Anan asibitin su mal musa suka kusan wuni sai daga baya bayan Abdulrahman ya shigo sun gama gaisawa sannan suka kaisu gida dansu dan huta sannan akayi musu girki sukaci, anan ma haka habu yayi ta faman kauyanci suna shiga gidanma ya tsaya ya karewa kitchen kallo yace "dama anayin madafa a cikin runfa? Nasan ana ginawa a fitar da kofarsa kawai ta ciki naga yan kaura sunayin haka amma ban taba ganin an samu loko kawai an zuba kwanuka ace nanne madafa ba" Abdulrahim ya dan kalleshi ba walwala sosai a fuskarsa yace "kasan a turai mukayi karatunmu su kuma haka suke kitchen dinsu shiyasa da zamu gina namu mukayi haka" habu yace "amma hakan ai bai kamataba kun kwaikwaiyi al'adarsu kenan" Abdulrahim har ya juya zai wuce sai kuma ya dawo ya kare masa kallo daga sama har kasa yace "ina tsammanin kamar gidanmune kudinmune kuma ra'ayinmune ko? Ka kama kanka" ya karasa maganar yana nunashi da yatsa sannan ya juya yayi sama ya barshi anan tsaye dama Mal musa yaja nasa yan uwan sunyi dakinsa.
Tun daga nan ko habu yaga abinda ya bashi mamaki sai dai ya kalla ya kada kai ya daina magana dan yaga alamar ba suyi maraba da wannan neman maganar tasaba, ranar anan suka wuni suci wannan su sha wannan har dare a inda akayi ta musun a dakin wanda habu zai kwana kowa yace bazai daukeshiba sannan bai kamata ma suce ya shiga cikinsu Mal musa ba, a karshe dai Abdulrahman ne ya dau girma yace ya dawo dakinsa amma sai ya dauko masa bargon dakin Khadija ya shimfida a kasa dan babu yadda za'ai ya kwana dashi a gadonsa yana dauko bargonma Abdulrahim ya kare masa kallo yace "tab wannan bargon daga dakinka sai car wash ko bola ma" Bello ya saka dariya Abdulrahman kuma kawai ya kada kai yayi gaba.
Washe gari tun azahar suka nufi gidan dady dama sunce 2pm zasuje can zuwa 4pm kuma sai su tafi gidan su Aisha, Abdulrahim ne ya kaisu dan yau suna tashi tun asuba Bello ya bar garin ya tafi delta aiki dan haka shi kadai ya kaisu habu ma barinsa sukayi a gida dan wannan maganar manyace sunga alamar shi kuma yana da shishshigi.
A gidan Dady kuwa babu yadda baiyi da momyba akan ta shirya musu abinda zasu tari bakin amma kememe tace wallahi ba zata shiryaba ai yasan ba son auren takeba ba kuma zata taba so ba dan haka ba zata shirya musu ko ruwaba, kawai sai dadyn ya dau waya ya kirawo anty zulai dama tasan da maganar harda mijintama ya gayyata ya nemi ta shirya masa abin tarar baki nan da nan kuwa ta hada komai da mijin nata zaizo ya taho mishi dasu, dady mijin anty zulai sai kuma wani alh musa cousin din dady sune suka tari bakin anan falon dady na waje inda yake saukar bakinsa, bayan sun gaggaisa aka baje musu abinci sukaci har dasu dadyn sannan aka danyi barkwanci sai mal labaran ya fara maganar kamar haka "to alhaji ka dai san abinda ya kawomu duk da abdulrahman dan kane kaine mai zuwa ka nema masa aure kaine da hakkin uba a kanka dan Abdulrahman haifarsa kawai mukayi amma tarbiya ci sha sutura ilimi alhaji duk kaikayi wanda kuma ba zamu taba daina gode makaba ubangiji Allah ya saka maka da gidan aljanna ya kare maka iyalinka bamu da abinda zamu biyaka dashi sai dai fatan Allah ya biyaka da aljannarsa madaukakiya" dady da yake ta zabga murmushi kamar bakinsa zai tsage yace "haba malam ai yiwa kaine d'a ai na kowane bakasan wanda zaiji kankaba bakasan wanda zaka samu aljanna ta dalilinsaba dan Allah nayi dan kuma ita yarinyar dan haka babu bukatar godiya" mal sadi yace "alhaji dole ne muyi maka godiya saboda ba kowane zai iyayin abinda kayiba musamman ga almajirai wadanda a cikin al'ummarmu suke tamkar abubuwan kyama ake gudunsu amma kai ka jawosu jikinka ba dayaba ba biyuba har su uku ai kuwa kayi aiki na kwarai dole a jinjina maka" mijin