Abdulrahman na kwance saman boot din motarsu Bello kuma yana zaune kusa dashi ya saka earpiece yana jin kida yana dan buga kafarsa jikin bumper din motar kawai sai gani yayi Abdulrahman ya mike zaune a firgice ya dafe cikinsa kafin ya cire earpieces din ya tambayeshi abinda ya sameshi ya mirgino daga kan boot din zuwa kasa still dafe da cikinsa idonsa a rintse yana faman mirgina kai yana salati, shima Bellon salatin ya fara ya rike da Abdulrahman din, sai da ya dau wani lokaci sannan ya bude idonsa a hankali wanda har yayi ja kamar wanda yayi kuka sai kuma ya mike da sauri Bello ya rikeshi shima ya mike tsaye yana cewa "wai Abdul lafiya? Menene?" Abdulrahman ya kalli hanyar da Abdulrahim yabi yace "wani abu ya samu Abdul" Bello yace "ta yaya ka sani?" kallonsa kawai Abdul ya tsayayi sai kuma ya tuna, su Abdulrahim wasu irin twins ne wadanda duk abinda ya samu daya sai dayan yaji, koda kuwa bacin raine idan ran daya yayi mugun baci to sai kaga dayan ma ransa a bace koda kuwa basa tare, idan ciwo daya yaji to dayan ma sai yaji zafin ciwon sai dai bazai kai zafin da wancen yakejiba.
Bello yace "kaga mudan jira tukunna kaga ba tabbas ciwon yaji idan mukaga bai dawoba sai mu bishi" Abdulrahman yace "bata lokaci kenan idan kuma taimakonmu yake nemafa? Idan kuma ciwo yaji ko wasu mugayen ya hadu dasu fa? Yanzu zamu bishi" Bello yace "to amma nafiso ka kwantar da hankalinka...." bai bari ya gama gaya masaba ya dau hanya a kafa yana cewa "kai ka zauna ni na tafi dan nasan dan uwana na bukatar taimakona" dole Bello ya dauko motar ya biyoshi ya shiga sannan suka tafi suna tafiya suna kalle kallen inda zasuga Abdulrahim
.
Dai dai silver jubilee round about sukaga mutane da yan sanda har da yan kwana kwana Abdulrahman yace da Bello "Bello tsaya mu duba ko yana cikin mutanennan ba yawane dasuba zamuyi saurin ganinsa indai yana wajen" Bello ya gyara parking suka fito suka fara duba fuskokin mutanen dake tsaye da basu wuce mutum biyarba with hope na zasu ganshi cikin na tsayen dan ko kallon mutum biyun dake kwance a kasa basa sonyi amma kuma babushi ba alamarsa dole Abdulrahman ya juyo ya kalli mutanen dake kwance a kasa daya dattijone zai kai wajen shekaru hamsin da yan kai sannan da alama talakane dan jikinsa ya nuna fin shekarunsa, dayan kuwa yana kallon fuskarsa gaba daya numfashinsa ya dauke jininsa ya tsaya kwakwalwarsa ta daina aiki ya zamana bashi da control akan jikinsa, taku ya rinkayi baya a hankali idonsa kafe akan fuskar dan uwansa kwance akan titi cikin jini, Bello wanda shima ya kula da Abdulrahim din ya kalli Abdulrahman cikin tashin hankali shi ya kula da halin da yake ciki da sauri ya taho wajensa ya kamashi ya zaunar kan dan dakalin dake gefen titi ya rike fuskar Abdulrahman din da hannayensa yana faman kiran "Abdul Abdulrahman breath Abdulrahman kanajina? Breath" can daga nesa Abdulrahman yakejin ihun Bello amma ya kasa juyo da idonsa ya kalli Bellon idonsa na kafe kan fuskar dan uwansa, wani irin zafi kirjinsa yake masa kamar ana hura masa wuta a ciki, kwakwalwarsa bata aikin komai yana iya ji a jikinsa yana loosing consciousness dinsa amma babu abinda zai iya akan hakan, Bello hankalinsa ya gama tashi ya rasa yadda zaiyi dashi can ga Abdulrahim na bleeding su kuma yan sandan hankalinsu nakan wasu mutane da suka kama sunki bashi wani taimako wanda zai bashi taimakon kuma gashi dashi da gawa babu banbanci tunda ko numfashi yaki yi.
