Chapter 39

57 7 2
                                    

Ranar wata alhamis yamma likis Abdulrahman ya dawo gida duk a gajiye dan yanzu ba asibitinsa kawai yakeyin aikiba ya fara aiki a malam Aminu Kano yana aikin zuciya haka daga makwabtan states ma sai kaji yau wannan state din sun kirashi gobe waccan sun kirashi shiyasa kullum yanzu ka ganshi a gajiye Sundays ne kawai ko me mutum zaiyi bazaiyi aikiba yace mai nema idan baya hutawa to tabbas wataran sai dai a nemoshi.

Yana shigowa ya haye sama yayi wanka da ruwa mai zafi sosai ya shirya ya sauko kasa neman abinda zaici, Khadija na wanke wanke Mal musa kuma na zaune kan stool suna hira Abdulrahman ya sauko, ya gaishe da Mal musa Khadija ta gaisheshi yace "zan samu abinda zanci kuwa a gidannan?" Khadija ta kunna microwave ta saita time din tana cewa "eh bari na dumama maka ya fara hucewa dama naka yana ciki" Abdulrahman ya kada kai yaja stool shima ya zauna kusa da mal musa suna dan taba hira har aka gama dumama masa abincin ta miko masa ya faraci sai mal musa yace "yauwa Abdulrahman dama inason nayi muku magana ina ganin ya kamata na koma gida kuma haka tunda na warke tuntuni ko ya kuka gani" Abdulrahman yace "baba gida kuma? Me zakayi acan?" mal. Musa ya danyi dariya yace "ya zakace me zanyi acan? Ina da iyali fa ina da mata da 'yaya ina da yan uwana duk suna can kuma suna da hakki a kaina" Khadija tace "amma baba su basusan kaima kana da hakki a kansuba suka manta da kai? Baba watanninka shida fa a garinnan ka duba yadda muka daukoka daga gidan amma babu wanda ya biyo bayanmu wai dan yaga halin da kake ciki babu wanda ya damu yazo ya dubaka sai kai zaka damu dasu?" mal. Musa yace "banda abinki dije sanda nake tare dasuma wanene yake zuwa dubani balle yanzu da sai sun biya kudin mota sannan zasuzo? Dama can ban taba saka ran wata rana wani cikinsu zaizo dubaniba amma kamar yadda kuka sakamin sharrina da alkhairi nima zanso na saka musu nasu sharrin da alkhairi, sannan kuma inason naje na yanke igiyar aurena dake kan jaru dan banajin zan iya ci gaba da kallonta a matsayin matata bayan abinda tayimin, inaso na tattara kadarata gaba daya na rabar muku tun ina raye dan na tabbatar idan yanzu na rasu ba zasu baku komaiba" Abdulrahman yace "amma baba kasan bamu damu da wata dukiyarkaba kai muka damu da dan haka ka kwantar da hankalinka innarsu habu kuma zaka iya tura mata wasika ba sai kaje da kankaba su kuma 'yayan naka da kake magana ba yara bane balle su nemi taimakonka kai kake bukatar nasu su kuma ba zasu taba taimakon nakaba dan Allah baba ka manta dasu kayi zamanka anan" Mal musa ya mirgina kai yace "Abdulrahman ba zaka ganeba idan nace zanyi abinda kace su kuma yan uwanafa? Dole na koma gida watakil dai daga baya na dawo idan kunaso dole sai na dawo din" Abdulrahman yace "shikenan baba zan shirya zuwa wani satin sai na kaika kaje ka gansu ka dawo hakan yayi maka?" mal musa yace "zaka iyayin kwanaki acan kuwa yanzu? Kuma kaga aikinka yana bukatarka sai dai ka kaini kai ka taho daga baya na dawo ko da kainane" Khadija tace "au baba to wai kwana nawa zakayi acan?" Mal musa ya amsa mata da cewa "ban saniba amma inaso na dan kwana biyu" shidai Abdulrahman kai kawai ya dauke yana furzar da iska daga bakinsa bayason wannan tafiyar kwata kwata yafiso babansu yayi zamansa dasu.