anty zulai yace "ai mutanenmu suna da wata toshewar basira basusan ladan da yake cikin sadaka ba musamman ga marayu da almajirai" Mal sadi yace "to ai malamai ma suna cewa da ace za'a dawo da mutumin da ya rasu ya dawo duniya ace an sake bashi dama da babban abinda zaiyi shine sadaka saboda yadda takeda saurin shigar da bawa aljanna tafi duk sauran aiyukan zakka sallah azumi da sauransu saboda su wadannan saka ka akayi wannan kuma kai dan kanka ka saka kanka" mijin anty zulai yace "shiyasa kullum nake cewa da ace mutanenmu kowanne gida zasu dauki almajiri koda guda dayane su bashi abinci su bashi abin sha ba sai sun siya masa sababbin kayaba idan na yaransu ya tsufa su dauka su bashi idan sunyi wanki ko sun sakashi yayi musu wanki suce kaima cire kayan jikinka ka saka cikin ruwan kumfar ka wanke kunga basu bashi sabulu ba ma kenan wallahi da bazamu dinga ganin almajirai yadda muke ganinsu a titi ba" dady yace "ai idan kana ganin almajirai wani lokacin sai kaji kamar kayi musu kuka" alh musa yace "to banda abinka yaya mansur aini na taba yiwa wani almajiyi kuka na taba fa ganin wani almajiri nan kan titin gidan gwanma wajen danjar yahuza na tsaya a motata lokacin ana wani irin zafi bani da ishashshen mai amma haka na kunna ac na daga glass wallahi na hango yaron gaba daya banajin zai wuce shekaru tagwas dan dayazo jikin motata sai da ya danyi dage sannan yake leko motar ta window kasan ba takalmi a kafar yaron? Ka duba zafin da titi yake dauka idan rana ta kwalle da zafinnan yaron haka yake yawo ba takalmi sai tsalle yake yana dage kafa wallahi bansan sanda hawaye ya zubominba ji nayi a lokacin da ina da iko wallahi sai na hukunta iyayensa dan yayi kankanta da wannan wahalar haka da dauko kudi na bashi nace maza yaje ya nemi takalmi ya siya bakaga godiya ba ba karamin tausayinsu nakeji da zafiba" mijin anty zulai yace "ba da zafi zaka tausaya musuba sai da sanyi idan ka gansu wasu wallahi ko kayan arziki babu a jikinsu sai kaga kai yaranka an saka musu rigunan sanyi da saba da hula amma su haka zaka gansu suna ta karkarwar sanyi kuma kaga da mutanenmu zasu rinkayin wani abu idan sanyi yazo idan kaje nan kofar wambai ko bakin asibitin murtala haka zakaga safa N50 N50 suma kaya masu dogon hannun har dana N200 N150 idan ka siyawa kamar mutum uku ma ya isa wallahi sai kaga wannan ya kaika aljanna baka saniba" dady yace "duk ba sanyi ko zafine abin dubawarba damunace, idan ana ruwa kaje wucewa makarantun almajirai zakaga ko kyakykywan gini basu dashi ruwa na ta faman dukansu sannan babu damar zuwa bara dama gashi ita damuna naturally akwai saka yunwa sai kagansu sun kwana biyu wallahi babu abincin arziki saboda ba ikon zuwa bara babu kuma wanda zai kaimusu ya kamata mutanenmu su shiga lamarin almajirai tunda su iyayen nasu ba zasu daina kawosuba gwamnati ba zata hana almajiranta ba sannan malaman tsangayun ba zasuce duk uban da zai kawo dansa ya kawoshi da abinda zaiciba mu iyaye sai mu saka hannu mu tallafi yaran tunda su ba laifinsu bane" mal sadi yace "kuma wasu daga wannan shan wahalar fa shikenan suke lalacewa saboda yunwa sai aja hankalinsu da abinci shikenan a dulmiyar dasu" dady yace "su kansu su Abdulrahman din ai Allah ne kawai yake sansu Abdulrahim ya taba bani labari yace akwai lokacin da wani dan madigo ya taba jan Abdulrahman da niyyar zai bashi abinci ya kaishi wani kango da yaron ya fahimci mutumin ba na Allah bane sai ya fara kokarin guduwa shi kuma sai ya saka masa karfi Allah ya taimaka shi Abdulrahim din yaga sanda akaja dan uwan nasa shine fa yaje ya jiwa mutumin ciwo irin ta baya dinnan ya buga masa katako suka samu suka gudu" mal labaran yayi salati yace "subhanallahi kaji