Jijjigashi ya kumayi ya sake daga murya tare da dan sosai marin fuskarsa yace "Abdulrahman i said breathe Abdulrahim yana bukatarka please Abdulrahman!" kamar kuma wanda ya farka daga bacci a lokaci daya ya fuzgi iskar ya kuma fara haki kamar wanda yayi gudu, kallonsa ya maida kan Bello sai kuma ya sake kallon Abdulrahim din dake kwance a firgice yayi kansa da gudu ya fara jijjigashi yana kiran "Abdul Abdul please don't do this Abdulrahim please" Abdulrahim dai babu alamun numfashi a jikinsa dan haka ya fara kokarin yi masa CPR wani dan sanda ya karaso da sauri yana ture Abdul din shima ya hankadeshi cikin masifa yace "I'm his brother he needs help" dan sandan yace "dan kana brother dinsa sai me? Dalla malam tashi" Abdulrahman yace "I'm also a doctor" dan sandan yace "can i see your id" rainin hankalin ya fara isar Abdulrahman da sauri ya zaro wallet dinsa ya fara neman license dinsa yana ganinsa ya jefi police din dashi da wallet din gaba daya sannan ya koma kan dan uwansa, ya saka abu ya danne inda akai harbin yadda zai rage zubar da jinin yakeyi ya yiwa Bello alamar yazo yace ya danne masa wajen da karfi shi kuma ya koma yi masa CPR din daya fara dan komai zai iya faruwa idan numfashinsa bai dawo ba, cikin ikon Allah kuwa numfashin nasa ya dawo ya bude ido da kyar Abdulrahman yace "Abdul stay with me ok? Karkaji tsoro inanan ina tare da kai babu abinda zai sameka insha Allah just try your best kayi focusing on me karka bari ka kuma loosing consciousness kaji?" kai ya dan daga masa a hankali jikinsa har karkarwa yake saboda azabar da yake ciki.
Abdulrahman ya kalli police din da har yanzu yake tsaye akansu yace "wai tsaiwar me kukeyine zakuzo mu wuce asibitine ko kuwa sai wani abun ya samesu?" dan sandan yace "kaga karka nemi kace zaka koya mana aikinmu muna sane dasu wadanda sukayi harbin muke kokarin kamawa" Abdulrahman yace "ina ruwana da wadanda sukayi harbi? Rayuwar dan uwana is at risk komai zai iya faruwa dashi yana zubar da jini da yawa kana gayamin wani wadanda sukayi harbi to ni zan tafi dashi idan yaso ku ku jira wadanda sukayi harbin ni zanje na kaishi asibiti" dan sandan yayi wata dariya sannan ya kira yan uwansa dake gefe suna zuwa yace "kunji wani bagidaje wai idan ba zamu tafi dasu asibitiba shi zai tafi dashi to bismillah kaje asibitin idan zasu karbeshi, asibiti basa taba karbar harbin bindiga sai da dansanda kafin ka nemo wasu yan sandan kuwa ya mutu" a zuciye Abdulrahman ya mike yaci kwalar dan sandan yace "sai dai kai ka mutu tsinanne kuma bana bukatar taimakonka ina da asibitina na kaina zanje na kula dashi da kaina gaba daya rundunar yan sanda bana bukatarta kuma sai kayi dana sanin wannan maganar da ka fada" ya kalli badge dinsa shima yayi yar dariya yace "aikin banza bakasan da wa kake ba zaka gane kuranka wallahi sai nayi maka sanadiyar aikinka idan bakayi wasaba koda kuwa hakan zai zama aikina na karshe a duniya" yana gama fadin haka ya hankadashi baya dashi da sauran yan sandan dake rirrike dashi ya juya yana kokarin daukan dan uwansa sai ga wata motar yan sandan ta karaso da gudu tana tsayawa wani mutum ya fito dattijone amma wannan da alama yaji hutu sabanin wanda yana ke kwance tare da Abdulrahim, sanye da jallabiya yake yana fitowa sauran yan sandan da yazo dasu da wadanda ke wajen duk suka kame masa shi kuma ya fara kalle kalle da idanunsa a wajen, wata yarinya ta taho da gudu ta kankameshi tana kuka shima ya rungumeta yana cewa "ya isa haka Aisha yi shiru nazo babu abinda wani zai kuma yi miki babu abinda zai sameki ya isa haka" sai da ya gama rarrashinta sannan ya taho wajen su Abdul yana rike da ita a lokacin kuwa har sun saka Abdulrahim a mota, yana zuwa yayi musu sallama yace "ya kuke sakashi anan motar me yasa har yanzu ba'a kaisu asibitiba? Maza muje asibitin tukunna mayi maganar acan" babu bata lokaci suka shiga nasu motocin mutumin kuma ya shigo tasu Abdul din sukayi asibiti, da farko Abdulrahman yaso su tafi nasu asibitin amma sai mutumin yace su dai je wani tunda can yace bai kammala haduwaba kuma babu likitoci shi kadaine.
ESTÁS LEYENDO
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Novela JuvenilLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