Abdulrahman na gama cin abincinsa ya tashi ya koma dakinsa yanajin wani ciwon jiki banda ya tsara wasu aiki da zaiyi gobe kuma emergency ne tabbas da gobe babu inda zashi kwanciyarsa zaiyi yayi bacci amma duk da haka goben maybe sai wajen 10am zai fita dan aikin nasa sai 1pm tukunna, yana shiga dakinsa wayarsa ta fara kara automatically fuskarsa ta canja daga frowning zuwa smiling dan yasan me kiran tone dinta na musammanne, sai daya fada kan gado sannan ya dau wayar ya saka ta a kunnensa yace "my princess" tace "naam yayana kana lafiya?" Abdulrahman yace "lafiya kalau sai gajiya duk da kina kirana naji wani energy yayi replacing gajiyar kamar na sha energy drink" Amira ta fara dariya tace "kai yaya Abdulrahman" yace "Allah kuwan yadda nakejina yanzu indai zaki cigaba da yimin magana zan iya zuwa har gidan dady yanzu da kafa" dariya sosai Amira take tace "to ai ko da safe ka tashi da full energy ba zaka iya zuwa gidannan da kafa ba" shima yayi dariya yace "dadai dan ball ne shi zai iya" Amira tace "to kaima ka dan dinga hawa gym din nasa mana sai kaga ka iya" Abdulrahman yace "ai sun sakani yanzu kullum sai na hau shi da Bello wai sunce idan nayi tumbi zaki daina sona" Amira dariya kawai takeyi har da rike ciki tace "ohh kai kuma kana tsoron kar na daina sonka ko?" Abdulrahman yace "ke! Tab kina wasa ni yanzu ba kisan gara ace na koma yarintata na koma almajiri ba cin yau bana gobe ba da ace kin daina sona?" Amira tayi gyaran murya saboda dariyar da tayi muryarta ta fara dashewa tace "ba tumbiba koma me kayi bazan taba cewa na daina sonkaba i promise" Abdulrahman yace "kai amma dai na gode da wannan promise din ba kadanba make sure kin cikashi" tace "insha Allah amma fa gaskiya kar kayi tumbin" sai kuma ta sake kwashewa da dariya tana haskoshi da katon ciki.
Bello na kwance a dakinsa a wani dare, yauma kamar kwanaki biyun da suka wuce ya daina zuwa hira dakin baba, so yake ya dan janye jikinsa daga Khadija ko zai samu sauki sai dai fa kamar hakan wani tashin hankalin yake jawowa zuciyarsa, duk second din da yayi ba tare da itaba ji yakeyi kamar ya yishi cikin wani kuntataccen waje har ji yake kamar numfashinsa zai dauke tamkar wanda aka kulle cikin wata container, yana kwance wayanshi ta fara kara ya mika hannu kan bedside drower ya dauko wayar, Abdulrahim ne through video call, Bello ya tashi zaune ya jingina da fuskar gadon sannan ya dauka immediately Abdulrahim ya fara magana "hey bro lafiyanka kalau kuwa? Kwana biyu idan muna waya bana jin motsinka nace kana ina wai kwana biyu kullen kanka kake me ya faru?" Bello ya dan yamutsa fuska yace "wallahi ba komai kasan kwana biyu ina busy daga wannan gari sai wannan ba zai wuce stress na aikiba" Abdulrahim yace "karka dorawa aiki kaifa ba rago bane ya daga fara aiki zakace wani stress ya kwantar da kai idan baka da lafiya gaka ga likitoci me kakeyi a daki" Bello ya danyi dariya yace "wancan likitan zuciyane ita kuma matar tasa ta yara so banajin suna da abinda zasuyimin" Abdulrahim yace "yanzu tell me what's going on?" Bello yace "I'm serious ba komai" Abdulrahim ya tsaya yana kallonsa can yace "Bello i don't think kaf duniya a yanzu akwai wanda yayi maka sanin da nayi maka kai ka sani so definitely something is wrong menene? Bai kamata idan wani abu yana damunka kazo ka kulle kankaba kamata yayi ka samu wani