kuma wani rashin imanin" mijin anty zulai yace "to ai idan ka bibiya shima da almajirinne wahala ta sakashi cikin harkar kuma wallahi muma iyaye duk muna da laifi sai Allah ya tuhumemu daga su wadanda suka haifesu suka kawosu almajirancin harmu da suke yawo cikin unguwannin muna ganinsu amma bama taimaka musu" alh musa yace "ai nima dai nadau alkawari insha Allah daga yau zan fara taimakon almajirai iya kacin iyawata" mijin anty zulai yace "abu mafi muhimmanci ma shine nuna musu soyayya mu daina kyamarsu mu daina gudunsu kyamarsu da mukeyi shine yake saka suke zama kazamai amma da zamu nuna musu soyayya kodan su ji dadin shiga cikinmu wallahi zasuyi tsafta" dady yace "speaking of nuna soyayya kasan abinda ya fara kawo su Abdulrahman gidana kenan? Soyayya tsakanin 10yrs Abdulrahman da 4yrs Amira tun ranar da tayiwa Abdul din maganar me yasa baya wanka yace mata zaiyi gobe washe gari tace me yasa baiyiba yace yayi kayansane ba wankakkuba tace ya daina saka kaya masu datti ya dinga wankewa tun daga ranar basu kuma fashin wankaba basu kuma bashin wankiba kunga yarinya yar shekaru hudu kawai tayi abinda mu manya da yawanmu bamuyiba bata basu sabulu ko omo ba amma ta nuna musu tana son ta gansu tsaf su kuma suka nemo sabulu da omon da kansu" haka dai suka yi ta maida maganganu akan irin wahalar da almajirai kesha basuyi auneba kawai sai gani sukayi mal musa wanda tunda aka fara maganar ko kala baice ya saka kuka, gaba daya hankalinsu ya dawo kansa suka fara bashi hakuri kowa na tunanin abinda ya fada daya tunzura mal musan amma ga mamakinsu kawai yana bude baki sai ya fara cewa "Allah ya isa tsakanina da jaru Allah ya isa yanzu duk wannan wahalar 'yayana sukasha ina raye kuma ina dashi ba bani dashi amma ta saka yarana a wahala wadda ke gaban nawa kuma ta nemi ta kashemin ita Allah ya isa tsakanina da ita bansan da wanne ido zan kalli kubra ranar lahira ba akan abinda nayi mata ita da yayanta" mal labaran yace "haba mal musa ya kake abu kamar yaro? Duk munsan ba laifinka bane ubangiji ma ya sani ka daina mata Allah ya isa ko baka fadaba Allah zai isar maka zai isar muku ko yanzu ai kun fara ganin sakayya wa ma yasan inda take? Sai Allah dan Allah ka daina wannan abin"
A karshe dai mal labaran ya jawo 'yar karamar jakar da sukazo da ita ya turawa alh musa dake kusa dashi yace "to ga kudin aure nan muna nemawa danku Abdulrahman auren 'yarku dan amarya da angon duk nakune" duk sukayi dariya alh labaran yace "tabbas kam duk namune dan haka mun bawa danmu Abdulrahman auren 'yarmu Amira Allah yasa abokan alkhairi ne" gaba daya suka amsa da ameen ya Allah, mal sadi yace "to muna kara godiya Allah ya saka da alkhairi sai kuma yanzu zamu saka rana ko kuwa mu jira jin daga gareku?" mijin anty zulai yace "basu bada watannin da sukeso ba su yaran?" mal sadi ya kalli mal labaran ya girgiza masa kai sannan yace "gaskiya basu bayarba jiya dai munyi hirar basu ko fara giniba sai nan gaba zasu fara" alh musa yace "ai wannan ba matsala bace tunda alhamdulillah da abin hannunsu gini bazai basu wahalaba ina ganin me zai hana mu saka watanni biyu" ya karasa yana kallon dady cikin neman shawara dady yace "eh kam ba matsala watanni biyun sunyi insha Allah" nan sukayi addu'oi sannan suka tashi zuwa masallaci da yake ana ta kiraye kirayen sallah.
Bayan sun dawo daga masallaci kuma su alh musa sukayi musu sallama sannan su kuma suka dunguma sai gidansu Aisha tare da dady nan ma dai abinda ya kasance kenan sun tarar da Abba cp shima da nasa yan uwan kuma sun karbesu hannu bibbiyu daganan aka gabatar da abinda za'a gabatar shima Abdulrahim aka bashi Aisha suka bada kudi aka kuma tsayar da watanni biyu kamar yadda suka bukata.
