Allahu Akbar kubra rai yayi halinsa dama duniyar ai ba matabbata bace bakine mu kuma tafiya zamuyi mu batta. Babu Wanda baiyi kukaba banda jaru da malam musa, jaru tayi kuka amma na munafunci, kana ganin kukan da takeyi kasan bana Allah bane gulmace, malam musa baiyi kukaba saboda a wajensa baiga abin kukanba. Wani irin zafi zuciyar Abdulrahim takeyi, mutuwar batayi masa ciwon da abinda mahaifinsu yayi masu ba, da ace ba za'a dakeshiba tabbas yau da sai ya kashe mahaifinsa har lahira.Wannan abu fa da malam musa yayi ba Abdul Rahim kawai ko Dan uwansa ya konawa rai ba kafatanin yan garin sai da sukayi Allah wadai da halayya irin tasa musamman ma da ungozoma ta fita ta fara bada labarin abinda ya faru, kowa ya tausayawa kubra ta kuma sha addu'a har a wajen wadanda basu santaba da yake ita ba Yar garin bace aurota yayi, wannan dalili yasa kubra tayi mutane da yawan gaske Dan ba'a taba ganin gawar da tayi wannan mutanentaba, wasuma cewa suke Anya babu aljanu da malaiku a ciki? Dan mutanen sunkai.
Sanda za'a fita da gawarta kuwa daga gidan yan biyu sun bawa kowa tausayi saboda rike makarar sukayi suna faman kuka kamar suma ransu zai fita su bita, abdulrahman fadi yake "inna dan Allah ki tashi, inna karki tafi ki barmu idan kika tafi mun shiga uku babu wanda yake sonmu a gidannan inna ko dan jaririyarki ki tashi dan Allah, karku dauke mana innarmu karku dauke" Abdulrahim kuwa alkawarurruka ya dinga daukar mata akan indai ta tashi ya daina fada ko wani zai dakeshi ko ya zageshi ba zai kuma fadaba zai dinga hakuri, amma duk kukansu haka aka banbaresu daga jikin makarar aka fita da ita.
Bayan an binnetane kowa ya watse dan malam musa ya Zama tamkar wani abin kyama babu Wanda ya tsaya yi masa gaisuwa, matan dake cikin gidama watsewa sukayi Amma memakon hankalinsa ya tashi a'a sai cewa yayi a dadinsa babu mai zuwa ya cinye masa abinci da sunan zaman makoki. Bayan an watse yan uwan kubra da sukazo daga can garinsu sukace to suma fa zasu tafi za kuma su tafi da wannan jaririyar da aka bari Amma malam musa sai ya buga kasa yace babu mai daukar ta tunda shine ubanta idan kuma suka tafi da ita to fa tabbas ya bar musu bayaso, wannan ya kawo hatsaniya mai yawa tsakanin yan uwan kubra da mal musa har sukayi zuciya sukace yaranma sun bar masa gaba daya sukayi tafiyarsu. Tunda yan uwan kubra suka tafi ranar uku kenan rainon Khadija ya dawo hannun yan uwanta babu Wanda yasan cinta ba Wanda yasan shanta balle maganar wankanta, da ta damesu da kukane sai Abdul Rahman yace da danuwansa "Abdul Ina ganin mezai hana muje wajen Inna matar mai kalangu ta dinga sammana nonon saniyarta muna bawa Khadija kaga sai mukaiwa ungozoma ta dinga yi mata wanka tunda bazamu iyaba ko?" Abdul Rahim na wani ciccijewa yace "Abdul karka taba tsammanin wani zai taimaka maka da wani abu, yanzu bamu da kowa sai kanmu Dan haka mu zamu taimaki kanmu, zan dingayi mata wanka nono kuma akuyar Inna data haihu rannan mu ringa tatsowa muna bata sai yafi mana da muje a wulakanta mu kasan ba bari zanyiba" Abdul Rahman ya girgiza Kai yace "bazaka iyayi mata wankaba kwananta ukufa tayi kankanta sannan ai ba'a Shan nonon akuya ko?" A zuciye ya dago Yana cewa "har akwai abinda kake tsammanin rayuwa bata koyaminba a yanzu da zakace bazan iya yi mata wankaba? Ka manta Inna ta taba gaya mana annabi Muhammad (s a w) ma nonon akuya yasha? Ka kyalesu ka kyale kowanne daga cikinsu sai nayi kudi zan Zama soja irin Wanda malamin boko yake gaya Mana zan dawo gaba daya na harbesu kaf dinsu kuma ka rike a kanka ta kan baba zan fara" bakinsa Abdul Rahman ya doke yace "Abdul baka da hankaline? Ka daina wannan maganar na tabbatar da Inna zatajika sai tayi maka fada sosai, yanzu dai ka gwada yi mata wankan mu gani idan ka kasa sai mu kaiwa ungozoma" haka yaran sukaje suka hada wuta Abdul Rahim ya dafa ruwan yayinda Abdul Rahman yake ta aikin jijjiga yarinyar. Yaran sunyi kokari sosai sunyi mata wanka suka shafa mata guntun Vaseline dinsu sannan suka saka mata kaya da yake dama innarsu ta tanadi kayan baby sannan mutane sun kawo mata da sukazo Zaman makoki. Nonon akuyar sukaje suka tatso dama wata yayar innarsu da tazo da yaro tazo da feeder ta barwa Khadijan a ciki suka zuba suka bata babu ko dumi har ta koshi sannan suka goyata.
Wani irin juyin mulki rayuwa ta yiwa tagwayen a yanzu sun koma tamkar bayi duk da dama asali bawai dadin rayuwar gidan sukejiba amma dai at least suna da uwa yanzu kuwa Babu, duk aikin gidan yanzu sune hatta surfe da daka da yake aikin mata su Abdul keyi alhalin ga yan matan jaru zaune suna kallonsu, sune shara, wanke wanke, daukar ruwa da itace ga daka Dan haka gaba daya Dan gayun da sukeyi da yanzu sun kazance idan ka gansu gwanin ban tausayi, Khadija kuwa cibiyarta har sai da tayi wari saboda su basusan gasawa akeba sannan ta damesu da kuka suka kaiwa ungozoma ai kuwa ta rikice Fadi takeyi "yanzu Dan rashin Imani ya hana yan uwan uwarku daukan yarinyar sannan ya bar muku ita? Yara yan shekaru takwas ya za'ayi su iya kula da jaririya danyar haihuwa? Wanene ma yake mata wanka?" A hankali Abdul Rahman ya nuna Abdul Rahim ai kuwa kawai baiwar Allah ta saka kuka Fadi take "mutuwa mai tonon silili banda mutuwa wazai Yi muku wannan yankan kaunar? Innanlillahi wa innailaihir rajiun jaru da malam musa sun shiga uku rayuwace kuyi hakuri komai mai wucewane" wannan shine dalilin da ya sa mafi yawan rainon Khadija ya koma hannun ungozoma itace take mata wanka tayi mata gashi ta saka mata wani magani cibiyar ta Fadi ta kuma daina wari, itace take bata Madarar akuyar da su Abdul ke tatsowa, wannan sai yasa suma abubuwan suka dan saukaka musu.
![](https://img.wattpad.com/cover/241558297-288-k502095.jpg)
ESTÁS LEYENDO
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Novela JuvenilLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...