ka gaya masa at least koda baiyi maka maganin abinba zakaji sauki a zuciyarka so oya gayamin ko nine bakason na sani?" Bello ya dauke kai ya daina kallon Abdul din can Abdulrahim ya bude baki cike da mamaki yace "oh my God! you are in love" da sauri Bello ya kalleshi yace "what? Where the hell..." Abdulrahim ya katseshi "wallahi Bello you are in love just tell me wacece? Oh my God ashe dai zanga wannan ranar?" Bello yace "dallah malam ya isheka" Abdulrahim yana dariya yace "I'm right right? Kawai ka gayamin wacece? Ka gaya mata kanasonta?" Bello yace "babu amfani wani takeso baniba" sai kuma jikin Abdulrahim yayi sanyi ya tsaya yans kallonsa yace "kamar ya? Ka gaya matane tace ma wani takeso ko kuma kawai kai kayi deciding wani takeso?" Bello yace "ban gaya mataba amma ita ta nunamin, kullum suna tare a waya idan kanason ganin dariyarta ka ganta tana waya dashi ya shiga ranta sosai" Abdulrahim yace "kaga Abdulmalik don't give up ni nasan yadda za'ayi gayamin wacece shawo kanta zamuyi ai ba kudinta ya kawoba sai ya kawo kudintane ta zama tasa amma har yanzu a kasuwa take so zamuyi fighting" Bello yace "Abdul kawai ka barshi zansan yadda zanyi" Abdulrahim yace "just ka gayamin sunanta already ka wani zauna kana kauce kauce kamar wanda yayiwa sarki karya tell me wacece? Na santa?" Bello ya sake dauke kansa ya kurawa can wani pic din Khadija dake kan mirror dinsa ido a waya ya dauketa batama saniba ya kai aka saka masashi cikin frame, Abdulrahim yace "haba Abdulmalik bakasan wai international call bane wannan? Kudina fa akeci" Bello ya danyi dariya "dama kanajin zafin kudi? I thought the famous footballer Abdulrahim kudi ba matsalarsa bane" Abdulrahim yace "wannan sai dai a gayawa special agent na shell ba wannan dan almajirin ba oya karka canja mana topic kai nake jira" Bello ya dan furzar da iska daga bakinsa sannan yace "fine! Khadija ce" kallonsa Abdulrahim ya tsayayi sai da maganar tayi sinking sai kuma ya kyalkyale dariya Bello yace "i knew it" yana cikin dariyar sai kuma dif ya tsaya kamar daukewar ruwa sannan yace "wait wait a dawo baya wani takeso?" Bello ya daga kai kawai Abdulrahim yace "ubanwa Khadija ta sani har take soyayya dashi? Kasanshi?" Bello ya girgiza kai yace "bansanshiba amma kamar sunansa Usman I'm not sure kamar dai haka take kiransa" Abdulrahim ya ture kujerar da yake kai ya mike ya fara zagaye a dakin nasa can ya koma ya zauna ya kalli computer din yace "wai yaushe har ta fara fita data hadu da ko waye ma? Ya akai take waya da wani ina Abdulrahman ya sani? Abdulmalik ba daki zaka shigoba fita ya kamata kayi ku rabata da ko waye, wanne tsinannan ne ma tukunna?" Bello ya girgiza kai "Abdul bansan wanne irin so take masaba idan na rabata dashi kuma taji haushinafa?" Abdulrahim yace "dan Allah Abdulmalik kaima karka batamin rai mana yaushe ta hadu dashi da har zatayi masa son da zaisa taji haushinka? Wai da khadijan ma gaba daya nawa take?" Bello yayi murmushi yace "tunda har ta kai munzalin da zansota kaima kasan ta kai wanda wani zai sota" Abdulrahim yace "shikenan ka cigaba da zama cikin daki like a coward ni kuma sai na rabata da koma wanene, God kai da Abdul are so annoying wlh" yana gama fadin hakan ya kashe computer dinsa ya bar Bello da waya a hannu.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Where stories live. Discover now