Sai daga baya sannan sukeji a wajen malaminsu wai ashe mutumin wani mai kudine a nan unguwar shahararen mai kudine dama ya saba irin wannan sadakar kayan sanyi da sanyi ko kayan abinci da azumi da dai sauransu yana zuwa wajen da yasan akwai mabukata irin makarantar allo ko prison da gidan marayu, sansanin yan gudun hijira da sauransu, su dai koma waye lallai sun gode masa don ya ceci rayuwar su ba kadanba.
Dama sun dan tara kudin su daga aikin da sukeyi a kasuwa na dako, sai sukaje suka siyo irin ledarnan mai kama da tanti suke shimfidawa suna kwanciya saboda dama a tabarmar bello suke kuma yayi musu kadan, haka suka cigaba da rayuwa cikin tsanani kullum sai sun fita sannan suke samun abinda zasuci ranar kuwa da basu samuba sai dai su hakura, haka dan kudin da suke tarawa ma ake sacewa sai sunyi aiki sun hana cikin sun dan tara kudi sai a sace wannan yasa suka koma kashewa ko siyan wani Abu idan sun samu kudin. Haka suka cigaba da rayuwa har sanyi ya wuce aka fara zafi, a lokacin ya zamana ko sun fita aikinma da kyar suke samu saboda rayuwa tafi tsada sai kaga mutum da ya biya 'yar ashirin ko talatin a daukar masa kaya ya gwammace ya dauka da kansa saboda shima wannan ashirin din zatayi masa amfani, haka barar abincima idan sunje suma na gidan bai ishesu ballantana su bawa na waje.
Watan su Abdul shida kenan yanzu a kano, zuwa yanzu sanyi ya yi sauki an fara zafi dan haka sai ya zamana su Abdul sun koma kwana a waje saboda cikin mutane sunyi yawa, ayanzu babu abinda abdulrahman yake da buri irin ya shiga makarantar boko, haryanzu zuwa yake cikin makarantar unguwar yayi ta kallon daliban suna kaiwa da komowa gwanin ban sha'awa, sai dai bashi da yadda zaiyi dan haka dole sai dai leken amma bazai iya shigaba, kullum idan ya fadawa abdulrahim sai dai yayi masa dariya kawai saboda yana ganin kamar hakan bata lokacine.
Wata ranar juma'a bayan sun dawo daga bara suna hutawane sai Abdulrahim ya kawo shawara yace "Wai Abdul mai zai hana muma da wannan barar mu kama sana'a kamar yadda na taba fada a baya? idan kamar muka dan samu kudi mu fara saida pure water a danja ko su alawa da ake sayarwa a wajen kamar ya fiye mana wannan barar ko?" Dan tunani Abdulrahman yayi sannan yace "hakama kuma abune mai kyau sai dai nikam na gaji da wannan satar da ake mana yanzu idan ma mun samo kudin sacewa za'a dingayi" bello Wanda yake daga kwance yace "to idan mun samu mai zai hana mu dinga kaiwa ajiya mana?" Sukace "kamar Yaya kenan" ya mike zaune yace "idan mukaje muka samo sai mu samu wani gida mu tambaya sai mu dinga zuwa muna kaiwa matar gidan ajiya kunga a can babu mai zuwa ya dinga daukar mana" duk suka gamsu da wannan shawarar dan haka wannan satin da suka samu kudinsu na barar da sukayi a danja da kuma zubar da sharar da sukaje da yamma sati na zagayowa sukaje wajen wani mutum mai coldroom sukaje suka kai masa kudinsu ya basu ruwa mai sanyi suka shiga kasuwa, sun zaka meeting point da kuma lokacin haduwa, lokacin yanayi kowa zai dawo wannan wajen, sai sun hadu gaba daya sannan sai su dawo makaranta tare, akwai wani gida da bello yakeyin aikatau nan suka dinga kaiwa matar gidan da bankinsu suna kuma lissafin naira nawa ne kudinsu a gabansu zata dauko bankin su zaka sannan ta maida ta boye musu.
Lokacin da yanayin zafi yayi sosai, a lokacin watannin su Abdulrahim shida kenan a Kano, ranar da ake a lokacin zafinta kamar a kasar Niger idan mutum ya shigeta har cikin kansa, rannan su Abdul sun dawo daga talla kawai takalmin abdulrahman ya tsinke, dama ya sha tsinkewa suna likeshi da wuta duk takalman nasu dama sun lalace dan haka suka yi shawara sukace yanzu abinda ya kamata shine suje su karbo kudinsu suje su siyo takalma irin fillo toms dinnan gaba dayansu, nan kuwa suka tafi wajen matar nan sukace ta basu kudinsu zasu siyo takalma amma ga mamakinsu tana dauko musu bankin suka bude sai gani sukayi kudin ciki gaba daya N540 ne, wannan abu ba karamin daga musu hankali yayiba, suka cewa matar ina kudinsu sai cewa tafi "a hannuna kuke bani kudinku balle ku tambayeni? Dama bankin ku nake dauko muku ku saka da kanku dan haka sai dai ku tambayi bankin" tana gama fadar haka tayi tafiyarta cikin dakinta ta barsu da sakakken baki, a zuciye abdulrahim yayi niyyar binta Abdulrahman ya yayi saurin rikeshi yace "ina zakaje Abdul?" Zai fara balai Abdulrahman yace "muje muje kawai" haka ya jawosu Abdulrahim da Bello kamar wadanda kwai ya fashewa a ciki zuciyarsu banda zafi babu abinda yakeyi.
ESTÁS LEYENDO
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Novela JuvenilLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