Dady yana dawowa gida dakin Amira ya shiga da jakar kudin a hannunsa, tana kwance kan gado kamar kullum dan cikin kwanakinnan momy ko makaranta ta hanata zuwa itama kuma da yake ba jin dadin jikinta takeba sai ta hakura bata tayarda hankalintaba, idonta a rufe yake amma dady yasan ba bacci takeba ya samu bakin gadon nata ya zauna ya saka hannunsa a goshinta yajishi zafi zau, jin hannunsa sai ta bude idonta wanda yake jajur ta zuba masa su sai kuma hawaye dady ya dan kada kai yace "haba Amira haba princess me kike yiwa kankine haka? Na gaya miki tunda Abdulrahman kikace kinaso kuma ni nasan halinsa nasan asalinsa yana da aikinyi bashi da wani aibu da musulunci ya hana a bashi matar aure ni na gaya miki zan tsaya miki sai kin sami abinda ranki keso indai alkhairi ne dan kullum abinda nake roka miki kenan" ya mika mata hannu ya cigaba "taso kiji wata magana" ba musu ta kama hannunsa ta mike zauna tana share hawayen fuskarta dady ya dauko kudin daya ajiye kan bedside drower ya dora mata a cinyarta ta bishi da kallon tambaya yace "bude ki gani" ta saka hannu ta zuge zip din kudine N500 note cikin jakar ta zaro ido tana kallon dady tace da wata dashashshiyar murya "dady kudin menene wannan?" ya sakar mata murmushi yace "kudin aurenkine ke da Abdulrahman yanzunnan muka karba nan da watanni biyu zamu daura muku aure insha Allah" da sauri ta ajiye jakar a gefe ta matso ta rungume dadyn sai kuma ta saka kuka.
Dariya yayi tayi mata har da dauko waya yace "bari na yiwa Abdulrahman din video ince gakinan kina kuka kince kin fasa" ta kuma kwantar da kanta tana dariya hadi da kuka a lokaci daya, bayan da gama ta zauna sosai har da su zuro kafa kasa dan wani karfi taji a lokaci daya ta kalli dadyn tace "amma dady momy fa? Ta yadda?" dady yace "aa Amira bata yaddaba amma zan yi mata magana nasan zata yadda" Amira ta sunkuyar da kai tace "dady tsoro nakeji kar tayi fushi dani tace naki jin maganarta ta hanani naki hanuwa" dady yayi shiru yana kare mata kallo yana kara jin son yarinyar a ransa yace "Amira ki kwantar da hankalinki zata sauko naje na tuntubi hajiyata tun ranar da sukace zasuzo itama ta yadda ta nuna amincewarta har take cewa ta dade tana addu'a Allah ya sa wani cikin su ukun ya fito yace yana sonki dan ta yaba da halinsu da kuma irin son da suke miki haka duk wanda na tambaya shawara da sauri suke karbar su Abdulrahman din antynki zulai ma bakiga murnar da tayiba su kansu yan uwan momyn taki sunyi murna dan duk sunsan halinsa duk da nasan wasu dan abin hannunsa suke sonsa da ba sonsa sukeyiba amma dai mu ba dan abin hannunsa muke son aurenba dan haka ki kwantar da hankalinki babu abinda mukeyi marar kyau Allah bazai kunyatamuba itama zata sauko kafin bikinma insha Allah" Amira ta jinjina kai baki har kunne dady yayi dariya yace "ohh princess ta yaya Abdulrahman irin wannan warkewa lokaci daya?" tayi saurin rufe fuskarta tana dariya, ana cikin haka wayarta ta fara kara ta saka hannu ta daukota Abdulrahman ne rabon da ta dau wayarsa tun ranar da momy ta koreshi kullum zaiyi ta kiranta amma bata dauka amma yau tana ganin sunansa wani farin ciki taji yana lullube zuciyarta ba tare da wani tunaniba ta dauka ta kai kunnenta.
Mikewa kawai dady yayi yana mata dariya ya dauki kudin ya juya ya fice ita kuma ta fada kan gado sai faman dariya takeyi, Abdulrahman da ke zaune shima a office dinsa baisan sanda yasa dariyarba yace "wow Amira wannan dariyar fa? Bayan kin gama gasani shine kikemin dariya ko?" tace "wayyo yaya Abdulrahman ni na isa na gasaka? Ai idan nace zan gasaka sai na fika jin zafin wutar" Abdulrahman yace "anya kuwa? Da kinajin zafin ba zaki daina daukan wayataba" Amira tayi juyi ta koma rigingine tace "da kasan da yadda nake hana kaina daukan wayar taka da bakayi mitaba" yace "to menene dalilinki na kin dauka?" kawai ta danyi murmushi yace "umhm ina jinki fadamin dalilinki" tace "idan na dauka zanyi mana famin ciwon da bamu da maganinsa ne" Abdulrahman yace "amma da ace muna jin muryar juna zamu rage wani radadin ko?" shiru kawai tayi daya fahimci batason wannan zancen sai ya faraa bata labarin zanen da akayi na gininsu yadda zai kasance future gidansu ai kuwa nan yaji asalin Amiransa baki ya bude.
