Chapter 19

42 7 0
                                    

A yanzu duk wanda yasan Abdulrahman da Abdulrahim yana ganinsu zai banbancesu, Abdulrahman dama can mai sanyine dan haka har yanzu yana nan da sanyinsa baya tara gashi a Kansa sai dai saisaye sannan kullum da manyan kaya a jikinsa sabanin Abdulrahim da yaji rayuwar gym da filin ball gaba dayan jikinsa a murde yake kamar na yan dambe, sannan mawuyacin abune ka ganshi da complete kaya a jikinsa barshi dai da armless da three quarter ga uban gashi daya tara a kansa yana kashe masa uban kudi, Abdulrahim a yanzu duk kudin da ya samu is either ya karar dashi a jikinsa ko a kansa yau shine wancan gym din gobe wancan saloon din dan haka ko zaka hadiyi Qur'ani dan rantsuwa idan ba wanda ya sanshiba babu mai yadda ada shi din almajirine, farcen jikin Abdulrahim ma abin kallone saboda gayu.
Abdulrahim ya fito daga dakin da ayanzu suke zaune shi da yan uwansa, ya karasa kusa da Abdulrahman dake zaune bakin shagonsu yana karatun littafin bulugul maram, Abdulrahim din ya tsugunna kusa da shi yana daure igiyar takalmansa yace "Abdul zan tafi babu abinda kake bukata?" Abdulrahman ya dago kai ya kalleshi yace "idan na fada abinda nake bukatar yi min zakayi?" Da sauri ya kada kai yace "just name it ko menene?" Abdulrahman yace "so nake ka zauna muyi hira nayi missing dinka yaushe rabon da mu zauna muyi hira ni da kai?" Kai Abdulrahim ya fara sosawa yace "Abdul kayi hakuri na sani yanzu bani da time amma kaima kasan dan saboda wannan match din namune amma ka bari muna gamawa..." Hannu Abdulrahman ya daga masa "dama nasan ba samu zanyiba jeka Allah ya bada sa'a" jikin Abdulrahim yayi sanyi sosai yana son dan uwansa shima yayi missing dinsa rabon da su zauna kawai hakanan suyi hira tun kafin su fara wannan match din amma ba yadda zaiyi bazaiyi sanya da training dinnan ba dan yau wasu yan kano pillars ne suka gayyacesu training, wannan wasan da yayan yarabawa yasuyi ba kuma yaso yayi underestimating dinsu suzo suna bashi mamaki.

Keya ya kuma sosawa yace "sorry bro Allah kaima kasan dan babu yadda zanyine amma zan rama maka" murmushi kawai Abdulrahman yayi masa sannn yace "nace kaje Allah ya bada sa'a" Abdulrahim yace "ameen na tafi" sannan yawuce yana dan jogging har zuwa bakin titi ya hau babur din da zai kaishi Sani Abatcha stadium inda zasuyi training din.
Abdulrahim na barin wajen Amira tazo tana faman zumbura baki ta nemi waje kan dan bencin da ke gaban shagon ta zauna tana ci gaba da zunbura bakinta, Abdulrahman ya fito daga shagon ya tsaya yana kallonta ita kuma sai ta kalleshi ta dauke kai ta kuma kallonsa ta dauke kai taki magana shima yaki ya tambayarta wanda ya tabata, wani mutum ya zo siyan taliya shi kuwa ya juya ya koma cikin shago ya barta a wajen wani bakin ciki daya turmuketa kawai sai hawaye.

Bayan ya gama sallamar mutumin ya fito ya sake tsayawa yana kallonta ai kuwa ta mike kamar kububuwa tayi hanyar gida da sauri ya tari gabanta yana cewa "ayya afwan kanwata haba Amira waye ya tabaminke? Gayaminshi ko waye" ta share hawayen da yake bin fuskarta duk da tana sharewar wani na sake fitowa tace "ba kai bane kake kallona?" Yace "Allah ya baki hakuri wai jira nake ki fadamin abinda akayi miki shiyasa nake kallonki" ya karashe yana kunshe baki saboda dariyar data taho masa.

Sai ta kama bubbuga kafa irin na masu shagwaba tana cewa "ka gani gashinan yanzuma dariya kakemin" ya fara kokarin maida fuskarsa serious yana cewa "yi hakuri na daina kuma ma bake nakewa dariyaba wani Abu na tuna" ta tsaya tana masa kallon tuhuma sannan ta kuma kyabe fuska tace "wai makaranta dady zai maidani bayan nace masa banaso banaso amma yaki yadda" Abdulrahman ya kalli dama ya kalli hagu a tsakiyar hanya suke dan haka yace "kinga Amira zomu zauna" ba musu ta bishi suka zauna kan dan bencin dake kofar shagon nasu sannan yace "ke meyasa bakyason komawa makarantar?" Hawaye nabin kuncinta tace "kawai banason boarding din banason rabuwa daku suma su dadyn sun sani tunda naje makarantarnan fa kullum sai nayi kuka da kyar nake bacci saboda tsoro wallahi na tsani makarantar ga seniors suyi ta cin zalin mutane banaso wallahi" Abdulrahman yayi ajiyar zuciya yana kare mata kallo kafin yace wani abu wani mutum yazo yace a bashi sugar Abdul yacewa Amira "ina dan zuwa" ya tashi ya bawa mutum sannan ya rufe shagon gaba daya dan so yake yayi concentrating akan kanwarsa.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Where stories live. Discover now