana biyu" mai gari ya jinjina kai yace "masha Allah to Abdulrahman meke tafe da kai naga kamar da magana a bakinka" Abdulrahman ya gyara zama yace "yauwa ranka ya dade dama kaga na dade ne sosai bana nan dan haka yanzu kusan bansan kowaba a garinnan balle nasan aikinsu shine nace bari nazo nasan ranka ya dade kasan mutane masu amana da zan iya yarda dasu tunda ba zama zanyiba nima ina da aikina a can kano ina son wani maginine wanda zai iya yimin gini na zamani" mai gari ya kada kai yace "hakane kam dan akwai mutane da yawa maciya amana sosai, insha Allah zan hadaka da ka da wanda ya kamata ina zuwa" ya mike ya leka waje ya kirawo wani yaro ya aikeshi sannan ya dawo ya zauna yana cewa "yaron makotanmune acan birni yake aikin gini indai yananan baka da matsala ya san abinda yakeyi sannan yana da amana sosai" Abdulrahman ya kada dai sai kuma suka cigaba da yan hirarrakinsu har wanda aka kira ya iso ya shigo ya mikawa su Abdulrahman hannu bayan ya gaishe  da mai gari mai gari ya fara magana kamar haka "yauwa garba wannan shima dan nan kauyenne yace yanason za'ayi masa ginine shine yazo neman na hadashi da yaro mai amana nace gakanan dan haka kuje kuyi maganarku sai kayi masa aikin dan birnine nasan ka iya aikin yan birni" garba yace "insha Allah ranka ya dade ba zan baka kunyaba zan rike amana kamar yadda kace zan kumayi aiki mai kyau" sannan suka fita shi dasu Abdulrahman bayan Abdulrahman din ya yiwa mai gari alheri.
Suna fita Abdulrahman yayiwa garba kwatancen inda gonarsa take sannan ya misalta masa yadda aikin yakeso ya kasance shi kuma yayi masa estimate na komai da ake bukata Abdulrahman ya zaro kudi masu yawa ya bashi sannan yace babansa zai dinga kula da ginin shi kuma kamar yadda aka zabeshi matsayin mai amana yana fatan zai rike amanar.
Suna komawa gida suka tarar ana ta faman fito da kayan jaru Abdulrahman ya matsa kusa da mal musa yace "baba lafiya me yake faruwa" mal musa yace "ta dawo kuma na saketa kaga bana bukatar kayanta a dakina" baki kawai Abdulrahman ya saki yana kallon uban ba tare da yasan abinda zai fadaba sai ubanne ya kalleshi yace "Abdulrahman karkace komai kawai ka kyaleni ina son gyara abinda na batane da kaina" dole yayi shiru shima ya kwashi kallo, da dare suka kuma komawa inda suka kwana jiya suka kwana washe gari sallama kawai sukazo suka yiwa babansu Abdulrahman yayi masa bayanin duk abinda yake shirin yi uban ya saka masa albarka sannan suka shirya suka dau hanya bayan sun yiwa babansu da adi alheri mai yawa dan duk gidan ita kadai suka yiwa alheri ita kadaice matar alheri.
A hanya babu wata hira da sukayi sosai Khadija ma baccinta ta kwanta ta kwasa hankalinta kwance sai Bello da Abdulrahman ne ma suka dan taba hira itama kadan kadan, suna zuwa kowa ya nufi dakinsa dan hutawa ranar a haka ta kare washe gari kuma kowa ya koma kan aikinsa.
Kamar yadda Bello yayiwa Khadija alkawari ya samu Abdulrahman da maganar Usman ya nemi alfarmar ya kyalesu idan yaso sai su saka ido sosai akan yaron su rinka monitoring moves dinsa yana yin kuskure sai suyi masa kafa, Abdulrahman ya karewa Bello kallo yace "wai kai Bello na zata son Khadija kakeyi" Bello yace "inji wa yace maka? Kanwatace kamar yadda take kanwarku" Abdulrahman yace "Abdul ne ya gayamin kuma ya tabbatarmin kai da bakinka ka fada masa" Bello ya sunkuyar da kai yana murmuring 'dan iska' sannan ya dago ya kalli Abdulrahman yace "ok na fasa sonta" Abdulrahman yace "ohh dama haka ake soyayya a fara lokacin da akai niyya a gama sanda akaso?" Bello yace "whatever ni dai ga alfarmar da nake nema please idan kuma zaka nunamin ba kanwata bace takace shikenan" Abdulrahman ya dafe kansa can ya dago ya kalle Bellon yace "amma Bello kana da matsala ok fine let's give it a try amma wallahi the moment yayi messing da kanwata na rantse sai kunga asalin ko ni waye gaba dayanku har kai" ya fada yana nuna Bellon da yatsa, Bello ya dan daki kafadar Abdulrahman yace "rest assured friend babu abinda zai faru insha Allah" ya mike ya nufi dakin khadijan yana murmushi shi kuma Abdulrahman ya danyi tsaki yana jin kamar laifi yayi wannan amsawar da yayi.
Wayarsa ya zaro ya kirawo dan uwansa yana dauka Abdulrahman yace "wai dan Allah yaushe zaka dawo? Ina missing dinka da yawa abubuwa sunyimin yawa wallahi" Abdulrahim yace "banajin duk missing dina da kake yi yakai wanda nakeyi at least kai da Khadija da bello a tare da kai ni kuwa ni kadaine" Abdulrahman ya danyi tsaki shi kuma Abdulrahim ya yi murmushi mai sauti yace "ok tell me what's wrong?" Abdulrahman ya kuma yin tsaki yace "wai Bello ne ya nace sai mun bawa Usman chance" Abdulrahim yace "what? Wanne irin chance ana zaune kalau akan kanwar tamu? Khadija ce fa Abdul ina fatan baka bashiba?" Abdulrahman yace "tayaya zan iya resisting Bello? Kai kafi kowa sanin halinsa" Abdulrahim yace "tab to ai kuwa wallahi ina nan zuwa da kaina shi Bello wanne irin dolone wai? Instead of yayi fighting for soyayyarsa sai yayi sacrificing dinta?" Abdulrahman yace "waishi irin masoyin kwarai dinnan" a karshe dai dole suka hakura amma akan mistake daya idan Usman yayi to ya barar da damarsa.
A wannan satin abdulrahman ya saka Khadija a makaranta ta 6-6 dan haka kullum acan take wuni kuma boko da islamiyya ake koya mata nan da nan kanta ya kuma budewa ta ware sosai Qur'an da hadisai sai gasu sun fara fita a bakin Khadija haka boko ma, su Abdulrahman kuwa kowa ya koma harkar aikinsa kowa ya zama busy sosai yayin da aka maidawa Khadija wayarta suka ci gaba da shan soyayyarsu ita da Usman dinta.

............
Hi angels
Jiya nasan kunyi ta jira kukajini shiru I'm sorry something happened but ga wannan nan dan kadanne zuwa dare zan sake wani insha Allah.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Stories to obsess over. Discover now