Washe gari Abdulrahman da Abdulrahim sukaje construction company din dayayi musu ginin asibitinsu suka basu zanen sannan suka daukesu suka kai inda filin yake suka ganshi aka kuma fara maganar kudin gini, kamfanin sunyi alkawarin su basu wata guda komai zai kammala idan sukace komai suna nufin komai dan haka suka sambada musu advance su kuma washe gari suka fara aiki.
Gidan Abba prof sukaje wajen hajiya aka fara maganar kayan lefe Abdulrahim yace "hajiya a ina za'ayi siyayyar lefennan ne" hajiya tayi dariya tace "lefenku Abdul ai yafi karfin shagunan Nigeria" gaba daya suka saka dariya Abdulrahman yace "hajiya sai shagunan ina?" tace "Dubai can zanje na hado muku lefe na gani na fada wanda kowa ya kalleshi sai ya kuma wanda za'asan the famous 'yayan dady da Abba zasuyi aure" nan ma dariyar suka sakeyi tace "kuma zuwa next week zan tafi dan naje na hadosu da wuri kar muyi abu a kurarren lokaci" Abdulrahim ya zaro wani atm card ya mika mata yana cewa "hajiya ga wannan sai ki fara amfani dashi idan ana bukatar kari sai mu karo" harararsa tayi tace "haba Abdulrahim ce maka nayi ku zaku siya? Abbankune zai siya dama jiya yayimin maganar da mukayi waya dan haka bana bukatar ko kwandalarku tamu gudunmawar kenan" baki kawai suka saki sunma rasa me zasuce dan farin ciki.
Ranar Friday tukur driver din Khadija specialist ambulance ya dauki su mal musa a motar Bello ya maidasu har gida tare da sha tara ta arziki sai kuma sun dawo biki amma kafin tafiyarsu habu ya samu Abdulrahman tunda yaga alamar ya danfi sauki ya rokeshi yace "Abdulrahman nasan nayi muku laifuka da dama kuma ina rokon dan Allah ku yafemin lokacin da bakwanan sanda Khadija tafi bukatar taimako sama da ko yaushe amma nima sai na biyewa sauran na yasar da ita naki na tallafa mata ina fatan zaku yafemin dan Allah" Abdulrahman yace "haba habu karka damu babu komai komai ya wuce Allah ya yafe mana baki daya" habu ya amsa da ameen sai kuma ya kama susar keya Abdulrahman ya kalleshi ya danyi murmushi yace "ya dai akwai wata maganar ne?" habu yace "alfarma nake nema idan kana ganin ba matsala ko leburancine nazo na dingayi anan asibitin naku idan ba damuwa" Abdulrahman yace "zaka iya barin can gida daka saba?" habu yace "dama ai ina zuwa lagos cirani na saba tafiya nanma zan iya dinga zuwa ina komawa ko bayan wasu watannine" Abdulrahman yace "shikenan ba matsala yanzu ka koma duk sanda ka shirya sai ka dawo" habu yayi ta godiya yana karawa sannan fa ya shirya yabi su mal musa da niyyar wannan talatar zai biyo motar kasuwa ya dawo. Jikin Khadija kuwa alhamdulillah ta samu sauki sosai dan yanzu banda mitar zaman asibitin babu abinda takeyi ko yaushe burinta kawai ta koma gida haka ita tace ta warke shi kuma Abdulrahman yaki ya kyaleta ko yaushe idan tayi masa mitar sai yace "Khadija kinki ki gane abinda yasa na hanaki komawa gida yanzu idan ananne idan wani abun ya faru ko bananan akwai likitoci da zasu kulamin dake idan a gidane kuwa sai na dawo dole ki kwantar da hankalinki akwai abinda nake jira zan maidake gida.
...............
Hi angels
So finally an kawo kudin Amira amma kuna ganin momy ta hakura kuwa?.
Menene labarin wani abu da ya taba faruwa da almajiri a gabanka wanda ya tayar maka da hankali ko har ma ya sakaka zubar da kwalla? Ina sauraron amsarku.
VOUS LISEZ
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Roman pour AdolescentsLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
